← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 94

Sashe 5

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ko 30 minutes basuyi da fitaba Salem ya sami parking space yayi parking sannan ya kalli Abdul yace
" alh Abdul kadawo driver seat " kallonshi Abdul yayi yana murmushi sannan yace
"Sir har ka gaji?"
"Yeah" daria Abdul yayi
"Sir a haka zamu samu biyan bukata?" Abdul ya tambayeshi, Salem yayi relaxing tare da lumshe idanuwa sannan yace
"I am excusted.. Inajin kaina yana son iyimin ciwo sannan am not use to hayaniya" ya fada yana mikewa zaune
"Sorry sir very soon zaka dan saba" ya fada yana fita daga cikin motan, zagayawa yayi wurin Salem sannan ya bude motan Salem yafito shikuma ya koma driver seat. Abdul yana tuki yana tambayan Salem sunan inda ya nuna mashi dazun amman yayi banza ya kyaleshi,
Suna komawa gida direct wajen first aid box ya wuce ya Balli aspirin yasha. Sannan ya wuce bedroom dinshi,

Aranan duk yanda Abdul yaso su kara fita ko kallonshi Salem baiyiba balle ya bashi amsa.

Wace garima makeup artist din ya kara zuwa ya chanza mashi fuska Amman ki fita Salem yayi wai the sun is very hot, sai bayan sallan asar suka fita, suna cikin yawo, mutane sai tsaida taxi suke amman ko kallonsu bayayi balle ya tsaya.

Around six Salem ya hangi wata babe tsaye, ta ci gayu cikin fitted gown,gata beauty, Salem kallon Abdul yayi sannan yace
"Alh kalli wata yarinya chan..she look cute" sai lokacin Abdul ya lura da yarinyan.
"Sir ka tsaya kayi toasting dinta mana tunda tayi maka" Salem dan rage gudun motan yayi sannan yace
"Ya zanyi toasting dinta...kasan ban taba woeing yarinya ba.." Ido Abdul ya zaro
"Sir what about all the girls?.."
"Su suke nuna interest a kaina..." Bai gamaba yaga yarinyan tana tsaidasu, Dan murmushi yayi sannan yayi parking yana cewa
"Allah gani gareka" da sauri Abdul yace
"duk inda tace kanuna kasan wurin" yarinyan Dan takawa yayi saitin Salem sannan tace
"Mallam sharada zaka kaini" wani kamshin turare Salem yaji sannan ga muryan yarinyan so melodious
"OK" ya amsa mataa shiga motan tayi suka kama hanya.

Da taimakon Abdul suka isa sharada, sai yarinyan ta cigaba da nuna mashi inda zai kaita har suka isa kofar gidansu, 1k ta fiddo ta mika mashi, kallon kudin Salem yayi sannan yace
"Bani da chanji"
"Keep the change" yarinyan ta fada mashi, Dan girgiza kai yayi sannan yace
"No...you keep the money" yarinyan hada gidan sama Dana.kasan tayi
"Malan kallanni da kyau ka kalli kanka wayafi wani bukatan kudin" ahankali Salem yace
"Nafiki bukata... Amman haka nan nakeson bar maki kudin" yarinya tsoki taja tare da wulla mashi kudin sannan tace
"Kaji matsiyaci da iya yii...dalla take your money" tana kaiwa nan ta shige gidansu. Salem kam dariya ya dingayi kaman mara hankali
"Wai kaji matsiyaci da Iya yi" yafada cikin daria. Shima Abdul daria yake, Salem kallon Abdul yayi sannan yace
"Ashe mata sun iya rashin mutunci " ya fada yana rike cikin don tsananin daria
"Sir indai wulakancin matane kadan ka gani...don wallahi suna dashi kwando2" Salem kara tuntsurewa yayi da dariya
"Ai sai yanzu na lura da haka ...anyway nasan wannan adventure namu zai zama fun cos am feeling it already"

💙♥💜💛💚
ZAKISAN KONI WAYE
♥💜💚💛❤
®zuwairat(ummu maryam)

7⃣

Har suka kai gida Salem bai bar dariyba,
"Ni ake cewa matsiyaci...gaskiyana tausayawa samari marasa money.. Don gaskiya da gani suna shan wulakanci" daria Abdul dake zaune yayi sannan yace
"Ai sir kadan ne wannan.." Dan tabe baki Salem yayi sannan yace
"Amman wasu yanmata basu da tarbiya..haduwa babu kunya babu tsoro ka zagi mutum"
"Ai sir wasu yanmata har marin samarin suke..." Bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"Kai alh Abdul ..ka bar karya mana...daga inasonka sai mari...ya rabbi kasa incikaro da irin wannan wallahi sai na taya ko waye daukan fansa" shidai Abdul daria kawai yayi don yasan irin wahalan dayasha hannun yanmata kafin ya gama degree dinshi yasami aiki a NGO kuma amatsayin bodyguard din Salem.

ONE WEEK LATER

cikin sati daya Salem ya gane abubuwa da dama game da mata don cikin sati dayan kullum sai yaga cool babes amman duk wacce yayiwa maganan so sai su wulakantashi , wasu har da zagi, Amman abun bai bashi haushi don duk sanda mace ta zageshi ko tayi mashi kallon banza sai ya wuni yana daria don dadin abun yakeji cos yanzu zai gane wacce zata soshi don Allah, yasan duk yanmatan dayayi toasting dasun San koshi waye da gudu zasu amsheshi hannu bibbiyu. Kuma yanmatan rashin kula garesu don fuskanshi da kayanshi mara guga kawai suke kallon Amman dazasu kuramashi ido su kalli agogon hannunshi, Rolex watch ne sannan inda zasu kalli zoben azurfan dake hannunshi costumise ne sannan da zasuyi hakuri su kalli kafanshi designer Prada ne kuma inda zasu kalli.hannunshi da kafanshi fari kal suke kaman ka taba jini yafito abunka da bafulatanin cikin daula.

Tunda suka fara fita kullum Salem cikin ciwon kai yake sannan tafin hanninshi yayi ja saboda dan tukin dayake cos rabonda yayi tuki har ya mance sai yanzu.

Duk wacce yadauka sai sun biyashi kudi koda yace baya amsa sai sun tillasa shi ya amsa amman suna bashi yana badawa.

Kuma wannan fitan ya kara wayar mashi da kai don yanzu yasan yakamata masu hali su dinga Dan fita don hakan zaisa su san halin da talakawa suke ciki cos yanzu ya kara sanin da akwai masu wahalan rayuwa sosai. Kullum sai yafita da akalla raw cash na 1million amman bai dawowa dako sisi saboda duk mai baran daya gani sai yabashi rabonshi.
Tunda yake bai taba fita koda abroad yaji it in dadin da yake ji ba cos he's having lots of fun. Haka yasan yayi deciding koda Allah yasa ya samu biyan bukatanshi, duk shekara zai dinga dan fita yana ganin abinda ke faruwa.

💛💚💜♥💙💛❤

Ameera ce tsaye cikin wata kayattacen daki, daka gan dakin kasan na yayan hutune, komai na dakin pink sannan ga wata madaidaiciyan plasma jikin bango da decoder, tashar boom TV take kallo don sai wata wakan Stanley enow ke tashi itakuma sai rawanta take, daga ita sai pant da bra sai rasa take kaman ance kiyi rawan zaa baki award. Duk ilahirin jikinta sai shaking yake, bayan wannan wakan aka sawakan sekem aikam nan rawa ya chanza, yanda take rawan tamkar daita akayi rawan sannan kaman itace tayi wakan don babu part din wakan da bata iyaba.

Wayan ta dake kan dan mini bed dinta sai ringing take amman bataji, sai bayan anyi mata 3 miss call sannan daga baya taji da sauri ta rage volume din decoder tare da picking wayan
"Babe ya kike?" Daga daya side din akace
"Haba ameera INA kika ajiye wayanki naketa kiranki ba amsa..." Ameera dake nishi saboda rawan datayi tace
" sorry sis wallahi ina nan INA practicing dance step dina ne...." Bata karasaba yarinyan ta tuntsure da dariya sannan tace
"Practicing kaman dole ko kuma ince kaman za a baki award?"
"Dalla malama what's your reason for calling"
"Daman ummace ta aikeni zoo road shine nace inzo ki rakani?" Ameera kaman jira take
"Yes kizo daman nagaji da gidan nan kuma mom ta hanani fita"
"OK..gani nan zuwa Amman please ki shirya don nasan halinki"
"Don't worry yanzu nan zan shirya" suka katse wayan. Da sauri ameera tabude katon wardrobe dinta Wanda ke shake da kayan sawanta,wash purple Arabian gown ta fiddo tare da Dan figigin Vail din kayan.
Dagudu tashiga bathroom ta watsa ruwa sannan tafito, cikin sauri ta shirya cikin kayan sannan ta dauko makeup kit dinta ta zauna gaban mirronta ta tsara kwalliyanta looking so breathtaking, sannan ta fesa turuka masu kamshin gaske. Wurin shoe rank dinta ta nufa ta dauki wasu light purple high heels sannan ta zauna bakin gadonta tana jiran zuwan kawarta mai suna zeenat.

Batafi minti 20 dazamaba zeenat tazo, taganinta ta window taga batazo da motaba
"Kambu ..badai da motata take son mujeba..." Bata karasaba zeenat tashigo
"Babe ina motanki.." Ameera ta tambayeta
"Tana wurin gyara wallahi...muje da naki..." Da sauri ameera ta girgiza kanta sannan tace
"Babu fuel kinsan daddy yana abuja kuma kona gayawa mom bazata bani ba..so yanzu meye abunyi?"
"To zai mu hau taxi..." Dan table baki ameera tayi sannan tace
"Amman fa kinsan banson hawan public car...mutum na iya kamuwa da wani communicable disease.. Balle bakasan ubanwa da uwarwa suka taba hawaba...." Tunda tafara maganan zeenat ke kallon ta, saida ta gama sannan tace
"Ke dai kullum halinki bai chanzawa...kawai daga hawan taxi sai my kamu da disease?... Dalla taso mu tafi time is not on our side" tafada tana fita daga dakin.
Zeenat kyakyawace Amman ko kadan bata kama kafan ameera ba...Amman when it come to character she's an angel.

Itama ameera fita tayi tabi bayanta Amman saida ta dauki dettol disinfectant spray tasaka cikin handbag dinta.

Dakin mom dinta suka tafi tana ganin ameera ta hada giran kasan dana sama, zeenat na shiga dakin ta saki fuskanta, bayan sun gama gaisawa ameera tace
"Mom zan raka Zainab zoo road" Matan shuru tayi kaman bataso sannan ta daga kai ta kalli agogn dake jikin bangon dakinta
"Kunga this is after 4, Ku tabbatar kun dawo kafin 7" da sauri suka amsa
"da yes mommy" sannan suka fita

❤💚💜♥💛
ZAKISAN KONI WAYE
♥💚💛❤💛
®zuwairat(ummu maryam)

8⃣
Chapter 5 · 0% Book details