Sashe 9
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Aunty zama ta yi a kasa tana kuka riris, fuskar ta cikin kafafun ta. Bayan ta dangwara min Aasim akan cinya ta. Tausayin Maccido kawai ta ke ji. Kafin a samu mutumin kirki mai son ‘yan uwan sa da karrama al'amarin su a baya irin Maccido abun mai wuya ne. Kafin a samu mutum mai kula da mahaifiya da tsantseni cikin mu’amalarsa da ita irin Attahir sai an yi sa’ar gaske. Rana daya daga yin aure ya zubar da duka wadannan halayen nasa. Mace ta canja shi, canjin da ta kasa ganewa.
Jikin Maccido ya yi mugun sanyi, shi ma nasa idon suka cicciko da kwallah. Amma kokari ya ke ya maida su. Rokon Aunty ya soma yi a kan ta yi hakuri, idan ya bata mata rai, bai yi da gangan ba.
Ba zan iya jure kallon wannan abun tausayi ba, babban mutum kaman Yaya Maccido na hawaye a gabana. Don haka na mike tsam na yi toilet dauke da Aasim ba tare da sun ankara da tashina ba. Zama na yi a gefen kwamin wanka ina hawaye ni ma rungume da yaron, na tausaya wa halin da suka samu kan su.
Ban san yaya suka yi suka ciwo kan Aunty Nabeelah ta yarda sai gobe da asubah mu tafi ba. Sai da na tabbatar Yaya Maccido ya bar dakin sannan na fito.
Muhsin ya bi ni da kallo har na samu gefen gado na zauna.
“Ma’u na, Ma’un Addah, wa ya taba mun ke?”
Ya yi maganar cikin raha irin tasa, amma ko kadan ba ta ba mu rahar ba ni da Aunty.
Dole ya tashi ya bar mana dakin, Aunty Nabeela ta dauki wayar ta da ke tsuwwa suka canza harshe ita da Fa’iq din ta. Sai larabci suke zumbudawa abin ya yi matukar burge ni. Na ce a raina, ina ma ni ma in auri Balarabe irin mijin Nabeelah? Shi ba zai yi min gorin boko da ban iya ba! Ba zai damu ba don ban iya karatun boko ba. Duk da dai yanzu a Sokoto ba kamar Bebeji ba, ba laifi ina tsintar ‘yan abubuwa da ba za a rasa ba sabida koyarwar Muhsin da dagewar sa wajen ganin ba a yi min maimaicin aji ba.
Sai ga Aunty na kyalkyatar dariya da mijin ta kamar ba ita ce ke kuka yanzu ba, yayin da ni kuma na shiga hidimar Aasim. Canza masa diaper na yi na hada masa madarar sa na dauke shi na soma ba shi.
Bayan sallar isha Aunty ta ce in tattara mana komai namu tun yanzu kada mu makara da safe.
Wajen karfe tara na dare Yaya Maccido ya shigo dakin, a yanzun kananan kaya ne a jikinsa shat da wando, samfurin Tommy Hilfiger ruwan bula mai haske da mai turuwa, duk da ya rame daga yadda yake a baya kyansa yana nan bai je ko’ina ba, sannan daukan wankan sa sai abin da ya yi gaba. Ya dube ni ina jijjiga Aasim, ya ce, “Ke kullum ba kya zama ne sai da yaro a hannun ki? Ki bar mata dan ta mana ko tare ku ka haife shi?”
Aunty Nabeelah ta galla masa harara, ta ce, “Ai ita ta san darajar na gaba da ita, ta kuma san nata shi ne nata. Hidimar da ta ke da dan uwanta ba zai gajiyar da ita ba”.
Murmushi ya yi ya zauna dab da ita, don ya san magana ta gaya masa, duk dakin ya amshi bakuncin turaren sa obsession (by CK). Har wani lumshe ido na yi don dadin turaren Yaya. Ya san Aunty Nabeelah bakar magana ta gaya masa, ya rasa laifin da ya yi mai zafi da yake fusata ta haka. Iyakar iyawar sa ya ba ta hakuri dazu kuma ya amsa laifin da take tuhumar sa da shi na watsar da Addah, ya mata alkawarin zai zo ya ga Addah, ya ba ta hakurin rashin zuwan sa da rashin kiran ta, shima ya rasa abinda ya ke hana shi shiga Sokoto, ji yake kamar bazai gane hanyar garin ba, ya fada mata sau da dama ya sha kama hanya amma sai kawai ya ji shi ya karya kan mota ya dawo gida, ya bata hakuri yadda ya kamata amma duk bayan dakika Aunty Nabeelah sake sabunta laifinsa take ya koma sabo fil!
Ta lura shi sam ba ya ganin girman abin da ya yi, ya yi admitting ya yi laifin ne ganin bacin ranta mai tsanani, ban da haka ai ya san Adda lafiya ta ke tunda yana gaishe ta a waya, ta san kuma irin commitments dinsa. Ko ita Addar ba ta korafi sai ita sarkin fushi da fushin wani.
Ya dube ni kadan, “Ki je ki dafa mana wani abun mu ci, matar gidan ta jima da yin barci, ba zata san kin shiga kitchen din ba, but be careful kada ki bata mata wani abun ta gane kin shiga”.
Wani bala'in haushi ya kama Aunty, ta ce, “Ba za ta dafa ba, na ce ba za ta dafa ba din balle ku ce ta lalata muku cooker gass, ko ku ce mata bagidajiya. Ka je ka ci gaba da ci a inda ka saba ci kafin mu zo, na tabbata matar nan azabtar da kai take da yunwa ko makaho ya shafa ka ya san wannan, mu da abincin gidan ka haihata-haihata Maccido. Wanda muka ci ma Allah ya amfana”.
Ya jefar da kai gefe zara-zaran gassun idonsa na lumshewa, ya ce.
“Wai Yaya Nabeelah me ya sa duk kin bi kin tsane ni yanzu? A baya ba mai so na irin Yayata Nabeelah, ba wanda ya isa ya taba mata ni. Amma tunda ki ka zo ban samu tattausar kalma ko daya daga bakin ki ba, a haka ki ke so mu rabu ki koma inda sai na shekara ban gan ki ba?”
Zuciyar Nabeelah ta dan sassauta, kalaman bakin sa sun bata tausayi, kowa ya san Tahir is her favourite brother, so ta ke ta fahimtar da shi kuren sa ya kuma fahimci wannan matar da ya aura ba alkhairi ba ce a gare shi, amma ya ki ya gane inda ta dosa. Kwata-kwata baya ganin laifin matar nan tasa, ko aibun ta. Ba kuma za ta fito fili ta fada ba, Adda ta hane ta da tada tarzoma.
Saboda Allah a matsayin ta na Yayar mijin ta uwa daya uba daya ba kanwar sa ba, wadda ba ta taba zuwa gidan ba ko sau daya, ta cananci irin tarbar da ta yi mata?
Ko sau daya ba ta bata abinci ba, sau daya ta zo ta gaishe ta daga bakin kofa ta gaya ma Ma’u magana, ba su kara ganin ta ba. Babban bacin ran Aunty Nabeelah irin rayuwar da ta fahimci ana yi a gidan, ko abinci ba'a ba shi, matar gidan ce master, shi subordinate. Amma ko a jikin sa.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE & TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI (07030137870)*
((6))Ta sauke numfashi a hankali, yanzun a cikin kallon da ta ke yi masa akwai sassauci da kauna.
“Attahir!”. Ta kirayi sunansa a hankali.
Ya dago kyawawan idanunsa ya dube ta.
“Me ya sa ka wannan ramar?”
Dan murmushi ya yi, ya ce, “Yanayin aikin mu ne kawai da ba hutu”.
Ba tare da ta yarda ba, ta ce,
“Addah yaushe za ka je ka ganta?”
“Insha Allah idan Lubabatu ta haihu, zuwa next month za ta shiga EDD dinta, za mu taho gabadaya”.
“Allah ya raba lafiya”.
Ya amsa da, “Ameen”.
Hannu ya sa a aljihunsa ya zaro bandiran kudi har guda hudu ya dora ma Aunty bisa cinyar ta.
“Ga shi ku sha mai, wannan yarinyar a saya mata wani abu kada Adda ta ce ban ba ta komai ba”.
Aunty ta ce, “Sunanta ASMA’U ba wannan yarinyar ba. Ta gode”.
Sallamar mu da Yaya Maccido ke nan.