← Book details Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 94

Sashe 9

Zakisan Ko Ni Waye Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salem kam yana fita yana rawan sanyi don sam bai wanka da ruwan sanyi balle abinda ameera ta zuba mashi direct daga cikin fridge yake, bayan shi wani irin zafi yake yimashi kaman ansa mashi garwashin wuta, Salem yana tafiya yana tunanin abinda yafaru, yau dashi talakkane da ya hadiyi zuciya ya mutu don bakin ciki, yana zuwa inda ya ajiye motanshi yabude ya shiga, zama yayi yana tunanin abinda zaiyiwa ameera da zai huce don alokacin gani yake koda zaa yankata gabanshi bazai tausaya mataba
"She called me a bastard...non entity... Ta zagi uwata..oh gossh..me zan wa family dinki?...wane irin fansa zan dauka kanki?...I will deal with you and am going to enjoy every bit of it...you and your hopeless father are going to eat your vomit..you will beg for mercy.." Maganan tsohon ya dawo mashi
"Karshen rashi kunyaki da rashin tarbiyanki yazo...filthy bitch" Haka shi kada ya dinga surutu, yafi hour daya zaune wurin yana tunanin, ringing wayanshi ya farayi ya dauko wata costurmise phone Wanda baifi guda goma a duniyab ya amsa wayan, daga chan bangaren Abdul yace
"Sir are you alright? "
"Yes..just ka nemo min the best doctor kafin in dawo gidan..." Cikin tension Abdul yace
"Sir are alright?... What's wrong with you sir?" Ahankali Salem yace
"Am ok...just get me a doctor" Abdul zai sake magana ya katse wayan.

Still Salem zaune yayi wurin yana tunani, don har lokacin bai san abinyiba amman yasan ko me zaiyi ba abu bane mai kyau.
"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" ya dinga maimaitawa don ji yake kaman zuciyanshi zai bude kirjinshi abinka da mai zuciya.

Sai bayan sallan magrub ya koma gidan yana tuki yana tunani, yana zuwa gida ya tadda Abdul zaune da wani mutum a falo, Abdul na ganin shi yayi saurin mikewa yana cewa
"Sir me ya sameka?"
"Nothing" ya amsa masa atakaice, Abdul kallon yanda fararen idanuwanshi suka koma ja yayi sannan yace
"Sir something is wrong..."
"I said am fine!!!!" Ya daka mashi tsawa sannan ya kwantar da murya yace
"Where is the Doctor?"
"Gashi nan" ya nuna mashi wanda ke zaune,
"Follow me" ya umarshi doctor, yayi hanyar bedroom dinshi, yana juyawa Abdul yaga bayan riganshi da jirwaye,Abdul yasan wani abune ya sameshi Amman baisan meye ba kuma yasan duk abinda ya sameshi shine sanadi don shine ya bashi shawaran suyi abinda yakeyi. Duk sai yaji ya tsani kanshi, yasan in har wani abu ya sami Salem shi zaayi holding responsible, ahankali yace
"Sir am sorry.." Juyawa Salem yayi ya kalleshi
"For what?" Shuru yayi baisan abinda zai ce ba.
Suna zuwa bedroom dinshi yacire rikanshi ya kwanta kan gado tare dayin rub da ciki sannan yace
"Doc dubamin bayana da akwai wani ciwone?" Dukawa doc yayi tafara observing bayan shi
"Sir da akwai abinda ya sami bayan ka ne?" Ya tambayi Salem, kai Salem ya daga mashi sannan yace
"Eh...dazu nazo wucewa mistakingly wani ya zubamin juice ajiki...kuma naji wurin yana yimin zafi" kara kallon wurin doc yayi sannan yace
"Sir bayan ka ba ciwo...Amman inajin juice din da aka zuba maka yana da wani Abu ciki shiyasa kake jin zafi ...zan rubuta maka magani yanzu" kai kawai Salem ya daga mashi, cikin ranshi yana cewa
"Har wani abu lta zuba ciki don ta illatani...daga cewa ina sonta" yana cikin tunani wayanshi ya fara ringing, yana dubawa yaga Khalid ne, saida yace.
"The person I need.." Sannan yayi picking, daga dayan bangaren Khalid yace
"Driver what's up..." Salem shuru yayi baice mashi komai ba, Khalid yacigaba dacewa
"Na yanka mana ticket din zuwa kallon kwallon man united...ko taxi driving bazai barka kajeba.." Salem dan murmushi karfin hali yayi sannan yace
"Bazanje...." Bai karasaba Khalid ya katseshi dacewa
"Kan uban nan...dan taxi driving sai ka ruguza mana aladanmu da muka saba..." Ahankali Salem yace
"Ba laifinka bane..." Khalid kara katseshi yayi
"Guy ya akayi naji muryan ka kasa...kodai yan matan Kano sun cima uwane?"
"Ba kadanba" Salem ya amsa mashi, wani irin daria rainin hankali Khalid yafara yi yana cewa
"Me sukayi maka" yafada har lokacin bai bar daria ba, ahankali Salem yafada mashi abinda yafaru, shima Khalid ranshi yayi mugun bashi, Salem yacigaba dacewa
"Kuma abin haushi shine har yanzu bansan abinda zanyiwa yarinyan nan in huceba...don nayi tunani har nagaji.." Shuru Khalid yayi na dan lokaci sannan yace
"Guy ko insa ayi kidnapping dinta muci mata uwa..." Kai Salem ya girgiza kafin yace
"Mom da brother dinta are nice.. Kawai inason abinda zanyi in bata mata da dad dinta..." Shuru suka sakeyi kafin Khalid yace
"Kaima matsala gareka...yanzu wake ta wani true love.. Kawai kasamu mace mai kyau ciki da waje ka aura, ka biya mata bukatunta da rana itakuma ta biya maka bukatanka da dare..that's life now... Amman true love no longer exists,..." Bai gamaba Salem yace
"Best kasan I want a woman that can sacrifice her self for me.. Nasan there is a woman out there for me..."
"Kana nufin bazaka yi giving up ba kenan... Ko sai ansumu yarinyan da ta watsa maka acid a handsome face dinka zaka hakura....." Tsoki Salem yaja kafin yace
"Dalla yimin shuru...kawai ka gayamin abinda zai yiwa yarinyan nan I huce"
"Nace muyi kidnapping dinta kaki...to bari inda a dauko maka ita kayi raping..." Wani dogon tsoki yayi sannan yace
"Amman bestie baka da hankali..ai ko ina mazinaci bazan kusanci wannan yarinyan ba balle kasan ba halinabane..kawai inason in gan yarinyan nan under my control... I want her to beg for my mercy... Wallahi guy yarinyan sam batayiba....killan shiyasa Allah ya turani gidan don in koya mata hankali" shuru suka danyi sannan Khalid yace
"Yanzu meye abinyi?"
"I don't know.."
"To marry her...tunda kanason ta zauna karkashinka...sai kayi yanda ka gandama daita.." Salem bai karasa jin abinda Khalid zaice ba ya kashe wayanshi.

Bayan hour daya Abdul ya kawo mashi magaggunan da akayi mashi prescribing, still Abdul tambayan shi yayi abinda yafaru Amman still Salem ce mashi yayi bakomai.

Tundaga wannan ranan Salem ya rufe fita, daga bedroom sai masjid, kullum cikin tunanin abinda zaiyiwa ameera yake Amman still bai samu solution ba daga baya ya bawa kanshi hakurin ya kyaleta Allah ya hadata da daidai daita tunda shi ba abinda yazoyi ba kenan.

Bayan sati daya da faruwan abun Wanda yayi daidai da satinsu uku a garin Kano, Salem yasa Abdul ya kira mashi makeup artist ya gyara mashi fuska.

Gidan Salem a zoo road yake , kuma duk Wanda yasan zoo road yasan hanyarta busy road ne, saboda da akwai masu business kala2 a wurin , bayan sun fito, basu dade da barin gidaba wani dan almajiri yazo tsallake titi garin Salem ya kaushe mashi mistakenly ya Dan gogi wata murano, da sauri yayi parking don bawa mai motan hakuri shima mai motan parking tayi tafito, Salem da Abdul na fitowa, Salem ya gane Ashe mai motan ameera ce, da sauri ameera ta dubi motan bayan motanta da Salem ya goga, wani irin ashar ta saki sannan ta daga kai ta kalli Wanda ya goge motanta, tana ganin Salem ne tanufeshi gadan2, tana zuwa gabanshi ta sharara mashi wani wawan mari, nan take ya dafa cheeks dinshi, cikin zafin nama Abdul yazo wucewa da sauri Salem ya rikeshi da hannu daya still hannunshi daya rike da cheeks dinshi,
Ameera kallon Abdul tayi sannan tace
"Oh kana son tabani?..please bring it on...da saina koya maka hankali..." Sannan ta juya wurin Salem da har lokacin bai saki kuncinshiba tace
"Kai kuma ka bar bina kuma motata da kayi scratching saiya sayi uwarka da ubanka" Salem tsayawa yayi kaman bara lakka, muryan wata yarinyan ya tsinta tanacewa
"Ke Allah ya wadar halinki..." Bata idaba ameera tace
"Daga ke harshi kunci uban da ya haifeku banzaye matsiyata..." Yarinyan ta sake cewa
"Kece matsiyaciya tunda har zaki iya daga hannu ki mari Wanda ya girmeki saboda wannan motan..." Salem ji yayi wata tace
"Tawa..amebo watin concern you"

❤💚💙💜💛
ZAKISAN KONI WAYE
❤💙💜💛💚
®zuwairat(ummu maryam)

1⃣3⃣

Yarinyan da aka kira da Tawa ta kalli Salem taga kaman da jini hancinshi, bata ce komai ba ta nufi wani chemist dake kusa da wurin, Salem na kallonta ta cire kudi cikin apron din dake jikin ta don da alaman abinci suke saidawa awajen, ba da dadewaba ta dawo rike da cotton wool, tana zuwa ta mikewa Abdul, ahankali Abdul yace
"Me zanyi dashi?" Yarinyan nuna Salem tayi da yatsa kafin tace
"Habo yake.." Sai lokacin Abdul ya lura da jinin dake hancin Salem, da sauri Abdul ya amshi cotton wool din yafara goge mashi hanci, har lokacin Salem bai dawo daidai ba, don tunda uwar da ta haifeshi baa taba taba mashi lafiyan jikiba, sannan daga nursery school zuwa secondary school Turkish international school yayi kuma ko kadan baa dukan yara, amman shine yau Mace ta mareshi yau, duk da yasan yana da saukin zuciya yasan he can't let this go.
Itakam ameera tana ganin yafara habo ta dauki motanta ta bar wurin Amman fa har lokacin bata bar zaginshi ba.

Abdul yafara Goge mashi hanci, shima sai lokacin Salem yasan yana nasal bleeding, cikin ran Abdul kam ji yake in shi aka mara zai fi mashi sauki sau dubu, don zuciyanshi tafasa yake kuma abinda yafi bashi haushi shine yanda Salem ya hanashi ya Koya mata hankali, Salem ya ji wata babban mace nacewa
"Tawa..na my money you use buy cotton wool?" Ahankali tajuya wurin matan sannan tace
"Zan biya ki cikin kudin da zaki bani anjuma " Mata da ganintaba mutunci kuma da alama ita Tawa takewa aiki
"Ai dole ki biyani..makulmaciya...ko wa ya kiraki oho..oya wuce ki bawa mutane abinci" nafa wayanda suke aiki tare suka fara yi mata dariya, itakam juyawa tayi wurin Salem sannan tace
"Oga sorry..Allah zai sak maka...kuma insha Allah kaima watarana Allah zai baka motan daya fi nata..." Salem tsaya kallonta yayi sannan yace
"Thank you"
"Bakomai..." Ta juya ta tafi tana cewa
"Daman masu kudi basu ganin talaka as anything... Allah zai saka mana".
Chapter 9 · 0% Book details