← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 94

Sashe 41

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

_Please fans kuyi hakuri for my irrational behavior.. Wallahi bacin rai ne ya ja hakan, gani nayi in mutum zaiyi maka gyara don Allah sai ya bika PC basai ya fada public ya jawa kansa attention ba. Kuma please duk Wanda yasan novel din nan bai yi mashi ba ba sai ya karanta ba, sai mutum ya gama karantawa yaji dadi sai ya nemi batawa mutane rai. Anyway it nothing don in baka da mahassada baka kaiwa koina._

"Wai me ka tsaya yi ne achan?" Salem ya tambayi majed da dawo daga gidan ameera agajiye, ahankali majed yace
"Wallahi sir sai biyar INA zuwa kasuwa..." Afusace Salem yace
"Can't you use your number six?... Kawai sai ka biye mata?... Tun dazu muke jiranka...now look at time" yafada yana nuna mashi Rolex watch din dake hannun shi, majed baice komaiba don gajiyan dayake ji ya ishe shi, Salem bai Kara cewa komai ba ya shiga cikin jet, sannan su Abdul suka shiga. Salem sai tunanin halin ameera yake, ko kadan bata jin kunyan ta aiki Wanda ya girmeta,
"Anya wannan halin baa jininta yakeba?...hmmm I pity you...Allah nagani bazan hada zuria da irin ki ba" ya fada cikin ranshi, kauda kanshi yayi yana kallon gidanshi daga kasa, sai tunanin tawa yake before yana tunanin komai yake so zai samu with our wasting of time, he was thinking in ya samu yarinyan dayakeso babu bata lokaci zaa ayi auren su at his own convenient time, before yana tunanin money can buy anything and any body amma yanzu tawa has proof him wrong, Dan karamin tsaki yaja ya kara juya kanshi daya side din, yanzu yasan in har mami bata yarda ba bazai auri tawaba, and the most annoying part she's not a money person don har billion yana Iya badawa don tawa tazama his,
"She's making me restless.. She's ruining my life.." Yafada kasan makoshinshi, da sauri Abdul ya kalleshi
"Sir did you say anything?.." Harara Salem ya wulla mashi sannan ya kauda kanshi daga wurin, duk yafi jin haushin Abdul daya bashi shawaran sannan yana jin haushin kanshi daya biye mashi,Dayasan haka falling in love ke maida mutum restless da bai bi shawaran Abdul ba, kara juyawa yayi suka hada ido da Abdul ya kara hararan shi sannan ya dauke kanshi,
"Garrrrr...am going insane...in regret falling for you.." Ya fada cikin ranshi. Tunani kala2 ya dingayi cikin ranshi har tunanin in ya gane inda take ya saceta ya kaita wani kasa ya aure
"Sai dai su ganta da ciki wallahi.." Ya fada cikin ranshi, sai ya saki Dan karamin dariya Wanda yasa dukan guards dinshi kallon shi, nan take ya murtuke fuska kaman ba shi yayi daria ba. Bai ankaraba yaji jet yafara landing, kalle2 yadan yi
"Har Mun isa?"
"Yes sir" suka amsa mashi.

_Three days later_

Yau Abba Salem zai tafi kwara, cikin kwana ukun life yazama unbearable and painful for Salem, komai nashi kara tsayawa tayi, tun ranan bai kara kiran tawa ba ita kuma bata kirashi ba, kwance yake bayan raka Abba ya hau jet, wayan shine hannun shi dayayi dailing number tawa sai yayi saurin kashewa, so yake yayi zuciya amma Sam ya kasa, Allah Allah yake Abba yadawo yaji inda abun zai kasance.

Su Abba sun isa kwara state lafiya kuma oba ya san da zuwan su amma sun fada mashi ba official visit bane its personal hakan yasa bai he palace ba ya zauna a makeken gidanshi yana kiran isowansu.

Around 4pm Abba da obj sai wasu ministers biyu Wanda suke yan asalin garin suka isa palace din, cikin girmamawa yan palace suka dinga gaida su Abba, oba na tsaye bakin fadanshi yana ganin su ya ajiye girmanshi ya tarosu suka rungume juna yana cewa
" kun mantani...especially you da muke region daya" yafada yana kallon OBJ, dukansu dariya sukayi yakara cewa
"Wannan shi ake cewa august visit.." Daria suka karayi, fadin kyaun palace din is a waste of time don ya hadu beyond your imagination, wani makeken wuri suka shiga gaba dayansu , kan dinning shake da abinci kala2, dukan su zama sukayi akayi masu serving din abinci, suna ci suna hira har suka gama, personal palour din obha suka wuce
"Thanks for the hospitality.." Abba ya fadawa oba, oba dariya yayi
"Haba ni ke da godiya... You are most welcome... Kunsan ba kullum aka ganin baki irin kuba" obj daria yayi yana nuna oba yana cewa
"Kai tunda ka hau wannan kujeran ka kara Neman mu...kullum kuna kan kujera ko Baku gajiya.. Oho.." Daria suka karayi, Dan hiran bayan saduwa sukayi sannan OBJ ya fara cewa
"Kaman yanda muka aika maka zamuzo amma is not something official..." Oba dan daga mashi kai yayi sannan ya maida dukkan hankalinshi kan OBJ, OBJ yacigaba dacewa
"Nasan abinda ya kawomu ba Abu bane Wanda muke da concern kanshi bane amma amatsayin mu na shugabani bai kamata muyi shuru mu kyaleba.... Kuma abu biyu muke bukata wurin ka amma sai mun samu nasara akan stage na farko sannan zamu samu karfin gwaiwan wucewa stage nabiyu..." Oba kurawa OBJ ido yayi yana kokarin gane inda ya dosa amma Sam hakan bai samuba
"To Allah ya bani ikon yin abinda ke tafe da Ku" ya fada
"Ameen" dukkan su suka amsa, dukkan su sauka sukayi kan kujera sukayi kneeling gaban oba, ido ya zaro
"What's this?... Please stand..." Obj girgiza mashi kai yayi
"Ai mu masu Neman alfarma ne sannan kai sarki ne kuma kasan aladanmu dole ga girmama na gaba da kai ko ba komai ka girmemu.." Oba Dan girgiza kai yayi
"Nasani...amma kun tashi na baku izini kuma insha Allah kome zaku nema indai bai fi karfin mu ba zamu Baku..." Abba murmushi jindadi yayi kuma har cikin ranshi yana farin cikin hada zuria da zaiyi dasu, OBJ ya fara mikewa sannan Abba followed by minister, ahankali obj yafara cewa
"Abu nja farko da mukeso shine kayi hakuri kan abinda yarka ameenatu tayi maka shekaru da dama da suka wuce...muna Neman yafiya on be have of ameenatu.. Ka yafe mata ka maidata cikin yaranka...." Nan take yanayin oba ya chanza, zoben azurfan dake hannun shi ya dinga murzawa ahankali, kanshi kasa yafi minti goma baice komaiba, ahankali ya daga red eyes dinshi ya kalli each and everyone of them sannan yafara cewa
"Gaskiya kun mameni...I never see this coming.. Don da nasan kan ameenatu ne da ban Baku daman ganintaba..." Shuru ya karayi yana ajiyan zuciya ahankali
"Nafison ameenatu kan duka yarana...am she spit in my face..." Da sauri OBJ yakara kneeling down su Abba suka bi bayan shi,
"We know... Shiyasa muke baka hakuri.. Ka yafemata...lokacin harda kuruciya....wa zaiki arziki inba yaroba?...Allah ya huci zuciyan his royal majesty" OBJ ya fada, still oba shuru yayi yana goge zuffan gaban goshin shi, don duk sanyin wurin bai hanashi sweating ba, ahankali yakara cewa
"Sit..." Ya umarcesu, kin mikewa sukayi
"Bazamu tashiba sai ka bamu amsan da muke nema..." Inji OBJ, oba runtse idanuwa yayi sannan ahankali yace
"Ba matsala... Na maida ameenatu cikin yarana....kuma right this moment zan kira yan uwanta su kiramin ita daga Kano ta dawo ta amshi role dinta na princess of kwara land...." Bai idaba obj ya kwanta kasa flat su Abba suka bi bayanshi suna yiwa oba godiya, komawa sukayi suka zauna, wasu guards dake tsaye left and right din oba ya kalla, ahankali na hannun daman shi ya runtsuna wani magana oba ya fada mashi cikin kunne, da sauri ya fita, ya kai minti goma sannan ya dawo ahankali yaje saitin kunnen oba yayi mashi magana Wanda babu maiji sai Allah, yana gama fada mashi ya koma inda yake tsaye, ahankali oba ya daga kai ya kallesu tare da murmushi
"Alhamdulillah abun yazo da sauki...ameenatu tana Ilorin gurin yayanta... So yanzu an fada masu gobe su zo nan palace.." Dadi sosai suka ji
"I owe you one" OBJ yafadawa oba, dukkan su dariya sukayi, hira suka cigaba dayi har lokacin sallan magrub yayi oba da Abba tare da minster daya dake Muslim suka tafi masjid , tun hanya Salem ke ta kiran Abba, ya kasa tsaye ya kasa zaune,

Salem sai up and down yake cikin falon shi, agogon hannun shi ya kalla yaga har 7pm basuyi magana da Abba ba,
"Oh. Allah.. This is not good.." Ya fadawa kanshi, number Abba ya kara dailing amma yana ringing baa dauka ba, ajiye wayan yayi ya shiga bathroom ya dauro ablution suka tafi masjid.
Chapter 41 · 0% Book details