Sashe 14
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Na kwantar da kaina jikin gadon da Adda ke kwance ba ta san wanda ke kanta ba. Shesshekar kuka nake yi a hankali cikin rauni da karaya nake fadin, “Adda, Allah ya tashi kafadun ki, Allah ya ba ki lafiya Addah… Ba ni da kowa sai Allah da ya halicce ni, sai ke…”
Kuka nake yi mai motsa zuciyar duk wani mai saurare da muryar da ke nuna maraici na. Alamun zaman mutum na ji a kujerar da ke kusa da tawa, hanci na ya surnano min wani lallausar kamshi na turaren obsession (by CK).
Hannu ya kai a hankali ya kama hannun Addah wanda babu karin ruwa a jiki. A hankali na dago ina bin shi da kallo, kallon da a sannu yake sauya kala yana komawa na kiyayya… na tsane shi, na tsane shi don na san duk matsalolin da Addah ke fama da su na hawan jini da yawan bacin rai shi ne sila. He is very selfish… kansa kawai ya sani da shaidaniyar matar sa.
Ko kusa bai zame wa Addah sanyin idaniya ba, haihuwar sa ba ta kare ta da komai ba sai tulin bacin rai. Ta dauki soyayyar sa da damuwa da lamarin sa ta aza a ranta har ya yi mata illah. Rabon da mu ganshi yau watanni bakwai ke nan, sai yanzu da ya ji an ce Addar na gargarar mutuwa shi ne ya wani kwaso jiki ya zo. To me ya zo ya yi mata? Ko ya zo ne don bakin cikin sa ya karasar da ita zuwa kushewar ta?
Ban san sanda na saki wani mugun tsaki ba. Na ji na tsani Yaya Maccido sakamakon treatment din sa ga Addah. Tsana mai yawa, wadda ta cire min burgenin da yake a baya.
Na mike zan bar wajen, kallon mamaki Yaya Maccido ya bi ni da shi, na san tantama ya ke kan tsakin da ya ji, da shi nake ko da wa? To in ba da shi nake ba da wa nake? Mu biyu ne kacal a dakin, sai Adda da ke kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Wannan ba lokacin da zai tsaya yana tantance Ma’u ta yi masa tsaki ba ne ko a'ah. Ya zo ne da kyakkyawar niyya ta YI WA KAN SA HISABI tsakanin sa da Addar sa, tare da yin repenting manyan kura-kuran sa. Repenting din da zai baiwa kowa mamaki. Ya kuma wanke zuciyar kowa nasa. Ya amincewa kansa bai kasance Da mai farantawa mahaifiyar sa ba. Ya kasance cikin wani irin ajizanci na lokaci mai tsawo. Amma yanzu jin kan sa yake kamar wanda aka tasa daga nannauyan barci. Ya yarda tunda ya auri Lubabatu ya canza akalar rayuwar sa bakidaya.
A yanzu kam ya yarda Lubabatu ba ta jan shi ga hanyar da zai samu rahmar Allah. Ya tabbata Addah ta yi hakuri a kansa hakurin da iyaye da yawa ba za su yi shi ba a kan ‘ya’yan da suka haifa. Yana rokon Allah ya ara masa dama ya gyara kuskuren sa, ta hanyar da ba wanda yayi tsammani, ko da wannan shi ne abu na karshe da zai aiwatar a duniya.
Hannun Adda ya kama ya rike gam! Hawaye na fita daga idanun sa. Daidai lokacin da likita da nurse suka murdo kofar suka shigo, ni kuma ina bayan su. Na je ne na kira su don su cire mata karin ruwan da ya kare su daura mata wani. Kallo daya na yi wa Yaya Maccido na fahimci kuka yake yi. Na kyabe baki a raina ina fadin,
“Daga baya ke nan!” ....wai sadaka da bazawara.
Ko ganinsa idanuna ba sa son yi, saboda yadda tsanar sa ta lullube min zuciya, har cikin kokon raina.
Gefen gadon Addah na koma na tsaya na harde hannaye na a kirji, na kuma tokare kafata daya a jikin bango. Ko kallon inda yake bana yi, addu’a kawai nake wa Addah cikin raina. Ina ji yana magana da likitan kan ya tattara masa bayanan komai na Adda, nan da kwana uku zai fita da ita Jeddah - Saudi-Arabia a yi mata aikin a can. A raina na ce,
‘Ta baya ta rago’.
Bayan fitar likitan ya dan saci kallon inda nake tsaye. Cikin taushin murya ya ce,
“Ba kwa bukatar wani abu? Zan je gida in dawo”.
Na zumburi baki, “Ba abin da muke bukata, in ma akwai Muhsin zai kawo idan zai zo”.
Ya dan tsura min ido kamar mai son tantance tone din murya ta mai alamun akwai fusata a ciki.
Kyabe baki ya yi, ya mike ya fice a ransa yana fadin, ko me na yi masa shi ya ja wa kansa da ya kula ni, bayan ya lura yau fizga nake kamar mai bugun aljannu.
Yana komawa gida sashen sa ya nufa, ya yi wanka, ya yi sallah ya canza kaya marasa nauyi ya kishingida a sofa bed. Wayarsa ya dauka ya kira Aunty Nabeelah. Sun dade suna magana wata irin doguwar magana mai kama da doguwar jayayya, daga karshe Nabeelah kuka ta koma yi masa a wayar tana sanya mishi albarka.
Ta ce, komai dare ya tafi Dogondaji, ita kuma za ta kira Bebeji.
Washegari Al-Qasim Yaya ya sa ya dauke ni muka tafi immigration don yin fasfo, don Yaya ya ce da ni za a tafi Jeddan. Cikin kwana daya fasfo ya fito aka shigar da neman visa na Addah kuma aka sabunta shi.
Ranar da za mu tafi tun dare na hada duk abin da zan bukata, washegari ambulance ce ta dauki Adda zuwa filin jirgi. Ni da Yaya kuma muna motar Al-Qasim, bai koma gida ba sai da ya tabbatar jirgin da muka shiga na emirate mai zuwa Saudi-Arabia ya bar kasa.
Yau sai na ga Al-Qasim ya zame min kalar tausayi, he look pale. Na nemi Muhsin na rasa tun jiya, ba inda ban duba ba ban ganshi ba, a jiya da safe dai ya ce min zai dan yi balaguro, amma ba jimawa zai yi ba sai dai har mu tafi wata kilan ba za mu hadu ba. Aunty Nabeelah ta kira ni ta wayar Yaya ba da son ransa ba ya ba ni wayar muna gab da tashi ta ce, “Ki ce alhamdulillah, subhanallah sau uku”.
Na yi yadda ta ce. A daidai lokacin dana gama fadar hakan ne naji gabana ya tsinke ya yi mugun faduwa, dai-dai lokacin da daqiqar agogon hannu na ta nuna karfe sha daya na safe, kirji na ya hau yin wani balli-balli har sau uku. Sai ta ce cikin sautin murmushi.
“Safe journey my lovely Sis, ki kula da kan ki, ki kula da Addah, zan iske ku a Jeddah next week Insha Allah!"