← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 33

Sashe 20

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gari ya soma haske, ni da Yaya babu wanda ya motsa, muna nan zaune a inda muka yi sallah kowa da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa. Wani yanayi ne na nutsuwa da ban san yadda zan kwatantashi ba ban kuma taba tsintar kaina a ciki ba. Bana so ko kuda ya gifta ta gabana don kada ya katse min bakin abubuwan da nake ji a raina. Don kada Yaya ya tashi daga gabana, ji na yi tamkar ya zame min garkuwa daga duk abin da zai iya cutar da ni.
Yaya ne ya fara tashi, sabida lokaci ya ja sosai. Toilet ya wuce kai tsaye. Wanka ya shiga, yayin da na soma tattare kayan da suke watse a kasa, na maida dakin neat. Ya fito sanye da rigar tawul ta wanka ya daure igiyar daga tsakiyar cikinsa. Kallo daya na yi masa ban kara marmarin maimaitawa ba domin kuwa kirjinsa na hango wanda ke rufe luf! Cikin lallausar suma baka sidik. Shi ma dai me ya sa yake saka irin wadannan kayan a gabana? Ai bai kamata ba. Ko da yake na dade da fahimtar shi bai san ya kamata ba. Tun da ya farlanta mana zaman daki guda din, da sai ya dau kayan sa a hannu ya shiga toilet ya canza tunda ya ce zaman namu tare ya zama dole.
Dan gajeren tsaki na yi hadi da zunburo baki, wanda ban san cewa ya shiga kunnen Yaya ba. Na juya na ba shi baya ganin ya fiddo kaya zai saka.
“Are you pouting at me (ni ki ke zumburo wa baki)?”
Na yi saurin girgiza kai tare da cewa cikin karkarwar murya,
“Amma Yaya sai na ga zai fi dacewa ka dinga saka kaya a toilet”.
Ina jin sautin murmushin sa, ya ce, “gashi ni ban iya takura wa kaina ba, ko ba komai na san daga ni sai kanwata a dakin”.
Kamar in ce masa, ai ni ba Nabeelah ba ce, sai na yi tunanin zai ja zancen zuwa wata ma’anar daban, don haka na ja baki na na yi shiru.
Sai goma na safe muka gama breakfast, wanda aka shigo mana da shi daga hotel din. Yaya ya isa ga madubin dogon yaro yana murza hula a kansa, sai da ya tabbatar ta zauna sosai, sannan ya dauki turarukansa biyu yana fesawa (obsession da oud abyad) da ya saya a nan Jeddah. Ya gama ya juyo inda nake na yi tagumi, domin haka kawai nake fama da yawan faduwar gaba da kasala.
“Zan je asibiti Asma’u, daga nan zan je wajen wani abokina a King Abdul-Aziz University, sai wajen azahar zan dawo. Za su shigo miki da abincin rana”.
Na marairaice, “Yaya don Allah zan bika, in son sanin halin da Addah ke ciki”.
“Ko mun je ba za su bari mu ganta ba, ki yi hakuri ki yi zaman ki. Idan Nabeelah ta zo sai ku dinga zuwa duk inda ku ke so tare.
Ba da son raina ba na hakura, na ce, “To ka sayo min KFC”.
“Ita kadai?”
“Eh”.
“To sai na dawo, take care”.
Wani irin dadi na ji a raina, ashe haka mata ke ji idan suka samu kulawa ko da ta fatar baki ce daga mazan su?
Sai azahar din kuwa ya dawo, ya kawo min KFC mai zafi da Laban mai sanyi. Daga nan ya kara ficewa bai dawo ba sai dare.
Yau ma irin kwanjiyar jiya muka yi, ina kan kujera yana tsakiyar gado, ina jin shi yana ta kiraye-kirayen waya da daddare. Ya kira matarsa sun sha hira, amma bai zurfafa hirar ba, sannan ya sassauta kalaman sa.
Duk da haka sai na samu kaina da matukar jin haushin Lubabatu, bayan a zahiri ita ya kamata ta ji haushi na ina nan ina more mata miji, har da kwana daki daya da shi babu sidi ba sadada. Idan har ta san muna taren ke nan, na fi kyautata zaton bai gaya mata da ni aka yi tafiyar ba ma, don lafiya-lafiya suke hirarsu.
Washegari ya ce min zai je cikin jami’a wajen Musbahu abokinsa, lakcara ne a can. Rokon sa na yi ta yi a kan zan bi shi har dai ya yarda, amma ya ce sai na sa niqaab. Ina ta zumburar baki na sa niqab din muka jera ni da Yaya muka fito.
Mai Ajrah ya shigar da mu har cikin King Abdul-Aziz University, daga nan muka taka zuwa ofis din abokin nasa. Mai fara’a da shi, baki mai zubin Mallawa.
Ya ce da Yaya, “Maccido yau ba kai ne bakona ba, Madam ce, don haka ita zan fara yi wa barka da zuwa”.
Yaya ya ce, “Musbahu ka ki aure ko? Har mun tara yara kana nan a tuzurun ka”.
Murmushi ya yi, ya ce, “In za ka ba ni kanwar nan taka me zai hana in biya sadaki kafin ku koma Nigeria?”
(Na dage niqaab dina sama don in sha iska shi ne har Musbahu ya ga fuskata). Na juya na kalli Yaya sai na ga duk annurin fuskar sa ya kau, kuma bai bi ta kan zancen Musbahu ba. Tun daga nan in muka hada ido sai ya yi ta dalla min harara. A karshe ma hirar ta ki dadi, ya ce da Musbahu za mu koma, yana so ya shiga asibiti.
Tunda muka hawo ajrah Yaya ya soma fada, fada yake yi tamkar ya kai hannun shi jiki na.
“Na ce ba za ki biyo ni ba ki ka kafe min kahon naci, ashe don ki zo ki tallata wa maza fuskar ki ne. In ba haka ba me ye na cire niqaabin a gaban maza? Ko an ce da ke in kin yi hakuri har gida Allah ba zai kawo miki mijin aure ba?”
Fadan yaya sai ya koma ba ni dariya, amma na san ko giyar wake na sha ban isa na yi ta ba a yadda yake matukar fusacen nan. Kadan ya rage ya kai min mari. Saboda Allah ina ruwana da wani niqaabi ni ba matar kowa ba, ba ‘yar takari ba? Na hadiye dariya ta ban yi ta ba, don na lura ba karamin fusata ya yi ba.
Yau ko ‘yar KFC din bai saya mana ba, tunda na bata masa rai. Ya rantse ya sake rantsewa ba zai kuma zuwa ko'ina da ni ba, in dankare a dakin hotel.

A hankali cikin ‘yan kwanakin da muka yi tare nake ta fahimtar wane ne Attahir (Maccido)? Sanin da tunda aka haife ni nake zuwa gidan su har rasuwar iyaye na da dawowata gidan su gabadaya ban taba yi masa ba. Na lakance shi, wata irin lakanta da bana jin ko matar shi da ya kwashe shekaru biyar tare da ita ta yi masa irin ta. Na san irin abubuwan amfanin sa kama daga suttura, turare, bath kit (kayan wanka) kayan askinsa (shaving kit) na Arganavita. Na san duk irin abincin da ya fi so da abin shan sa, na san likes and dislikes din sa. Na gane halayen sa ciki da ba. Na lakance shi karshen lakanta, ta yadda na tabbata ranar komawar mu gida tabbas zan kasance cikin kewar sa.
A baya ina masa kallon wani mutum mai izza da girman kai, ina masa kallon mai wasu irin baudaddun halaye da suka sha bamban da na mutane. A dan zaman nan namu cikin birnin Jeddah sai na gane Yaya Attahir Maccido yana daga cikin kariman mutane; wato mutane ma’abota kirki da karamci ga duk wanda zama ya hada su da shi na dan lokaci mai tsawo.
Babban abin da ke burge ni da Yayan namu shi ne; tsaftarsa, ba ya kwanciya sai ya yi wanka, haka in ya fita ya dawo sai ya yi, in ya sa kaya sau daya ba ya maimaita su sai an wanke an goge. Bai cika sanya kananan kaya ba sai in a gida zai zauna. Kusan kullum cikin shaddoji, voile da yaddidikan filtex masu karshen tsada da aka yi wa dinki tazarce yake rayuwar sa. Dinkunan sa kullum simple, ba'a cika su da ado, amma in ka duba links dinsu za ka samu masu daraja ne sosai.
Zan iya kwana in wuni ina fasalta muku wane ne Maccido? Don haka na bar wa mai karatu sauran, ya gane cewa Attahir is classique, perfect, decent and genius. Ta yadda in na zauna sai in yi ta kintace da hasashen Lubabatu wace irin sa’ar zuwa duniya ta yi?
Gobe ne Aunty Nabeelah za ta sauka a Jeddah, kuma a gobe ne za a bar mu mu ga Addah, don haka don zumudi yau barci na ragagge ne. Yaya Maccido ko barcin sa ya shaka har da minshari.
Tun asubah bayan mun idar da sallah na fada wanka, ganin rawar jikin da nake yau sai ya shiga bata lokaci yana yi min yanga yadda yake so, na ce mu fita tun bakwai sabida Nabeelah sha daya na safe za ta sauka. Tunda akwai tazara tsakanin cikin gari da airport. Yaya Maccido ya ce, tabdi ai shi bacci ma zai koma, sannan sai ya tashi zai yi wanka. Ya shige cikin quilt ya bar ni a zaune kamar na fashe da kuka.
Haka na daure na kyale shi na zauna ban da aikin duba agogo ba abinda nake yi. Karfe tara na kure karar talabijin don dai ta tashe shi.
Ya tashi yana yamutsa fuska ya shige toilet. Nan ma sai da ya ci rabin awa ya fito ya shiga shiryawa lakakai-lakakai. Na shige cikin duvet yadda nake yi duk lokacin da na fahimci zai canza kaya, tunda shi hakan ba damuwar sa ba ne.
Ya dau turare yana fesawa na mike na rataya jaka ta na nufi kofa zan saka takalmi. Amma sai Yaya ya ce, wai shi sai ya karya kumallo. Hawayen da ke makale tun dazu na bari suka zubo kawai.
Ya kama baki yana min dariya, wai Nabeelah ko uwata ce sai haka.
Ganin na ki zama na babbake a bakin kofa ina ta share hawaye, ya hakura da cin abincin ya zura takalmin shi tare da daukar wayoyin shi guda biyu ya zuba a aljihun shi, ya ce.
“Mu je don Allah, kada ki sa ni in kware da wadannan kananan idanun naki”.
Chapter 20 · 0% Book details