← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 94

Sashe 91

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wakoki suka dinga chanzawa suna hira har lokacin sallan ishai, sallah sukayi Khalid ya bukaci da suka kara raka biyu na nafilla, ba musu ta bishi, suna idarwa ya juya yana kallon ta, kanta kasa Sai wasa take da yatsunta,
"Hmmm zan cire wannan kunyan,..." Ya fada yana mikewa, jallabiyan dake jikinshi ya cire ya mikar daita ya cire hijjab dake jikinta,
"Baby let take our bath..." Yafada yana kallon reaction dinta,
"Tare zamuyi?..." Ta tambayeshi
"Yes..." Yafada yana daukanta, wuntsul2 tafarayi da kafanta, yaki ajiyeta sai cikin bathroom direct to bathtub dake cike da foamed water, nan take kayan jikinta suka jike, shima shiga yayi bayan ya cire nashi kayan, Ameera rufe fuskan ta tayi don bata taba ganin nakedness dinshi ba, kayan jikin ta ya cire da kyar don sai cewa take
"Ka bari zanyi wanka ni kadai..." Cike da kunya sukayi wanka ya dauko kaman jaririya. Yana kawota kan bed wasanshi ya chanza dana kullum, dakewa Ameera tayi don tayi wa kanta alkawarin amincewa dashi.
Saida yaje za main part ta fara kuka, lallashin ta ya dingayi amma bai daina abinda ya faraba, Khalid Sai adua yake ta kwararo mata don tunda yake bai taba jin abinda yaji wurin Ameera ba har cikin ranshi yana cewa Salem yayi asara,

Ameera ido ya raina fata dukda Khalid was gentle don Sam bayason kukanta amma saida ta koka sosai, da sauri ya mike bayan ya samu nutsuwa yayi kneeling ya kama hannun ta yana yimata adua har lokacin bata bar kuka ba, rarrashin ta ya dingayi har saida tayi shuru ya shiga bathroom ya hada mata ruwan dumi ya dawo ya dauketa.

Bayan ta gama wanka ta fito tana tafiya ahankali amma tafiyan ta bai bace ba sosai nace ba kama Tawakaltu da aka yiwa dalla dalla ba 😂😂😂. Shima Khalid wanka yayi ya fito yayi kneeling gaban gadon hannun shi rike da nata ya cigaba dayi mata adua, har dasu thanks, Ameera kwance idanuwanta lumshe tana sauraron abinda Khalid ke cewa ranta fal da murnan ta kawo budurcinta gidan mijin ta, aduan Khalid yaki karewa, bude idanuwanta tayi ta galla mashi harara tana cewa
"Ya isa haka nan mana..." Dariya ne ya kufcewa Khalid don kaman ba ita tayi maganan ba, kin tashi yayi ya cigaba da yi mata aduan,, Sai turo baki take tana magana Ahankali batare da Khalid yaji abinda take cewa ba.

Bayan sati daya da wedding din Khalid su Salem suka dawo Nigeria, a lokacin cikin Tawakaltu wata 4 da two weeks, abuja suka sauka duk guys dinshi cewa suke
"Sir daga yanzu ka tashi daga slim... Don kayi fat..." Dariya yayi tana cewa
"Thanks to my princess..." Ya amsa masu
wacegari suka je yola, Abba ma saida yace Salem yayi kiba har yana zargin haka nan yaki zuwa bikin Khalid don babu alaman ciwo ajikin shi.
Bangaren Umma sukaje, Umma na ganin su ta mike da sauri, da sauri itama Tawakaltu tayi kneeling kaman yanda ta saba, fada Umma ta farayi tana cewa
"Kar ki kara wannan kneeling din...baki ganin conditions dinki?...please kar ki kara..." Ta fada tana mikar daita tsaye, cikin girmamawa ta gaida ta itama cikin jindadi ta amsa tana nuna murna ta a fili, tsaraba yan aiki suka shigo dashi ciki,Umma kallon Salem dake ta fama murmushi tayi ta saki murmushi tana tunanin Ashe danta zaiyi kiba haka?
"Amma son lafiyarka lau kaki zuwa wedding din amininka ko?.." Umma ta tambayeshi, murmushi yayi
"Aa...Umma bani da lafiya..." Bai idaba Umma ta katseshi dacewa
"Karya kake...baka kama da Mara lafiya..." Kallon Tawakaltu yayi
"Princess ba bani ba lafiya ba?..." Ya tambayeta yana kanne mata ido daya, Umma dake kallon abinda yake ta dauki pillow ta wurga mashi tana cewa
"Indai lafiyan ka lau kaki zuwa wedding din Khalid baka kyauta ba..."
"Umma da gaske bani da lafiya...ai kinsan haka nan bazanki zuwa auren Khalid ba..."
"Kai dai ka Sani..." Ta fada tana kama hannun Tawakaltu dake zaune kusa daita. Dakinta suka shiga shikuma ya haye dinning yafara cin abinci.
A dakin Umma aka kawowa Tawakaltu abinci Umma ta amsa ta fara feeding dinta kaman yanda ta saba feeding Salem, da farko kunya tafaraji amma daga baya sakin jikinta tayi taci ta koshi,
"Da fatan Salem yana kula dake yanda ya kamata?..."
Umma ta tambayi Tawakaltu, Ahankali ta daga mata kai alaman eh,
"Kar ki boyemin komai.. Ki dauke ni amatsayin maminki...remember amananki akabani...ance in dauke ki kamar su shuwa kuma na dauka...so kar kiji kunyar fadamin abubuwan sda Salem ke yi maki Wanda baki so...." Tawakaltu dadi takeji har cikin ranta
"First love babu abinda yake yimin...." Ta amsa mata kanta kasa
"Bakisan yanda danki yaci min uwa ba kafin in fara sabawa..." Tafada cikin ranta.
"Da akwai inda yake maki ciwo yanzu?.." Umma ta sake tambayan ta,
"Aa...kasala ce kawai Sai dacin baki..." Ta amsa mata cikin natsuwa
"Wannan is normal... Ko zaki zauna nan in kula dake har ki haihu?..." Da sauri ta dagawa Umma kai alaman eh Sai dariyan keta take cikin ranta don tasan Salem zaici kaniyanta
"Amma inason zuwa wurin su mami..." Tafada ciki sanyin murya
"Ai wannan ba matsala bane...Sai akaiki a maidoki..." Umma tayi assuring dinta,
"Kwanta ki huta..." Inji Umma, ahankali tayi kokarin mikewa Umma ta umarceta da ta kwanta kan gadonta. Kwantawa tayi itakuma Umma takoma falo har lokacin Salem na zaune kan dinning, zama Umma tayi opposite to him ta shaida mashi hukuncin data yanke,
"Kambu...Matan nan zata kulla min tsiya..." Ya fada cikin ranshi, azahiri kam saida ya kusa kwarewa da ruwan dayake sha, da sauri ya ajiye cup din yana cewa
"Umma wa zan dinga dafamin abinci..." Yafada sounding out of words, harara Umma ta balla mashi
"Da wake dafa maka?..."
"Ai Umma... Wai itatace zata zauna?..."
"No...ni
Nace ta zauna..." Zaro ido yayi don yasan halin ummanshi
"Kuma ta amince?..."
"Kai bansan iskanci..." Tafada tana mikewa, shima mikewa yayi ya shiga dakinta itakuma ta zauna falo tana kallon dadin kowa atashar arewa 24.
Yana shiga ya hangi Tawakaltu ta bage kan gado, karasawa yayi wajenta ta bude ido
"Princess ya akayi kika amincewa Umma zaki zauna nan bayan kinsan larurata?..." Marairace fuska tayi tana cewa
"Sugar ya zanyi...I can't say no..."
"Yo can't say no?... AI Wallahi yanda kika amince haka zaki koma kice mata zakibi...in ba hakaba duk weekend zan zo nan kuma kinfin sanin sauran...." Dariya tayi cikin kasaita tana cewa
"Ni gaskiya bazan Iya fada mata haka ba..." Mikewa tayi ta matsa kusa dashi har suna shakan numfashin juna Sannan tace
"Amma kai ka fada mata..." Tafada tana lashe bakinshi,
"Daman da gangan kika amince zaki zauna nan...karki damu...nasan Maganin ki..." Yafada yana kaman bakinta, kiss yayi mata, zare bakinta tayi tana cewa
"Meye magani na?../"
"Bazan kaiki Kwara ba..." Yafada yana kara kai bakinta saitin nata kaman bai taba kissing dinta, Dariya tayi mashi tana cewa
"Umma tace zatasa akaini a maidoni..." Takashe maganan tana yi mashi gwalo, Dariya yayi
"To anjuma zansaki kuka yanda zata jiki ta koremu ...." Kwantawa tayi tare da juya baya tana cewa
"Ba Sai ka ganniba?..." Mikewa yayi ya karayi mata kiss Sannan ya fita tare da bugun bumbum dinta da karfi.

*Da fatan ansha ruwa lafiya... Allah ya bada lada ya biya bukatun mu na alkhairi* 🙏👏🤝👏
💚💙💜❤💛
ZAKISAN KONI WAYE
💜❤💛💙💚

®zuwairat(ummu Maryam)

8⃣2⃣

Masoyan zakisan koni waye ina mika godiya ta gareku, thanks for your support

Ban manta dakeba the birthday gal, Sarah am wishing you a fruitful and prosperous years ahead, happy birthday🎂🎂🎂 hope you find all you desire in life.

Yan ummu Maryam page I love you all💋💋

ZAKISAN KONI WAYE fan 1 to 8 duka ina kaunarku.

Yan Zuwairat novel 1 and two I love you die, Allah ya bar zumunci har dake khulud sarauniyar surutu.

Yan khaleesat hydar novel I heart all of you, comments dinku na Sani nishadi.

💛💚💙💜❤

Da yamma Salem ya zo komawa abuja kiri2 Tawakaltu ta ki binshi don har gabanshi umma tace
"Ki bishi in kin yi niyya..." Ta makale kafada tana cewa
"Zan zauna dake..." Salem kam kaman ya hadiye zuciya ya mutu, har bakin jet ta raka shi, ko kallon ta baiyi ba ya shige, hannu yayi mata alaman ta zo, ahankali ta taka ta shiga ya rike ta yana cewa
"Yanzu princess ni zaki yiwa haka?..." Marairace fuska tayi tana cewa
"Ni kunya nakeji ban iya abinka..." Hararanta yayi yana cewa
"Don't worry... In ma guduwa kikeson yi daga gareni ba komai bane cos zan dinga zuwa nan kullum ki bani hakkina..." Dariya tayi batace kala ba, kissing dinshi tayi kokarin yi ya kauda kanshi gefe. Sauka tayi akayi sama dashi.

The following day Umma ta bukaci yasa akawo jet don zaa kai Tawakaltu Kwara.

Ranar da taje kam mami kasa bacci tayi don murna, kowa Sai cewa yake Salem ya Iya kiwo don ba karamin chanza musu tayiba.

Kwana ta biyu hau jet don komawa yola Ashe Salem ya fadawa pilot ya kawota abuja, aikam gidanshi aka kaita, yana jin karan jet ya fito sanye da three quarters da polo, kallon ta yayi yana cewa
"Allah ya kawo min kaza gasassa daga sama.." yafada yana dariya, marairace fuska tayi tana cewa
"Sugar nice kaza?..."
"Ni badake nakeba..." Yafada yana daukanta gaban su majed yayi mansion dinshi daita.

_Two months later_

Su Ameera ansha amarci kaman hauka don har ta saba da rayuwar aure, ba karamin kulawa Khalid yake yi mata ba, kusan komai shi keyi mata har da wanke undies kullum cikin fada mata how much he loves her yake, Ameera har gajiya take da jin I love you.

Yau suka dawo Nigeria kuma da fever ta dawo don tana kwance jikin Khalid Sai rawan sanyi take,bayan kaman hour daya wani abokin Khalid yazo da kayan aiki,
Chapter 91 · 0% Book details