← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 94

Sashe 6

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna fita suka tsaida taxi amman mutum in na tsayawa ameera ta kalleshi sannan tace
"Malam ka wuce" mutum kallon ta yayi
"Malama ai bake kika tsaidaniba " mutum ya amsa mata, ameera tabe baki tayi sannan tace
"Kayita tsayuwa nan" ta gayamashi a tsiwace, itakam zeenat ta saba da halin ameera, mutum ya watsa mata mugun kallo sannan yace
"Shegiya mai kama da aljannu" itama ta kalli mutum Wanda akalla ya girmi ubanta tace
"Shege mai kama da shaidanu" mutum fixgan motan yayi yabar wurin yana cewa
"Banza mara tarbiya" dukda mutumin ya tafi bai hana ameera cewan
"Uwar data haifekace mara tarbiya" kallonta zeenat tayi tare dacewa
"Haba shekira ai wannan mutumin ya girmi daddy fa?.." Harara ta ballawa zeenat sannan tace
"Daddy ki ya girma..don ni kam bai kai ubanaba balle ya girmeshi" Dan tsoki zeenat taja kafin tace
"Wata rana sai kin ja ruwan dafa kanki wallahi...nonsense kawai" itama ameera tsaki taja sannan tace
"Kema kinsan baa haifi mutum ba wallahi..kuma kika kara cemin nonsense sai injuya gidan ubana ai ba dole bane in rakaki" haka suka dan taba chan2 baki kaman yanda suka saba kafin kowa tayi shuru.

Sunfi minti ashirin tsaye, duk dan taxi din da suka tsaida sai ameera ta kare mashi kallon sannan tace ya wuce,saida suka tsaida taxi yafi biyar, suna tsaida na shiddan zeenat tayi sauri ta shige.

Itakam ameera saida ta fesa dettol disinfectant spray a inda zata zauna, mai motan juyawa yayi ya kalleta, itama ta kalleshi tare dacewa
"Non entity". Ko kallon zeenat batayiba har suka isa zoo road.

Karfe shida da rabi suka fita daga gidan yayan zeenat, dan takawa sukayi kafin su karasa bakin titi, kaman dazunma duk mai taxi din da suka tsaida sai tace suna kama da kazamai ko kuma tace sun cika muni

❤💛💛💚💙💙💙

Salem kam har ya mikawa Abdul car ya daga kai sai ya hangi wasu yanmata su biyu tsaye, maida key din yayi Wanda hakan yasa Abdul cewa
" sir ya akayi kuma" ya tambayi Salem, dan murmushi yayi sannan yace
"Kalli wasu babe chan.bari muje don wancan mai purple gown din tayimin.." Dan daria Abdul yayi sannan yace
" sir ai magrub ya gabato..." Salem ya katseshi da cewa
"Don't worry...in har suka tsadamu to zamu san gidansu, gobe sai muje"
Rage gudun motanshi yayi lokacin daya kusa zuwa inda suke tsaye, aikam zeenat na ganin taxi sai ta tsaidashi, dadi Salem yaji cikinranshi don ya gagara yaji muryan budurwan dake sanye da purple gown. Yana tsayawa ameera ta zubawa Salem ido, shima zuba mata ido yayi yana kallon ta bako kiftawa, bai ankaraba yaji dayan budurwan tayi saurin bude motan tashiga, itakam saida taga gama kallon Salem sannan ta ja wani irin dogon tsoki tare da kauda kanta gefe
"Please babe ki shigo mu tafi kinga magrub ta gabato" yaji budurwan da tashiga motanshi tace, itakam ameera tafi minti biyar sannan ta bude handbag dinta ta dauko dettol disinfectant spray ta fesa inda zata zauna, Abdul da Salem juyawa sukayi suna kallonta, itama kallonsu tayi da sexy eyes dinta kafin tace
"Malan wannan kallonfa..ko Baku taba ganin disinfectant bane?" Tafada tana gyara zamanta, Salem kam beautiful mouth dinta ya kurawa ido yana imagining yanda zasuyi tasting. Juyawa yayi ya tada motan lokacin da zeenat tace
"Malan GRA zaka kaimu" .
Yana tafiya yana kallon ameera ta mirror, Abdul nuna mashi hanya yake amman dukan hankalinshi ya tafi ga ameera data fiddo iPhone 7 tana danne2, kaman ance ta daga kai, sukayi 4 eyes, wata irin mugun harara ta balla mashi tare dacewa
"Malam ijn idonka yayi maka ya ka ciro mu raba ...village monger" Salem sauke idonshi yayi tare da yin murmushi, cikin ranshi yana cewa
" wai ne take cewa bakauye alhalin nasan inda naje aduniya da kyar taje kafin ta mutu"

Zeenat matsawa tayi kusa da ameera sannan cikin rada tace
" babe kalli hannun wannan mutumin tare da agogon hannunshi" baki ameera ta tabe sannan tace
"For what?" Salem yaji suna magana ahankali yadan saci kallonsu ta mirror, yaga zeenat nayiwa ameera rada, Amman bayajin abinda suke cewa
"Babe please ki kalla mama"zeenat ta sake cewa ameera, sai lokacin ameera ta daga kanta ta kalli hannunshi.

Gani tayi hannunshi farin kal sannan ga Rolex kwance kan fatan hannunshi, baki ta tabe kafin tace
" kilan barawo ne...INA taxi driver INA Rolex watch " Salem da Abdul Dan kallon juna sukayi dan sunji abinda tace cos baa ahankali tayi maganan ba. Abdul kam murmushi yayi cos yasan they don't know who they are dealing with.

Cikin minti 50 suka isa gra, a wani katafaren gida suka tsaya
"Babe ki shiga gida kawai su wuce dani" zeenat tafadawa ameera,
"Sai munyi waya" ameera ta amsa mata kafin tafita, Salem bayanta yabi da kallo
"Angel" ya furta ahankali

💜💛💙♥💜
ZAKISAN KONI WAYE
💛💙💜💚♥
®zuwairat(ummu maryam)

9⃣

Bayan su ajiye zeenat, suka samu wani masjid sukayi sallan magrub sannan suka koma gida.
Suna isa aspirin yafara sha kafin akawo mashi abinci, abin mamaki sai ya tsinci kanshi da tunani yarinyan daya sauke, daya kai loman abinci sai yayi murmushi, Abdul kallonshi yayi
"Sir meke saka daria?" Ya tambayeshi cikin girmamawa
"Wallahi yarinyan dazun ce...halinta ya bani mamaki.." Ya gayawa Abdul, shima Abdul daria yayi
"Ai sir yarinyan ta iya ban daria, ga tsiwa" Salem ajiye spoon din hannunshi yayi yana daria
"Wai baku taba ganin dettol disinfectant spray bane?" Salem ya fada cikin irin muryan ameera, daria suka sake yi,
"Wai village monger" Abdul ya fada, Salem kam daria har da rike ciki,.

Wace gari Salem har Allah2 yake mai makeup dinshi yazo yayi mashi don kwana yayi tunanin yarinyan, musamman yanda take tafiya sannan har lokacin bai bar jin kamshi turarenta ba. Har karfe biyu artist din bai zoba, yana kwance kan wani lafiyayyen gado ya dauki wayanshi ya kira Abdul, bayan ringing biyu Yadaga yana cewa
"Sir me kake bukata?"
"Alh ka kira artist din nan yazo mana" dam murmushi Abdul yayi kafin yace
"Sir yau da wuri zamu fitane?"
"Eh" kawai ya fada a takaice

Wajen karfe uku yazo yayi mashi chanjin kala sannan ya fiddo kayan sawa jeans da riga polo, baa taba sa kayanba Amman sun Dan koke saboda wankin da Abdul yayi masu, dagasu yayi yaga sunyi over squeezing, daukosu yayi yaje wajen Abdul
"Alh ka gogemin wannan kayan" ya fadawa Abdul
"Sir...talaka Nada lokacin guga?" Dan daria Salem yayi sannan yace
"Ai ba talakan bane, kuma gaskiya bazan iya tsayawa gaban wannan yarinyan babu gugaba "
"But..." Abdul tafara cewa bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"No but...am commanding you as your boss" da sauri Abdul ya amshi kayan ya gogesu.

Bayan sallan asar suka tafi pizza hut suka danyi eating sannan suka kama hanya gidansu ameera dake sultan road,
Around 5 suka isa gidan, haka nan Salem ya tsinci kanshi da fadiwan gaba ko dan bai taba zuwa gidan budurwa zance bane oho. Wani wuri Abdul yayi parking kasancewan shike tuki, bayan yayi parking Salem yafito, ya nufi bakin gate din gidansu, yafi minti biyar tsaye kafin ya daga gorgeous hannunshi yayi knocking a katon gate din gidan.
Wani mutum ya bude da alaman shine mai gadin gidan ne,
"Lafia?" Yaji mutumin ya watsa mashi tambaya, ahankali Salem yace
"Ina wuni" ya gaida mutumin, saiya ga yanayin mutumin ya sauya zuwa na murmushi
"Lafia lau dan nan..wa kake nema?"
"Budurwan gidan nan nake nema" Salem ya amsa mashi kuma saida yagama furta maganan yaji ba haka ya kamata yace ba.
"Ya sunanta" mutumin ya tambayeshi, dan shafa silken hair dinshi yayi
"Hmmmm...ban san sunantaba...jiya ta manta wani abu cikin taxi na shine nakeson bata" yafada kaman Mara gaskiya, mutumin kura mashi ido yayi for a while kafin yabude mashi kofan
"Shigo" yace mashi, Dan juyawa yayi ya kalli Abdul tare da kanne mashi ido daya shikuma kuma Abdul ya daga mashi hannu alaman good luck, yana shiga ya daga kai ya kalli katon gidan mai shegen kyau amman is not compared to gida daya cikin slim estate, wasu kujeru ya gani gefen parking lot din gidan.

Kan daya daga cikin kujeran ya zauna yayi balancing kaman gidanshi while mai gadin ya shiga cikin don kiran ameera.

Afalo ya tadda ameera da affan zaune suna kallon geet, sallama yayi yashiga gabanshi na disco saboda sanin halin ameera, bata daga kai ta kalleshiba tace
"Ya akayi?" Ahankali yace
"hajiya...wani mutumne yake nemanki.."
"Go and tell him to call me" don kaidanta kenan, duk Wanda zaizo wurin ta sai tabashi appointments, mai gadin baijin turanci, jikinshi na rawa yace
"Hajiya...banji..."
"Kai illiterate.. Cewa nayi kace mashi ya kirani...misfit kawai" ta fada tana wulla mashi irritating look, dan kara runtsunawa yayi kafin yace
"Hajiya cewa yayi wani abu kika mance cikin taxi dinshi.." Bai karasaba ta katseshi dacewa
"Je ka gaya mashi na bar mashi ko menene" mai gadin yafito da sauri don yanda ameera take mulkasu ko mom albarka, direct inda Salem ke zaune ya nufa, Salem upright ya zauna yana jiran abinda mutumin zaice.

"Malam tace tabar maka" Salem kurawa tsohon ido yayi for a moment kafin yace
"Kace mata its important..tazo bazan bata mata lokaciba" mutumin kaman bazai jeba, Amman sai yajuya.

Sallam yakariyi yashiga falon, afusace tace
"Wai ya akayine?" Dan runtsunawa ya karayi sannan yace
"Hajiya yace bazai bata maki lokaciba .."
"Wai baka da common sense ne...cewa nayi kace mashi nabar mashi" jikin na rawa ya fita, Salem kallon yanda mutumin ke tafiya jikinshi da bari yayi,
"Malam dan Allah kayi hakuri kar kajamin..tace tabar maka" ahankali Salem yafara cewa
"Kayi hakuri dan Allah..ba wani abu ta manta ba...kawai inason ganintane...please kaje ka gaya mata...nayi maka alkawarin bazan kara aikenkaba..." Jim mutumin yayi sannan yayi shahada ya koma.

Sallama yayi yashiga
"Hajiya..." bai karasaba ameera tacire room slippers din dake kafanta ta jefeshi.

Salem dake zaune ya hangi tsohon ya fito da gudu yana shafa keyanshi
"Dan girman Allah ka tafi" yafadawa Salem sannan ya juya ya koma bakin gate har lokacin bai bar shafa inda ameera ta jefeshiba.

Salem kam mamaki yake, Amman baisan abinda ya sami tsohon ba Amman tunani yake killan hajiyan gidance ta yimashi wani abu sam baiyi tunanin ameera ba.
Chapter 6 · 0% Book details