← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 94

Sashe 85

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Ameera na barin dakin mom ta shirya dan karamin bag Nata Sannan ta dauki wani babban bag ta saka kayan data fidda don badawa, car keys dinta ta dauka ta tafi dakin mom ta fada mata zataje bank
"Me zakiyi bank?..." Mom ta tambayeta
"Inason in Ciro kudi don inyiwa zu hinde shopping..." Mom Dan kallon Ameera tayi tana jin dadi cikin ranta Sannan tace
"Ba Sai kinje bank ba...ai kudin da Khalid ya baki sunanan...sai kiyi amfani dasu..." Tsale tayi
"Yauwa mom..nagode..." Tafada tana duba inda mom tayi wrapping kudin ta ajiye, yanda mom ta ajiye su haka suke har lokacin, bude laden tayi ta dauki wrap daya
"Mom zan shiga cikin gari in sayi abubuwan da zasu bukata..."
"Are sure dad dinki zai yarda?..." Dariya tayi
"Eh mana...I know for sure.." Mom ma Dariya tayi tana cewa
"Like father like daughter..." Ameera bata kara cewa komai ba ta fita, batayi nisa sosai ba don da akwai manyan shop unguwan su, daya daga cikin su ta shiga ta fara siyan kayan kaman su bag of rice carton of spaghetti, macaroni, cuscus Sai su mai da Maggi atakaice Sai da ta kashe kusan 70k cikin kudin don har da su kayan tea da sardine ta saya masu, biyan kudin tayi aka zuba mata kayan bayan motanta ta koma gida. Koda ta dawo gidan bata bude boot ba nan ciki ta bar kayan. Ganin motan dad ya shaida mata cewa ya dawo, wurin shi taje ta shaida mashi abinda take son yin ko two words baiceba ya amince mata, rungume shi tayi ta koma dakinta tana mai jin dadin zata ga su hinde , kwanciyan ta kedawuya wayanta ya fara ringing, tana dagawa Sai taga sir Salem, murmushi tayi Sannan tayi picking, sallama tayi, daga chan bangaren Salem najin muryan ta saida yayi mika Sannan ya amsa mata sallama.
Gaida shi tayi kaman nothing is wrong ya amsa yana lumshe idanuwa at the same time yana kallon Nudeness dinshi,
"Baby ashe kiyayyan da kike yimin har zai koma kan abokina?..." Ya tambayeta kaman bai son magana, murmushi Ameera tayi tana relaxing kan gadon ta
"Sir ban ganeba..."
"Kin gane mana...ya zaayi kiyi dumping Khalid just because he's my friend?...." Ya fada cikin nutsuwa,
"Hmmm..." Kawai tace
"Baby meye maanan hmmm...pls baby don't do that to Khalid... Wallahi yanason ki kaman ranshi..." Ameera shuru tayi tana sauraron muryan shi mai zaki kaman sugar, Salem yacigaba dacewa
"Kinga I did not screw you...even if I did it should not stop you love for Khalid... Or don abinda nayi maki a Chan inda na ajiye ki ne?..." Ya fada yana biting lips dinshi,
"Ni babu abinda ka yamin..." Tafada muryan ta na rawa
"Ok...then pls ki amincewa Khalid... If it is because of me zan bar rayuwan shi in kyaleku...I will not visit..."
Ameera dai shuru tayi Sai ta fara tuna abubuwan da Salem yayi mata sanda yaje wurin ta,
"Pls say something... Don't dump us for a footballer...." Yafada Ahankali, still Ameera shuru tayi batace kala ba, ajiyan zuciya Salem
"Pls baby... Don't do this to us..." Yafada cikin whisper, ahankali Ameera tace
"I have to think..."
"You have all the time you want... But please don't dump Khalid... Khalid yana sonki fiye da yanda kike tunani...I know you will be a good influence to his life...pls help him and Allah will help you too..." Yafada cikin sanyin murya,
"Ok..but pls let me think about it..."
"To shikenan.. Should I call you to know your decisions?..." Ya tambayeta Ahankali,
"No need sir..." Salem Dariya yayi Sannan yace
"Aisha kinsan me?..." Ahankali tace
"Aa..." Sannan yacigaba dacewa
"Acikin duk mazan da suke sonki kinsan Wanda ya chanchanci ya moreki?..." Ameera shuru tayi tanason jin what he's driving at, yacigaba dacewa
"Duk nafisu chanchanta...you know why?...cos I change your life.. Amma ba matsala...but since I can't have you don't let my friend loose you...pls am begging you..." Ya fada cikin nutsuwa, Ameera mamakin maganan shi tayi , what does that mean, ta tambayi kanta,
"Kinji pls..."
"I will think about it..." Shine amsan data kara bashi.
"Ok then...thanks for your time... Kina bukatan wani abu?..."
"No thanks" ta amsa mashi, Dariya yayi
"Kinsan yanzu am like a big brother to you..." Yafada yana dariyan rainin hankali, itama Dariya tayi
"Yaya bana bukatan komai..."
"Kedai fadi gaskiya.. I know ladies with shopping... My lil sis shuwa ko dukan ta zakayi ka kaita shopping zata amince..." Yafada yana dariya kaman ba sir Salem ba, itama Ameera Dariya tayi Sannan tace
"Hakane..."
"Hakane..kenan kema haka kike..." Ya tambayeta yana dariya
"No...nidai ban ce hakaba..."
"Don't worry... Zansa Khalid ya kaiki shopping Dubai...kawai don't dump us..." Murmushi tayi
"Ka sanme?..." Tafada ahankali
"No...baby..."
"Stop calling me baby..." Dariya yayi
"Ko sisters dina baby nake kiransu...we are in 21 century so that doesn't matter... Fadamin"
"Zanje abuja gobe..."
"Me zakiyi chan?..."
"Wurin su Zainabu zani..." Dariya Salem yayi
"Who is Zainabu?..."
"Wacce na zauna dasu gidan da ka ajiyeni..."
"Lafiya zakije wurin su?..." Ahankali tace
"Just want to visit them... Am missing them..." Shuru yayi yana tunanin maganan Ameera
"Baby you have changed so much....alhamdulillah.."
"Thanks to you..." Hira suka cigaba dayi kaman wasu masoya, har Tawakaltu ta fito daure da towel ya bata wayan suka cigaba da hira shi kuma ya shiga wanka.

Da dare sultan yazo amma bata fita ba, fada mashi tayi bata da lafiya. Falo yazo yayi mata sannu ya koma, sama ta hau tayi kwanciyan ta tare da kashe wayan ta, sultan bai dade da fitaba Khalid yazo yaji wayanta switch off ya aiki mai aiki su kirata akace tana bacci nan hankalin Khalid ya kara tashi, ya koma ya kara Kiran Salem ya shaida mashi, kwantar mashi da hankali Salem yayi.

Wace gari da wuri Ameera ta kama hanya Sai lokacin ta tuna bazata gane wurin ba, Salem takira ta shaida masa, tura mata number majed yayi yace in ta isa ta nemeshi.
Chapter 85 · 0% Book details