← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 33

Sashe 19

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

((10)). Da na ga tsayuwar ba za ta kai ni ba, duk kafafuna sun sage, dole na ja jiki zuwa cikin dakin. Kujerar farko na samu na dofana jikina kamar a ce kyat! In zura a sittin. Da na ji motsin kofar toilet har wata irin firgita na yi. Wai an ce makaho bai san ana kallon sa ba sai an taba shi, ya kamata in yi wa Yaya magana watakila ya manta cewa, dukkannin mu baligai ne, sannan kuma ba muharraman juna ba.
“.....Yaya sai na ga kamar bai dace mu sauka daki daya ba”.
Na fada a matukar darare, kamar wadda ke tsoron furta maganar tata.
Yana shimfida darduma zai tada sallah ba tare da ya juyo ba, ya ce, “Allah koh?”
Sai kawai ya kabbara sallahr sa.
Na yi mutuwar zaune da al’amuran Maccido Taheer, masu neman hauhawar da jini na. Domin bayan ya idar da sallah abinci ya ja ya soma ci, bayan ya gama ya nufi closet yana kokarin sauya kayan jikin sa.
Da sauri na mike na yi hanyar kofa a lokacin da na fahimci Yaya Maccido rigar sa yake cirewa. Runtse idanu na na yi, wani irin gam! Na karasa ga kofar da lalube. Maccido na kallona yana murmushi sosai, ya ce,
“Asma’u!”.
Tsayawa na yi daga tafiyar laluben da nake yi, amma ban juyo ba. illahirin jikina rawa yake yi. Ban san sanda ya tako ya cimmani ba daga shi sai farar singileti da dogon wando. Hannaye na biyu ya kama da duka hannayen sa hagu da dama, ya ce,
“Bude idanun ki ki dube ni”.
Na dan motsa idanun yayin da yawu ya kafe a baki na.
“Open your eyes ki dube ni”.
Girgiza kai na shiga yi, hawaye na zubo min.
“Bai kamata ba Yaya!”.
Ya kara matsowa gabana saura kadan ya hade space din da ke tsakanin mu. Ya ce, “What are you afraid of (me ki ke tsoro)?”
Shiru na yi na kasa amsawa, ni kaina ban san me nake tsoron ba, kawai dai na san bai kamata ba mu zauna daki daya ni da shi. Hatta wannan closeness din da ya assasa a tsakanin mu na san mun keta hurumin Ubangiji.
Jin na yi shiru ban amsa ba ya kai hannu ya dafa kafaduna guda biyu, murya can kasa, ya ce, “Asma’u. I’m your brother ba zan cutar da ke ba. Ina so ki sa a ran ki cewa, kina cikin amanata. Na dauko ki ne cikin amana, kuma cikin amanar zan mayar da ke hannun Addar ki. Idan har kin amince da hakan ki bude ido ki dube ni”.
Dole kowa Yaya Maccido ke wa magana da wannan muryar tasa ya yi masa abin da yake so. Wata irin kasala muryar tasa ta saukar min, hadi da faman murza yatsu na da yake yi su suka taru suka birkita ni. Ko’ina a jikina rawa yake yi, amma a hakan na yi kokarin na bude ido na dube shi don dai ya yarda na amince ba zai cutar da ni din ba. Abin da na hango cikin idanun sa mai girma da zurfi ne da ya shallake tunanin mu. Ai ba shiri na maida idon nawa na lumshe su, shi kuma da wata irin azama ya rungume ni kam-kam a jikin shi.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakeel...”. Na furta da karfin da ya sa ba shiri Yaya ya sake ni. Sai na durkushe a wurin na soma kuka. Kukan da ban san dalilin yin sa ba. Na dai san Yaya ya sa mun yi abin da bai dace ba, ya keta alfarmar Ubangiji sabida sakacin sa da gangan. Ina ga mun kwana a daki daya? Ni gabadaya ma ya canza min, kamar ba Maccidon da na sani ba, handsome, giant, mijin Lubabatu. Wannan ya koma Tahir mai shekaru ashirin da biyar ba wanda ya ajiye ‘ya’ya biyu ba.
Ganin kukan ba zai kai ni ko’ina ba, don Yaya barin gabana ya yi ya shiga jona kettle zai dafa (gahwah-Al-arabiyyah), bai kara bi ta kaina ba. Jakunkuna na guda biyu na jawo na durfafi kofa, gara in je ko kofar dakin da Addah ke kwance ne in dinga kwana, amma ba da ni za a yi wannan katobarar ba. Tunda dai na rike sunan asibitin magana ta kare.
Na murda kofa na sake murdawa, amma ko gezau! Ta ki buduwa. Ban san sanda ya isa ya murza mata mukulli ya zare ba. A jikin kofar na sulale na zauna ina kuka. Kukan da na tabbatar in har da imani a zuciyar sa dole ya tausaya wa halin da na ke ciki.
Ilai kuwa kukan nawa ya dame shi. Ya hana shi nutsuwa. Ya ce, “Asma’u ki yi min shiru. Ki bar ganin ina lallaba ki. To me ki ke tunanin zan yi miki in mun kwana daki daya? Ko kuwa kina so ne ki ce min kin san akwai wata mu’amala tsakanin mace da namiji wanda ni ban san shi ba?”
Kukana ya makale jin abin da ya ce, in ma ban sani ba ai yau ga shi ya nuna min akwai din.
Ya taso ya baro gahwah din da yake sha zuwa inda nake, har yanzu singlet dinsa ce fara kal a jikin shi da dogon wandon kayan da ya cire. Hannu ya miko min ina daga zaune.
“Hold my hand and get up!". Ya fada da muryar da na kasa amincewa ta Yaya Maccido ce. Maccidon nan Ma’abocin izza da kasaita a cikin kannen sa, wanda tsakani na da shi sai hange daga nesa.
Sai na kasa resisting wannan lallashin nasa. A hankali na sanya hannuna cikin nasa. Ya mikar da ni tsaye ya ja ni zuwa three seater din da ya taso, muka zauna kusa da juna. Shayin gahwah din da ya hada a dan kankanin kofin tangaran din Larabawa ya nufo baki na da shi. Juyar da kai na yi alamar ba zan sha ba. Ci gaba ya yi da shan abin sa, sai da ya gama ya ce.
“Now, listen, mu yi magana ta fahimta irin ta Yaya da kanwar sa. Ki lissafo min duk abubuwan da ba kya so a zaman mu, na yi miki alkawarin zan kiyaye. Don gaskiya aljihuna ya yi kasa sosai, ba ni da kudin da zan kama miki wani dakin”.
Shiru na yi ina nazarin kalaman sa, babu alamun wasa a fuskar sa, ko da ma can shi ba ma’abocin wasan ba ne. Sai dai na san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, da kuma wani dalili nasa na daban amma ba don bashi da kudin kama min daki ba. Amma da hankalin sa saboda Allah me ya sa zai yi haka? Me ya sa ya san tun farko bai shiryawa tafiyar ba ya dauko ni? Ni ina duba ya kamata ne, ko da nake karama ashe na fi shi hankali. Don dai ni ban taba jin irin wannan katobarar ba.
“Ke nake sauraro, ina so zan kwanta”.
“Kada ka kuma zuwa kusa da ni, kada ka kara taba ko farce na even by mistake”.
Ban san sanda na fadi hakan ba, na manta ko da wa nake magana, tsabar bacin rai yasa na manta wanene Maccido.
Ga mamakina murmushi ya yi, ya ce,
“Su ke nan sharuddan naki?”
Kai na gyada masa. Na ce.
“Sauran matsalolin zan san yadda zan yi da kaya na. Ubangiji ya sani ba ni da laifi”.

“Consider it done. Don haka kwantar da hankalin ki. I will not dare touch you again. Yanzu mu yi shirin kwanciya kaina ya fara ciwo, kin sa ni magana da yawa”.
To amma kwanciyar Yaya za'a yi ta? Gadon dakin guda daya ne. Karasawa na yi na dauki pillow daya na jefa a kan three seater na kwanta, ko kayan jikina ban canza ba. Rana ta farko ke nan tunda na yi wayo da na kwana ba da kayan barci ba. Ina kallon shi ta kasan ido na ya je closet ya canza kayan jikin shi zuwa pajamas bayan ya rage wutar dakin ya bar dim light.
“Amma da kin koma gadon ko? Kin bar min nan din wuyan ki zai yi ciwo”.
Na dan bude ido na kalli saitin da yake ina auna yadda tsayin shi zai yi occupying three seater, ai kuwa sai dai ya yi ciwon baya.
“Na ci kankanta, na bar maka”.
Murmushi ya yi mai sauti ya dauko quilt din gadon ya rufa mini. Sannan ya karasa gadon ya kwanta.
Da asubah shi ya tashe ni da alama shi har ya dauro alwalla, na je na dauro na zo na same shi bai tayar ba yana jira na. Shi ya ja mu sallar muka yi jam’i cikin daki. Yana gaba na ina bayan sa bayan mun idar. Wata irin nutsuwa da gamsuwa na ji a rai na irin wanda ban taba ji ba a rayuwata, a lokacin da na gabatar da ibadah. Sai na daga hannuwa ina kwararo addu’a na nemawa Addah lafiya dauwamammiya, sannan na yi wa kai na ta gama wa da duniya lafiya.
Bayan wannan ba ni da wani buri don ni a rayuwata ban taba hango wa kaina AURE ba, na san ina son yara, amma na mutane, don ni kam ma bana lissafa kaina a sahun mata. Ni din ba kowa ba ce face Asma’u ‘yar Addah, kanwar Nabeelah Maman Aasim, autar Nene Zainabu. Kamar akwai wani exception tsakani na da sauran mata (ni din ban cika mace ba) watakila da na cika mace da wani da namiji ya taba cewa yana sona, bakin jini na kam ya wuce misali. Yau da na kasance kusa da Maccido, cikin wani kyakkyawan yanayi, sai zuciya ta ta karkace, ta zarme, ta soma son kwatanta ni da mata ‘yan uwana, musamman wadanda ke gidan aure, ashe contentment din da suke samu ke nan in suna tare da mazajen su?
Chapter 19 · 0% Book details