← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 33

Sashe 26

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

A ranar da muka dawo da daddare bayan mun ci abincin da Hawwa ta tanadar mana Yaya ya dube ni kadan ta kasan ido ina zaune jikin Addah. Ya ce.
“Asma’u, dauki kayan mu ki shigar da su sassan mu, da wuri zan kwanta, don gobe sammako zan yi zuwa Abuja, ayyuka sun tarar min fiye da kima, ga wadancan sun dame ni da waya”.
Na gane matar sa yake nufi, ban ce komai ba na yunkura da nufin daukar babbar jakar sa.
Addah ta ce, “Ke Ma'u, koma ki zauna, in ga kafar ki ta taka sassan nan, sai ran ki ya baci. Babu wanda ya san da auran ku, ba'a yi miki jere ba, ba'a shirya ki ba, ba a raka ki gidan miji ba, kawai sai ki kwashi jiki ki shiga dakin miji don ke akuya ce ko? Ko don kin ga na bar ki kin bi shi Madinah? Wannan ai ibadah ce, ba kuma wanda ya isa ya hana ibadah musaman ta hajji da umarah”.
Na koma na zauna cike da kunya ina fadin,
“Da ma fa kayan zan kai masa kawai Adda ba zama zan yi ba”.
Addah ta harare ni, “Sannu tattabara sarkin soyayya, Muhsin ya kai masa, ke da shiga sassan nan sai Nabeelah ta dawo, ta yi miki jere. Mun shaidawa 'yan uwa da abokan arziki auren ku. An yi ko walima ce. Wuce daki na ki kwanta kafin in bata miki rai”.
Ta gaban Yaya Maccido na wuce ina zumburo baki, Adda bata yi min adalci ba, ni kwata-kwata ba nufi na kenan ba, na yi niyyar kai masa kayan ne ma albarkacin idon ta, kada ta gane ba wani shiri tsakanin mu, ba nufi na in tare dakin Yaya ba, ina ganin yadda ya sunkuyar da kai, na wuce, ya bi ni da kallo, a karo na farko duk sai ya ba ni tausayi.
Addah ma ba ta wani jima ba ta shigo, sabida duk a gajiye muke. Muna shirin kwanciya Yaya Maccido ya kara shigowa, daga bakin kofa ya tsaya hannayen sa cikin aljihu, fuskar sa dauke da damuwa tsantsa domin shi yau ya shirya angoncewa. Bai taba tsammanin hukuncin da Addah zata yi kenan ba, Allah ya gani ya yi hakurin da ba duk maza ne zasu iya ba. Amma Addah na kokarin karya masa juriyar sa. Da ya san hukuncin da zata yi kenan, ai da bai yi hakurin da ya yi ta yi ba.
“Asmau ina ki ka saka min cajar waya ta ne?”
Ya fada daga bakin kofa hannayen sa zube cikin aljihu, looking upset. Na rasa wacce cajar waya yake nufi, don ni ban dauka ba, don haka na ce,
“Ka duba cikin karamar trolley din ka, can na zuba komai".
Ya ce, “Ni ban san wata karamar trolley ba, in za ki dauko ki dauko min, ina falo”.
Addah ta ce, “Maccido ko ka fi kowa naci, yau ba kai ba hada daki da Ma’u, ka bace min da gani ko in sabar muku dukkanin ku”.
Cikin kunkuni ya ce, “Haba Addah? Daga neman charger? Na tafi ku kwana lafiya. Ba nufi na kenan ba".
Addah ta yi murmushi ta ce, “Allah ya tashe mu lafiya”.
Sosai Yaya Maccido ya shaqa, yayi fushi sosai, ya juya yana fadin, “Na tafi Addah, ki yi ta ajiyar 'yar ki a daki, in na ga ta uku sai in kara, tunda Allah ya bani dama”.
Ta kara sakin murmushi ta ce, “ko biyu ne ma ka karo, ni dai tunda Ma'u na ta shiga, kowa ma kake so kayi ta kawowa’.
Attahir ya dago lumsassun idanun sa muka hada ido, ya sakar min harara ganin ina dariyar su ciki-ciki, bayan shi ya fada ne don mu ji haushi ni da Addah, yayin da ni kuma na lumshe masa nawa idanun cikin wata irin siga wanda bansan lokacin da na yi hakan ba...
Da sauri ya juya ya fice ya bar dakin.
Chapter 26 · 0% Book details