← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 94

Sashe 16

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tawa komawa tayi ta zauna har lokacin bata dainajin shocking ba, Salem murmushi yayi ya kai cupin bakin shi, wani irin daci yaji don tunda yake wannan ne karo na farko daya sha maltina, hadiyewa yayi, sai yaji makogaron shi nayi mashi zafi, cikin ranshi yafara cewa
"Allah yasa kada wannan abun ya zama ajalina" da kyar ya kara sha akaro na biyu fuskanshi kaman na mai shan giya. Gefe ya ajiye, tawa kallon shi tayi
"Sir ka shanyeshi.."
"Indai bakison daukan gawata kin barni haka nan" yafada cikin ranshi sannan yadan harareta
"Nagode" saida ya Dan goge bakin shi da bayan hannunshi sannan yace
"Oremi dauko pen Muyi list din" mikewa tayi tashiga ciki, few minutes later ta dawo da pen da paper. Zama tayi kasa a gabanshi zata fara rubutawa yadan taba kafadanta ta daga kai, alama yayi mata dasu tafi waje, girgiza mashi kai tayi , shikuma yace
"Please" da ba kowa zaijiba, mikewa ta karayi tashiga ciki tacewa mami sun tafi kasuwan
"Ku dawo lafiya" yaji mami tace cikin hausanta mara fita, tawa tafito
"Mu tafi" ta fada mashi murya chan kasa, kaman yana jira ya mike har ya rigata fita tabi bayanshil.
Yana fita ya bude mata murfin mota Amman taki shiga
"Ki shiga mana" ya umarceta,Dan girgiza mashi kai tayi
"Ka rufe in bude da kaina" Dan daria yayi
"Laifine mutum ya budewa budurwan shi mota.."
"Ni ba budurwan ka bace.." Ta katseshi tana murmushi
"To laifine mutum ya budewa friend dinshi mota?"
"Ai ka girmeni.."
"Nasani Amman inason bude maki cos you are a lady" gyara tsayuwanta tayi
"To mu kwana anan" bashi da choice dole ya maida ya rufe ya zagaya yashiga cikin ranshi yana tunanin
"Daman haka suke kodai she's just kidding with him" shiganta cikin motan ya katse mashi tunani.
Kallon ta yayi
"Oremi please taimakamin zakiyi..kiyimin list din abubuwan da mace kamanki zata bukata in ita kadai ke zaune kuma bata fita" tawa kallon tuhuma tayi mashi sannan tace
"Ban gane ba?" Dan murmushi yayi
"Sister ta nakeson yiwa siyayya"
"But kace boarding school zata" dan shafa keyanshi yayi don ya mance daya fada mata hakan,
"Oh sorry..Ashe hakana gayamaki..daman aure zatayi to mijin bashi da ko sisi so sai nayi niyyan siya duk abubuwa dazata bukata" baki tawa ta bude don sai ya burgeta
"Amman gaskiya kana da kirki".
" kafin kisanabinda zanyi da kayan kenan" yafada cikin ranshi
"Meyasa kika fadi hakan" ya tambayeta, ahankali tace
"Ai naga kaima hustling kake Amman kasan ciwon yan uwanka" murmushi yayi tawa yacigaba dacewa
"To kayan abinci kawai zamu rubuta?.."
"Aa..dukkan kaya harda nasawa..Amman masu sauki na talaka"
"OK" kawai tawa tace sannan tasake cewa
"Bari mu fara da kayan sawa..atampa bawa zan rubuta" Salem shuru yayi kaman mai tunani
"To..ki rubuta shida..Amman kar kudin su yawuce
2k" ba musu tawa ta rubuta sannan tace undie nawa
"Uku each" tawa ta rubuta pant da bra uku,
"Gyale fa" ta tambayeshi, Dan girgiza kai Salem yayi
"Ai cikin gida take babu inda zata"
"Ok..zaka saya da shadda da lace ko materials?"
"Gaskiya bani da kudin.."
"Turare fa?" Tasake tambayanshi
"Matan kauye basu shafa turare sai Ku Matan birni" yafada
"Matan birnin ma sai masu halin" tawa tafada cikin ranta
"Kayan kwalliya fa?"
"Bandasu"
"Amman at least ka sayamata man shafawa ko?"
"To rubuta mata Wanda kike shafawa indai bashi da tsada"
"Cocobutter ne kuma karamin 600"
"Rubuta mata babban" ta rubuta
"Yan kunnefa?" Ta sake tambayanshi
"Nawa kudin na kunnenki?" Ya tambayeta yana nuna bariman dake kunnenta
"250"
"Babu Wanda kudin ta bai kai hakaba?"
"Da akwai mana..har na 70 naira da akwai"
"Kirubuuta na 70 guda biyu" ta rubuta.
"Mun gama da kayan sawa now kayan aikin gida..set din tukunya zamu rubuta?" Ido Salem ya zaro
"Me zatayi da set..kawai rubuta kwano, cup , spoon, pot, knife,.. Hmmm saime kuma..rubuta bibbiyu " duka tawa ta rubuta su
"Yarda broom da dustbin ko?"
"Eh yauwa na mance su..".
Haka tawa ta dinga lissafa mashi kayan aikin gida suna rubutawa,
"Sai su gado da kayan daki" inji tawa
"Wane irin gado..kawai rubuta student foam sai ledan daki sai curtains masu sauki don ba kudin gareniba" ta rubutasu
"Sai abinci" tawa ta fada mashi
"The fun part" ya fada cikin ranshi, kallon ta yayi sannan yace
"Kaman ke kina iya cinye buhun shinkafa cikin wata hudu?" Ya tambayeta, ido ta zaro
"Kam ina hauka?..gaskiya bazan iyaba...why do you ask?" Dan jinginawa yayi sannan yace
"Ai don insan irin yawan rice din da zan saya mata,..lissafamin kayan abinci in gani..ki dinga rubuta su"
"OK" ta amsa mashi sannan ta fara rubutawa tana cewa
"Rice, macaroni, spaghetti, indomie.." Da sauri Salem ya katseta dacewa "banda indomie...ni ban ciba balle in sayawa wani...cigaba" Dan murmushi tawa tayi sannan tacigaba
"Garin tuwo, kuskus,.." Salem ya kara katseta
"Nifa ba kayan birni nace ki rubuta ba..kawai rubuta irin garin danwake, alkubus.." Kayan gargajiya Salem ya dinga lissafawa kaman yana cinsu itakuma sai rubutawa take.
"Sai kayan miya..." Ta fada mashi bayan ta kammala rubuta kayan abinci
"To ki fadesu inji" Salem ya amsa mata yana kallon bayan wuyanta da ya dana bayyana, wasu kananun gashi yagani kwance har bisa gadon bayan ta, sai yaji tana cewa
"Kuka, egusi..tasshi, maggi, gishiri,albasa..." Suma haka ta rubuta su, data rubuta mai tsada Salem yace ta gogeshi don bashi da kudin siyansu.
"Mun gama..." Ta fada mashi,
"Kawo su in gani" ya fada mata yana lumshe sexy eyes dinshi kaman mai jin bacci, mika mashi tayi, amsa yayi ya kara hadawa da hannunta, wannan karinma janyewa tayi da sauri, saiyaga ta hada giran sama sana kasa
"Sorry..mistake nayi" yace mata, batace komaiba, kallon list din yayi
"Wow..kina da fine handwriting..ki gama uni ne..?" Kallon shi tayi for few seconds sannan ta sada kanta kasa
"Ka taba gani degree holder yana saida abinci a restaurant?" Shuru yayi bai bata amsa ba tacigaba dacewa
"Ka taba ganin talaka yayi degree?" Salem saiyaji jikinshi a mutu
"Nayi maki alkawarin zaki gaji da karatu" ya fada cikin ranshi sannan yace.
"Ai with Allah komai ma is possible" yafada ahankali
"Hakane" ta amsa mashi sannan ta kara cewa
"Amman kai kayi karatu sosai" dan murmushi yayi sannan yace
"Kin taba ganin degree holder yana tukin taxi?" Tawa dan daria tayi
"Ai Nigeria kenan everything is possible..Amman seriously kayi karatu"
"Meyasa kike ganin kaman nayi karatu?" Ya tambayeta
"Ai naga turancin ka mai dadi" nikam nace dan baki ganshi a office ba.
"Ai yau da gobe..yanzu lissafamin kudin kayan nan da wayanki" yafada mata don abar maganan cos shi mutum ne Mara son karya kuma in ya fada mata baiyi karatuba karyan kara yawa zaiyi tunda doctorate gareshi.

Kara amsa tayi tafara calculating da wayanta don dukkan kayan ta rubuta harda kudin su, bayan kaman minti goma ta daga ta gan yanda ya kurawa bayan wuyanta ido, ahankali ta maida gyalenta daya fadi daga kanta sannan tace
"Gaskiya kudin dayawa" ahankali Salem yace
"Nawa" yafada kaman mai rada
"72k" wara idanuwa Salem yayi kaman Wanda bai taba ganin irin wayannan kudin ba
"Gaskiya oremi.. Duka kudina 70k..suma na kusa shekara ina tarasu" ahankali tawa tace
"Yanzu me zamuyi?" Ta tambayeshi kaman its her problem
"Mu rage wasu kayan.." Dan daria tayi
"Ai dukkan kayan are important.. Wane kake ganin zamu rage" kallon ta yayi eyeball to eyeball sannan yace.
"Underwears" da sauri tawa ta kauda kanta
"anya wannan mutumin ba dan iskabane?..."
"I heard you" ya fada mata ido tawa ta zaro don atunaninta maganan zuci tayi,
"Kasan basai mun rage komaiba..ina da kudin da nake tarawa saboda kudin hayanmu...zan baka 2k sai ka kara.." Mamaki ne kwance kan fuska Salem don kasa boyewa yayi
"In lokacin biyan kudin yayi kuma ban baki bafa?" Ya tambayeta yana karajin sonta cikin ranshi
"Ai insha Allah zan samu wasu kafin time din..." Shuru yayi yana tunani kala2 cikin zuciyanshi
"OK" yace mata.

Fita tayi daga cikin motan ta shiga gida, bayan kaman minti biyar ta fito da kudin, saida ta shiga motan sannan ta mika mashi, amsan kudin yayi yaga yan Dari bibbiyu ne guda goma
"Thanks... Zan biyaki..I promise"
"Ba sai ka biyaniba...so yanzu zamu tafi kasuwane ko yaya?" Shuru yayi ya kalli waje yaga yanda rana ke shining yasan ko kashe shi zaayi bazai Iya shiga rana ba
"Kawai ki barshi da yamma zan shiga kasuwa tunda yanzu zuhr ya kusa"
"Amman cemin kayi bakasan kasuwa ba" kara shafa kanshi yayi
"This gal is smart" yafada cikin ranshi
"Ai wannan abokin nawa zansa ya rakani"
"To shikenan" ta fada feeling disappointed don har lokacin bata gaji da ganinshi ba.
"Rubuta min number ki bayan takardan" yafada mata don yasan da zaran ya fidda wayanshi asirinshi zai tonu. Ba masu ta rubuta mashi kasan list din sannan sukayi sallama, ko wannensu da tunanin dayake.

💚💜💛💙❤
Ranar da Salem yabar gidansu ameera dad ya maidata gidan kanwanahi dake sharada, duk yanda mom tayi yabar ameera gidan ki yayi
"Bari in kai yata inda zaa bata kulawan da amare ke bukata" yafadawa mom. Suna isa gidan dad ya ajiye ameera ya koma, kanwa dad irin wayyanyun Matan nan ne, don tun ranar tafara durawa ameera kayan mata masu kyau da tsada sabanin wayanda tasha abaya,
"Yarinya kisha kiyi tatul don daya dandanaki bazai kara shaawan wata ya mace" inji anty Sadiya kanwar dadi.

💚💜💛💙❤
Salem dawowa daga gidansu tawa, Abdul ya kira ya mikawa list din tare da cewa
"Alh inaso kayi typing din wannan ka turawa agent dina...ka gaya mashi ya sayi dukan kayanan ya ajiyesu cikin wannan gida...and tell him ban yarda akara ko arage wani abu ba"
"Yes sir" abdul ya amsa mashi. masjid ya wuce, yana dawowa yashiga shiga bedroom dinshi wayanshi yafara ringing, murmushi yayi don yasan ummanshi ce
Yana picking yaji tana cewa
"Son what's happening??" Ahankali yace.
"First love ban ganeba..meya faru?" Cikin fada Umma tace
"So you are asking me ko?" Ahankali yakara cewa
"Umma bansan abinda nayiba ko" yafada cikin shagwaba,
"Mutane nata kirana da abbanka sunayi mana congrats wai zaayi aurenka this coming Saturday!?" Salem baki ya rike sannan yafara kalle2 cikin dakin kaman mara gaskiya.

_Nagode kwarai da irin kulawanku, Allah yasaka maku da alkhairi_
Chapter 16 · 0% Book details