← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 33

Sashe 27

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari tun kan mu tashi Yaya da Al-Qasim wanda zai tuka shi sun yi sammako sun kama hanyar Abuja.
Da kayan mu suka iso na ba wa Muhsin tsarabar sa tare da ta Al-Qasim, na ce,
“Ni na rasa abin da na yi wa Al-Qasim tunda muka dawo ba ya yarda mu gaisa”.
Muhsin ya dinga kyalkyala dariya, ya ce, “Kishi ya ke Ogan sa ya kasa shi. Wai ke kina nufin ba ki taba sanin Al-Qasim son ki ya ke yi ba?”
Baki sake na ke kallon Muhsin, "So? Wane irin so?”
Ya ce, “So na aure, so na soyayya. Ya dade yana son ki, ya gama burin auren ki, ya jinkirta ne zuwa ki gama lesson din ki ki sake waec don kar ya raba miki hankali. Sai kawai ga wannan sharp-shooter din ya zo rana daya ya yi masa kamshin mutuwa ya sure ki kamar kiftawar ido, kin ga ko ai dole ya yi kishi”.
Mamaki ya hana ni cewa komai, don dai ni ko da wasa ban taba kawo hakan a raina ba, kuma ban taba ganin wata alama daga gare shi mai nuna hakan ba. Sai na ji tausayin shi ya kama ni, na ce,
“Muhsin zan masa addu’a Allah ya ba shi wadda ta fi ni, kuma don Allah ka ba shi wannan tsarabar. Ba zan taba mancewa da taimakon da ya yi min ba a rayuwa, shi ne silar da na fara gane karatu, har na yi developing hope a cikinsa. Shi din mutumin kirki ne ko don yadda yake kula da Adda da komai na gidan nan. Da ina da kanwa da na ba shi”.
Muhsin ya ce, “A kunnen Yaya”.
Na ce, “Ka yi sauri kada kuda ya riga ka, in ya kore shi ai komai kanka zai dawo. Yanzu kuwa ka samu kana karatun ka a nutse babu stress a kan ka”.
Tun tafiyar Yaya na koma ba fuss ba ass! Ban san na saba da shi ba, ban san na shaqu da shi ba, ban san zan yi kewar sa ba, bansan soyayyar sa ta shige ni a dan zamqn da muka yi tare a Jeddah ba sai da ya tafi ya bar ni. Ya kuma daina kira na. Duk na zama wata irin sukuku! Soyayyar Yaya Maccido sai kara shiga ruhi na ta ke a hankali tana kassara ni, tana karar da kuzari na, tana tafiyar da duk wata walwala ta a cikin gida.
Adda ta kasa gane kaina, tambayar duniyar nan ta yi na ce ni ba abinda ke damu na, akai-akai ina ji yana kiran Addah amma ni ko sau daya bai kira ni ba. Wannan abu ya dame ni matuka. Wani lokacin sai na dauki waya da niyyar kiran sa sai in fasa, gudun ko yana tare da matar sa.
Yau ma ina zaune gefen Addah ina cin abincin dare Yaya ya kira wayar Addah, ina ji suka gaisa suka cigaba da hira, har suka yi sallama ban ji Yaya ya neme ni ba, itama Addah bata ce gani a kusa ba. Hawaye ne na ji zasu bada ni, don haka na tsame hannu na daga cikin tuwon na mike na yi uwardakin Addah, kwanciya na yi rigingine akan gadon Addah ina hawaye, zuciyata na wani irin suya. Ban ji shigowar Addah da zaman ta a gefe na ba, sai sunana da na ji ta kira.
"Ma'u me yake damun ki? Duka a kwanakin nan ina lura da ke cikin damuwa kike" "babu komai Addah kai na ne kawai yake ciwo" murmushi Addah ta yi, ga mamaki na sai cewa ta yi "in shi bai kira ki ba, ke ba saivki kira shi ba? Ba mijin ki ba ne? Maccido tun yana yaro mai son kulawa ne, mai son a bashi girma, sai kin tashi tsaye sosai wajen kula da shi, in ba haka ba zaki sha wahalar sa. Ungo nan kira shi da kan ki ki gaishe shi" ta miko min wayar ta.
Girgiza kai na yi "Addah in yana kusa da matar sa fa? Kika sani ko ya gaya mata auren mu ko bai fada ba? Bana so in ja masa matsala" Addah ta daure fuska sosai ta ce "na ce ki kira shi, kada ki yi musu da ni Ma'u".
A sanyaye na karbi wayar daga hannun Addah, bata bar wajen ba sai da ta tabbatar na kira lambar Yaya har ta fara ringing. Kayan sallahr ta ta dauka ta bar dakin.
Ga dai waya ta shiga, kuma Yaya Maccido ya dauka, amma sai na kasa magana. Shi da kan sa ya gaji da shirun ya gane ba Adda ba ce ni ce, ya ce "Asma'u yau kin tuno ni?" Hawaye suka ciko ido na, na ce "kullum ma ina tuna ka" "ban yarda ba Asma'u, da kina tuna ni da kin neme ni, you don't care for me anymore. Duk a cikin rashin son ne? Ranar da zan taho ko sallama baki zo mun yi ba, duk yadda zan yi in ja ki a jiki don ki sake da ni ki kuma karbe ni a matsayin miji na yi Asma'u, ban san me ya sa ba kyaso na ba".
Hawayen dake cike a idona suka idasa gangarowa akan kundukuki na, sabida yadda Yaya Maccido ya ke maganar, dole ya raunata zuciyar diya mace, balle mai saurin kuka iri na, da kyar na iya cewa "Yaya ni ban fada ba...." "kin fada Asma'u, ba sau daya ba ba sau biyu ba akan ido na, ba kya so na balarabe kike so, kuma na yi miki tsufa, hmmm, Nabeelah ma shaida ce kan kin fadi hakan" "ka yi hakuri Yaya na tuba, wasa nake yi, na tuba na bi Allah na bi ka". Dariya ya yi ya ce "baki duba kan nawa kin gani ba fa ko akwai furfura ko babu, kike saurin janye maganar ki. Ni dai na san ina son Asma'u, ko ita tafi kowa tsufa a duniya. Zan tabbatar miki da hakan duk ranar da kika bani dama".
Zuciya ta ta yi wani irin sanyi daga kuncin da ta ke ciki a baya, sakamakon kalaman Yaya Maccido "amma Yaya me ya sa ba ka kira na? Tunda ka tafi ko sau daya baka kira ni ba" na fada cikin shagwabar da ban san ina da ita ba. Yaya ya ce "because i want to confirm if you care for me or not, yanzun ma ban tabbatar da hakan ba idan ba na gani a zahiri ba" "me zan yi Yaya ka yarda na damu da kai fiye da yadda kake tsammani?" "Ki yarda ki tare a dakin ki da zarar na zo, shine kawai zai tabbatar min kin damu da ni Asma'u, kin kuma karbe ni a matsayin mijin da Allah ya zaba miki, kin san na yi hakuri ko? Hakurin da maza da dama iri na ba za su iya ba".
Kunya ce ta kama ni na kai tafin hannu na na rufe fuskata tamkar Maccido yana gaba na. Domin na gane hakurin da yake nufi ya yi, Nace "Yaya ni ba ruwa na sai abinda Addah ta ce" "ai na san bakin ku daya ke da Addar taki, duk cikin ku babu mai tausayi na, shikenan, kada ku zarge ni in na nemo mata ta uku".
Wani dunkulallen abu ne ya zo ya tsaya min a kahon zucci, wuta ta dauke min, nace "Yaya....." "ki bar ce min Yayan nan, ni ba Yayan ki bane yanzu, nafi so na ji kin ce Maccido" "bazan iya ba Yaya, because i respect you much,..... don Allah kada ka kara zancen auren nan....zuciya ta za ta buga Yaya!"
Ina jiyo sautin murmushin Maccido, "Then sai kiyi kokari ki zama cikakkiyar matar aure in ba haka ba aure ba fashi, ba daya ba har biyu. Na yi aure don ina bukatar kara aure amma sai gasa ni kuke Asma'u, yaya kike so in yi da rai na?" Murya ta na rawa na ce "Yaya in ka daina maganar kara aure ko me kake so zan yi maka" Yaya Maccido yayi murmushin da na jiyo tashin sa cikin wayar ya ce "promise?" "Yes, i promised" "to ki shirya min tarba ta musamman, ranar Juma'a ina tafe insha Allah" "Allah ya kawo ka lafiya Yaya" "call me Maccido, ko sau daya ne please Asma'u" na kai tafukana na rufe fuskata, wani irin feelings na fizgar zuciyata zuwa gare shi, "ba zan iya ba Yaya, don Allah ka yi hakuri" "ban yi hakurin ba Asma'u, na bi ki bashi, idan nazo sai kin fadi 'Maccido' a kunne na na ji" "na yi alkawari Yaya in ka zo ga ni ga ka zan fada" duk dai don in samu ya zo din, na yi kewar sa yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba.
Yaya Maccido ya ce "kina ta daukar alkawarin da ba zaki iya cikawa ba, first of all kin yi alkawarin yi min duk abinda na ke so, sannan kin yi alkawarin zaki kira ni da sunana a gabana. Well, don ke zan kamo hanya Asma'u don haka i expect a very warm reception from you" Murmushi na yi na canza position din rikon wayar daga dama zuwa hagu, ji nake tamkar in shiga cikin wayar in tadda Attahir, gaskiyar sa ne ina ta daukan alkawarurrukan da bani da tabbacin zan iya cika su ga ni ga shi, yanzu ma don ba na ganin sa ne.
Shigowar Addah ya sa nayi maza na kashe wayar ba tare da mun yi sallama da Yaya ba, ban gayawa Addah Yaya ya ce zai zo Juma'ah ba sabida kunya. Addah ta ce
"Ma'u kashe wayar nan haka ki je ki kwanta, Allah ya tashe mu lfy".
Chapter 27 · 0% Book details