← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 33

Sashe 12

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Yau bayan ya tashi daga mall ya zo gidan kamar yadda ya saba da manyan ledoji a hannun sa, ya yi sallama ya shigo falon, daga ni sai Adda muna kallon talabijin.
Addah ce ta amsa, ni kam a zuci na amsa. Na kalle shi sau daya na dauke kai, a raina ina fadin,
“Ga fa duba-rudu ya iso”.

*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*

https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d

YIWA KAI HISABI

Har gaban Adda ya karasa ya tsugunna ya gaishe ta, sannan ya aje mata ledojin da ya shigo da su masu tambarin ‘Maccido mall’, kayan amfanin gida ne da ya kan debo mata a shagon su da toiletries da abincin gwangwani iri-iri. ‘Yar karamar ledar da ta rage a hannun sa ya iso gare ni ya aza min bisa handle din kujerar da nake zaune,
“Autar Adda ga tsaraba na yo miki daga mall”.
Dauka na yi na bude babu ko an gode, sabida yadda yake ba ni haushi da kallon sa, amma ganin choculates ‘yan uban-ubansu masu tsada ban san sanda bakina ya bude ya yi godiyar ba. Na fiddo mars da kit-kat na bude na gutsira kunnena har motsi yake.
Adda ta ce, “Ki dai sha kadan, kin san lokacin watan ki ya kusa, kada ki zo kina min murkususun nan naki”.
Wata kunya ta kama ni, na saci kallon Al-Qasim, sai na ga bai ma gane zancen da Addah ke yi din ba. Zama ya yi bisa centre carpet daga gefen Addah yana yi mata bayanin ribar da ake ta samu a wannan shekarar.
Rannan kafin ya shiga mall ya zo gidan da sassafe yana sauri, bayan sun gaisa da Addah ya tambaye ta, ko na tashi daga barci? Addah ta ce, bari ta dubo ni. Ta same ni tashina ke nan ina shirin shiga wanka, ta ce,
“Ma’u zo mana, Al-Qasim yana nemanki”.
Na zumburo baki, “Duba-Rudu za ki ce Addah!”.
Dakuwa ta yi min, “Ungo naki, bana son raini wa na gaba. Kada in kara ji kin ce masa Dubarudun nan, ke da wane idanun ki ke dubansa har ki ka san yana duban naki?”
Sake zumburo baki na yi, na daura zani bisa rigar barci na na dora hijabin sallah ta na bi bayan Addah.
Yana tsaye tsakiyar falon rike da kwamfutar kan cinya (laptop) a kunne. Ya yi kwalliyar sa tsaf yadda ya saba. A perfect gentleman. Ina fitowa ya tako zuwa gare ni da saurin sa muka game a tsakiyar falon.
Ya ce, “Yauwa kanwata, kin fito?”
Na gyada kai.
Ya sake matsowa da laptop din.
“Wani dan taimako za ki yi min, ai kin iya microsoft excel ko?”
Cikin jin kunyar kada in bada kaina in na ce ban iya ba, ban ma san mece ce ita din ba, na gyada masa kai kawai.
“Yauwa! Please Master ya kira ni Abuja yanzun nan (Yaya Maccido), ga shi ina da muhimman bayanan da ban shigar cikin kwamfuta ba. Ga su a rubuce bisa sheet din nan don Allah daga yanzu zuwa dare ki shasshigar min”.
Ya miko min takardun da kwamfutar.
Ban yi kasa a gwiwa ba na karba. Ya yi min murmushi tare da godiya.
Ya ce, “Me zan kawo miki?”
Na ce, “Babu komai, ka gaida min Ihsan kawai”.
“Za ta ji, insha Allah”.
Da haka ya yi mana sallama ya tafi.
Na koma daki na aje (laptop) bisa gado na na zuba mata ido ita da takardun. Kwata-kwata ba abin da na fahimta. Wannan shi ne karshen tozarci idan Al-Qasim saurayin da ke ji da kansa ya fahimci zero nake a boko. Duk kidifirin da na ke masa ai dariya zai koma yi min tunda (empty-head) gare ni. Wasu hawaye suka ciko idanu na, na ce bari in yi wanka in zo in jagwalgwala abin da ya sauwaka, da babu gara ba dadi.
Bayan na yi wanka doguwar riga kawai na saka na zo na dinga danne-danne a kwamfuta, shiga nan fita can ban san sunan komai ba, ko abin da nake yi daidai ne ko ba daidai ne ba.
Har azahar ina abu daya. Sai da Addah ta turo Hauwa ta gaya min ga Nabeelah a waya, sannan na rufe kwamfutar ba tare da na yi switching off ba, sai da cajin ta ya kare ta kashe kanta.
Sai da Al-Qasim ya yi kwana biyu a Abuja sannan ya dawo, don shi ne ke kula da sabon ginin wani mall din ko ko Plaza da Yaya Maccido ke yi a Abuja. Wanda ba shi da maraba da na Sokoto a komai..
Da daddare ya zo gidan suka gaisa da Addah. Tunda na ganshi gabana ya fadi don tunda na aje kwamfutar sa ban kara bi ta kanta ba, ko dan caji ban sa mata ba.
Ya dube ni da murmushi, ya ce, “Ihsan na gaishe ki tayi ba ki masha Allah ga shi tana gudun ta ko’ina”.
Na yi murmushi sosai, na ce,
“Oh my daughter”.
Ya ce, “Maza a dauko min aikin da na sa ki, Master na jira in tura masa yanzu”.
Ba musu na mike kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, na dauko kayan sa na kawo masa. Ya karba yana shirin kunnawa ya ce, “Ya? Babu caji ne?”
Na ce, “Ban saka ba”. Na fuske abuna, don ma kada ya kara yi min wata tambayar.
Da kansa ya tashi ya je ya jona ya bata lokaci ta kama sannan ya kunna. A hankali yake duba abubuwa da aikin da ya sa ni Nana Asma’u in yi masa.
Duk wasu muhimman applications masu dauke da bayanai masu muhimmanci na goge masa su. Da ya shiga excel don ganin aikin da ya sa ni sai ya tarar na cika raws din da sunana Asma’u Adam Bebeji da kuma ABCDEFG.
Mamaki, takaici, tu’ajjibi suka taru suka lullube Al-Qasim Ka'oje. Me hakan ke nufi? Ba ta iya ba ko shakiyanci ne ta jaza mai asara haka?
Amma ai ‘yar makaranta ce, ajin karshe a sakandire, makarantar ma mai aji da mukami, ko last week shi Adda ta tura ya biya (school-fees) dinta kudi na gugar wuri masu yawa. Kada dai a ce asarar kudin tara ake yi a kan Asma'u?
Amma da yake mai ilmi ne bai nuna komai a fuskar sa ba. Ya dauko murmushin karfin hali ya dora wa kyakkyawar fuskar sa.
“Ma’un Adda, na ga aiki ya yi kyau fa na gode”.
Na saki baki ina kallonsa, “ABCD fa na rubuta maka. Ni ma su kadai na iya, shi ya sa na rubuta maka su sai kuma sunana”.
Adda ta rage sautin talabijin ta bada attention dinta ga hirar mu.
“Al-Qasim wai me ye?”
Ya ce, “Adda aiki na bai wa Ma’un ki ta taya ni, sabida Master ya kira ni Abuja da sauri, shi ne aka rubuta min Asma’u Bebeji maimakon aikin nawa, aka kuma yi min ciko da ABCD aka ba ni alakoro da goge min duk wasu muhimman bayanai da ke cikin kwamfuta”.
Adda ta juya tana sakin dariya. Dariyar da ta kular da ni na tashi na bar musu falon. Sai da Adda ta yi dariyar ta ma'ishi sannan ta ce,
“Wa ya aike ka? Kuma ba ka tambaya ta iya ko ba ta iya ba kawai sai ka ba ta?”
Ya langwabar da kai cike da takaici, ya ce, “Sai da na fara tambayar ta fa ta ce ta iya”.
Adda ta sake yin dariya ta ce, “Ma’u da ka ke ganinta kanta babu komai na karatun boko. Tunda aka haife ta haka take, sunan zuwa makarantar ta "jeka-na-yi-ka". Ina tsammanin daga sakandire ta gama shiga aji don ba za ta iya karatun jami’a ba”.
Maganar ta doki Al-Qasim sosai, domin kuwa shi so na yake, so na hakika. Wanda yake fatan ya kai mu ga siradin aure ya samu tsatso daga gare ni. In haka ne to me zan koya wa ‘ya’yan sa idan yayi kasadar aure na?
Ya dubi Adda fuskar sa dauke da tausayi da soyayyar Asma’u.
Ya ce, “Akwai abin yi akai Adda, ba haka za'a kyale ta ba. Ni na san irin matsalar ta. Tana da Learning Disability, tana bukatar koyarwa ta musamman (Special Education). Insha Allahu Ma’u za ta yi karatu kamar kowa har matsayin da ya fi degree sai ta taka”.
Ba karamin jin dadin kalaman sa kan Ma’un ta Adda ta yi ba. Rana ta farko da wani ya taba ba ta ‘hope’ kan karatun Ma’u. malamanta cewa suke, jaka ce, wasa ne kawai a kanta.
A daren ya kira Master dinsa (Yaya Maccido). Rana ta farko da ya taba yi masa magana a kan kanwar sa Ma’u. Maccido ya tuna Adda ta taba yi masa magana kwatankwacin wannan a kan Asma’un. Ya bada shawarwarin da yake ganin in an bi za'a taimaka mata ta rubuta WAEC wannan shekarar ta shiga jami’a.
Yaya Maccido ya dora alhakin komai a wuyan sa ya ce, a ciri kudi ko nawa ne a dauki nauyin karatun nata.
Zuwa wannan lokacin Addah ta dangana a kan Maccido, ta yarda ta haifi Maccido ne, amma Lubabatu ta haifamawa. Tsakanin ta da shi sai aiken kudi wanda ita ba ta bukata sam. Abinda ta ke samu a kason ta na mall har ya fi karfin bukatun ta. Nabeelah dai ta ce, ta dage da addu’a akwai abin da ya juyar da kwakwalwar Maccido daga kansu.
Al-Qasim ya sanar da Addah shawarar da suka yi da Maccido na daukarwa Ma’u malami na musamman wanda ya yi specializing a kan learning disability zai fara karantar da ita watanni shidda kafin su zana waec. Ba karamin dadi Adda ta ji ba da wannan gudunmuwa ta Al-Qasim ga Ma’u.
Ta yanar gizo Al-Qasim ya sa cigiyar Malamin Ma’u. Cikin watanni biyu aka samu, amma daga jami’ar Danfodiyo zai je kullum wajen Ma’un. Sai da suka gama komai Maccido ya dunkule albashin sa na duka watanni shiddan da zai yi yana koyar da Ma’u ya ba wa Al-Qasim ya ba shi. A ka sa ranar da zai fara zuwa.
A harabar gidan nan ma’adanar motoci akwai rumfa a nan za mu dinga zama. Al-Qasim ya sayo blackboard, duster da marker wa malamin.
Sai da aka gama komai Addah ta zaunar da ni ta yi min bayani yadda zan fahimta. Ina wuta in jefa Al-Qasim?!
Lallai ya cika Duba-Rudu, wato har kwakwalwar tawa sai da ya sa madubin Duba-Rudunsa ya hango maganin ta. Ni ina ruwana da shi? Me ya yi ruwansa da harkata? Da haka kawai zai zo ya sa a takura min? Zama na yi gaban Adda ina share hawayen abin nan da Al-Qasim yayi min, Addah tana lallashi na tare da fadin Al-Qasim alheri yake nufi na da shi.
Rana ta farko da Malamin ya zo an kai ruwa rana kafin in yarda in fita. Amma a rana ta biyu, ni da kaina na fita babu bacin rai. Wannan ya samo asali ne sabida hanyar da Malamin ke bi wajen koyar da ni (so much persuasive, caring with endurance). Cikin sati daya sai ga ni ina bai wa Addah da Muhsin labarin Malam Sa’ad ba a taba malami mashahuri irin shi a duniya ba.
Muhsin ya yi dariya ya ce, “Ai daga yau mun daina Hausa a gidannan, turancewa kawai za mu rika yi ni da Ma’una”.
Da taimakon Malam Sa’ad, da bada karfin gwiwar dan uwana Muhsin, tare da jajircewar Al-Qasim Ka’oje, na fara fahimtar ilmin boko tare da ganewa ashe shi din abu ne mai sauki, kallon tsoro nake masa. Ko wata daya ba a cika ba turanci mai kyau ya soma zama a bakina.
******
Chapter 12 · 0% Book details