← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 94

Sashe 51

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

®zuwairat(ummu maryam)

5⃣1⃣

_Please fan inason kusani cewa wannan book din na riga na tsara kayana daga farko har karshen shi, duk masu cewa in ya saki ameera sun daina karantawa.. Kuna iya daina karantawa tun yanzu...likewise masu cewa in bai saki ameera ba su daina karantawa.. Suma suna Iya daina karantawa ...Sannan masu cewa in aka saki ameera novel ya lalace you will be surprise.. And masu cewa nabawa Yoruba power cikin novel din da yawa har suna cewa koni Yoruba CE..to am not Yoruba.. Amma na zauna da Yoruba likewise Hausa so its the reality of what am seeing that am writing.. So kowa yayimin hakuri yaga karshen novel din nan.
Thanks for the love and affections._
_
💙❤💛💚💜

Salem dake zaune gaban Umma daria yayi sannan ya amshi list din daga hannun Umma yana dubawa shima dariya yayi
"To wannan akwati daya na meye hope ba lefe suke nufi ba..." Daria Umma tayi
"Hmm..so kona meye nidai 24lb zanyiwa daughter in-law..." Salem murmushi jin dadi yayi yana tunanin
"In sunje chan zatayi shopping kayanta na Nigeria Dan kanta" Abba kara amsan list din yayi ya dinga dubawa
" kayan nan doubling dinsu zamuyi..like tunda sunce 300 tubers of yam akai 600.. Rice akai 10bags, komai linkawa zamuyi.. Cows kuma tunda sunce biyu Sai akai biyar..ko ya kika gani?.." Ya fada yana kallon Umma
"Hakan yayi..don naji yarubawa da akwai cin nama a occasions....so ana iya karawa da raguna uku" daria Salem yayi
"Kam..Umma duk cin namansu sun cinye cows biyar?..."
"Ko basu cinye ba..mudai zamu kai..in ya rage su rike..." Salem mikewa yayi
"Umma bari inje inyi calming nerves dina...nagaji..." Hararanshi Umma tayi
"Abba ka dayaje kwara state saiyace me" Salem daria kawai yayi ya fita ya bar Abba da Umma zaune, Umma wayan ta ta dauko tana cewa
"Bari inkira Hajiya hannatu ko containers din kayanta sun iso... Sai muyi siyayyan daga wurin ta kawai tunda ba lokacin da zamu je Dubai yanzu"
"OK..hakan ma yayi.. Make sure you buy correct things..." Inji Abba, Umma daria tayi tana cewa
"you know me..."

Ahankali ameera ta shiga kitchen taga babu sauran abinci gashi kudin hannun ta sun kare, hinde da yaranta sunyi shurko2 suna jiran abinda zaayi, ameera fitowa tayi ta bugi gate, masu gadin budewa sukayi don atunaninsu hinde ce ko yaranta, suna gani ameera sukayi saurin maida gate, baki ta tabe tare da Jan tsaki
"Malam ba fita zanyi ba..kawai Ku kira sir Salem Ku fada mashi bani da sauran abinci..." Tafada tana jinginawa da gate, masu gate banza sukayi daita, saida ta kai minti ashirin basu ce mata kala ba, kara dukan gate din tayi
"Kunsan wallahi Ku kirashi ko kuma in tara maku mutanen garin nan...kun San karamin aiki nane..." Daya daga cikin su ya dauki wayan shi yafara dailing number sir Salem.

Salem na komawa side dinshi na family house ya kwanta tare da rungume pillow yana lumshe idanuwa ahankali kaman mai jin bacci, yanajin wayan shi tafara kara yayi tsaki tare dacewa
"Can't someone have a nice and quite time?.." Yafada yana daukan wayan, yana ganin number Mara suna ya Dan saki murmushi don most of the time sisters din tawa suna kiranshi suna zolayanshi, picking yayi daga chan bangaren akayi mashi sallama, amsawa yayi sannan yace
"Waye?.." Daga chan bangaren mutumin yayi mashi bayani ko shi waye kaman yanda ya saba, bata rai Salem yayi don har ga Allah mancewa yake daita mussanman tunda komai ya daidaita da tawa, shuru yayi for a moment sannan yace
"Bata wayan.." Da sauri aka mikawa ameera waya, Salem komawa yayi ya kwanta ya bar wayan on hands free, ameera don daidai ta muryan ta tayi
"Good afternoon..." Tafada with strong and firm tune, Salem dan kallon wayan yayi don yanda ya ji muryan ta so strong da firmer don babu alaman karaya cikin muryan ta, Dan tabe baki yayi
"Son of a bitch speaking... Me akayi?" Yafada batare da ya amsa gaisuwanta ba, ameera lumshe idanuwa tayi tare da zama kasan inda take don wani irin masculine voice dataji
"Sir...wai daman abinci na ne yakare..."
"Are you insane... Ya zaayi kice dukkan uban abincin da aka ajiye har sun kare?" Yafada afusace har yana mikewa zaune, ameera shuru tayi tana tura kanta cikin cinyanta, saida ya kai aya Sannan tace
"Sir..."
"Don't sir me... I said ya akayi dukan abincin yakere..and don't play dumb with me...filthy fool" ameera kuka tafara kokarin yi
"I don't have time.." Dasauri ta daidaita muryan ta Sannan tace
"Bani kadai keciba..."
"What!... Kunjimin shegiya.. Da abincina kike good Samaritan?... Na ubankine?...kina son ki nuna min you are now charitable ko?... Karyanki..cos people with deadly habit don't quit easily" ameera kuka tafarayi tana cewa
"Am ka yafe..."
"Keep am not done talking... Kilan kin mance abinda kikayi.. Well let me remind you.. Kinga wannan tsohon da kika fesawa pepper spray a ido?..har yau ban bar imagining how he feels and curse you ba..." Yanda yake magana kaman yanzu abun ya faru don muryan shi Sai fita yake da wani irin bitterness, kuka ameera tafarayi sosai
"Ka sakeni inje in nemi yafiyansu..please.." Baki Salem ya kara tabewa
"Hmmm..don't you think is a little to late to cry when the head is cut off?.." Ameera kuka ta dingayi kaman ranta zai fita, don tasan Salem ya gama ganin bakin haka ya tabbatar mata she don't stand a chance when it comes to having her love,
"Kuma da kike cewa in sakeki..just relax..in the next 5 weeks you will be a free bitch...kuma kika kara sa aka kirani bazan sakekiba Sai nan da wata biyar..." Cikin kuka ameera tayi saurin cewa
"Sir..abincin fa..." Dariya ne ya kufcewa Salem don a tunanin shi bazata kara maganan abinci ba
"Ban saniba.." Hannu yasa zai kashe wayan yaji tana cewa
"Duk yau banci komai ba... Am starving.." Tsaki yaja Sannan ya kashe wayan
"This girl will never change" ya fada yana dailing number agent dinshi, nan ya sanar dashi ya aika yaro ya kai 500k chan gidan kuma Wanda ya aika ya tsaya ya saya mata duk abubuwan da take bukata.
Komawa yayi ya kwanta tare da kashe wayan gabadaya.

Sai bayan asar aka kawowa ameera kudin kuma saurayin cewa yayi ta aikeshi yayi mata siyayyan kayan datake bukata. Alokacin ameera tayi kuka har tagaji don gani take Salem bazai sa akawo kudi ko abinci. Iyalen hinde kam duk sunsha tagumi. Ana kawo kudin kowa ya warware amma banda ameera cos Sam bashine matsalan taba. Nan take ameera ta tambayi hinde cinkafa buhu nawa zai ishesu har sati biyar? Nan suka fara list har da kayan lashe2 da sabulan wanka da wanki mostly for hinde s family. Duk uban siyayyan da sukayi saida suka samu chanjin kusan 270k.

❤💛💜💚💙

Tawa na zaune falo, daka ganta kasan tana cikin kwanciyan hankali cos yanzu tayi mugun kyau, gashin kanta ya sha gyara sosai Sannan skin dinta look so radiant (who say black is not beauty), yanzu kamanninta da rihanna ya kara fitowa sosai. Komai nata moderate, Sai yanzu naga abinda Salem ya gani daya like mata. Suna Zaune kan gadonta tayi ganmo da kafanta Sai temple run take cikin wayan ta, bude kofa akayi ta daga kanta, mamice ta shigo da wata babban mace data sha speck, daganin matan mai halice cos she looks glamorous, nunata mami tayi
"She's the bride tobe.." Tawa taji mami ta fada mata sannan ta fice daga dakin tabar tawa da Matan, da sauri tawa ta ajiye wayan hannunta ta sauka daga kan gado ta gaida Matan cikin girmamawa. Bayan Matan ta amsa ta dauki kujeran gaban mirror ta zauna ta fuskanshi tawa Sannan tafara cewa
"My daughter how old are you?"
" 18..going to 19" tafada kanta kasa, murmushi Matan tayi,
"Alhamdulillah.. Tunda Allah yasa zakiyi auren wuri..to da akwai lectures da yakamata in dinga baki for two weeks, acikin lectures din da akwai Wanda zaku dauka tare dashi groom..." Tawa dai kanta kasa batace komai ba, Matan tacigaba dacewa
"Sannan zan kula da abinda ya kamata kici, abinda ya kamata kiyi, Sannan zan koya maki traditional dance steps for your introduction and traditional wedding.." Gaban tawa yafara faduwa cos ko daga kafa bata iyaba indai rawa ne. Sai kafkafta idanuwa take kaman Mara gaskiya,
"So from now har lokacin wedding dinki kina under my care.." Bata idaba mami tashigo , key ta mikawa Matan
"Ga makullin wurin Dana nuna maki dazun.." Matan amsa tayi mata godiya Sannan ta kalli tawa
"Nuna Mani inda kayan sawanki suke in yi maki parking..." Da sauri tawa ta mike
" No...no" Matan tafada tana daga mata hannu
"Don't do that.. You are a princess and a bride to be...komai naki yazama cikin ruwan sanyi"
"Ikon Allah.." Tawa tafada cikin ranta,kuma tana mamakin inda zasu da zaayi mata parking

❤💛💜💙💚
ZAKISAN KONI WAYE
💜💛❤💙💚

®zuwairat(ummu maryam)

5⃣2⃣

Yanuwa kunsan dukkanmu ba sanin kamu mukayi, social media ta hada mu and I love all of you, kuma yanda kuke comments ko kuma reply comments din wasu ke nuna in kai literate ne ko kuma illiterate, so those that have good manners congrats cos yana na kyau da kuma riba...those that lack manners kuma can easily hug transformers cos it will be better.

Kuma please Ku Dan yimin uzuri don zaku jini shuru for a while.

HABIBA MOHD, I LOVE YOU DIE ALLAH YABAR MU JONE

❤💙💚💛💜
Chapter 51 · 0% Book details