Sashe 8
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
**SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
*
~HISABIN NAFS~
((5)). Har na gama girkin na dauko shi zuwa daki suna nan a yadda na bar su. Kai da ganin Yaya Maccido ka ga wanda damuwar duniya ta yi wa rubdugu. Yana zaune gaban Aunty kan sa a sunkuye. Ban san dai me ya ke gaya mata ba, amma na ga alamun ta sauko daga fushin ta sun koma magana ta fahimta.
Ta ce, “To wannan bakin da ramar da ka ke yi na mene ne? Matar taka ba ta ba ka abinci ne ko mene ne?”
Ganin shigwa ta ya sa bai ba ta amsa ba. Ta maido dubanta gare ni, ta ce.
“Kawo abincin nan Asma’u”.
Na karasa gabanta na ajiye katon tray din ta ce, “Sannu kin ji, Allah ya yi miki albarka”.
Ta dau plate da serving spoon ta yi serving Yaya, ta loda masa abincin sosai ta tura masa, sannan ta zuba wa Muhsin, ni da ita kuma ta hada mana a faranti daya.
Tunda Yaya Maccido ya soma cin abinci bai dago kansa ba. Kafin ka ce me ye wannan ya tashi da farantin. Aunty na kallonsa ta kasan ido cike da tausayi, ta ce.
“Ko a kara maka?”
Ya ce, “I’m okey, zuba dai in kai wa Lubabatu ita ma ba ta ci abincin dare ba”.
Wani kallon banza Aunty ta yi masa, ta ce, “An hana, ba za a bayar ba, na karfi ne ku zo ku kwata”.
Murmushi Maccido ya yi, wanda ke kara masa kyau a duk sanda ya yi shi, ya mike yana fadin.
“Bari in bar ku ku huta, inda abin da ku ke so da babu a gidan ku fada da safe sai a sayo”.
Suka fita shi da Muhsin, kowanne jiki ba kwari.
Aunty ta dauka da safe Lubabatu za ta shigo ta gaishe ta, amma shiru ka ke ji ba ita ba karin kumallon mu. Shi ma maigidan ba mu gan shi ba.
Bayan na yi wa Aasim wanka, na shirya shi ta ce in shiga madafi in sama mana abin da za mu ci. Ran Aunty Nabeelah a matukar bace yake, ban taba ganin ta cikin fushi haka ba. Na shiga kicin ina tunanin abin da zan sama mana mai dan sauki, na jona ruwan tea a kettle na debi dankali na soma ferewa. Ina cikin aikin na ji taku an nufo madafin. Kafin matar gidan ta bayyana cikin kwalliya ta kasaita, kamshin turaren ta duk ya bade kicin din. Ta yi min wani sakaren kallo ta ce.
“Ke kuma wace ce haka za ki shigo min kitchen babu neman izni babu komai? Ko haka ake yi a kauyen ku?”
Na sunkuyar da kai rike da dankali a hannu.
Ta nuna min hanya, “Wuce ki ba ni waje gayyar na ayya kawai”.
Ba musu na ajiye wuka da dankali na fice.
Aunty na gyaran kayan mu lokacin da na shiga, ta daga ido ta dube ni, ta ce,
“Har kin gama?”
Kaina a kasa na ce, “Ta koro ni”.
Kafin in rufe baki sai gata ta shigo daga bakin kofa ta tsaya tana taunar cingam rakakas! Rakakas! Ta ce da Aunty, “Sannun ku da zuwa, jiya kun zo ina jin barci, kuma zuwan naku ba notice”.
Aunty ta daga ido tana kallon ta kawai”.
Ta ce, “Mai aiki za ta zo yanzu sai ta dafa muku abincin, wannan yarinyar ta fiya gidadanci ko kunna gass ba ta iya ba”.
Ba ta jira cewar Aunty Nabeelah ba, wadda ta daga kai a fusace zata mayar mata, amma nan da nan gargadin Adda ya shigo cikin kan ta, Lubabatu ta yi wucewar ta.
Abinka da cikin jego, Aunty yunwa ta ke ji sosai, amma haka ta yi juriya. Yaya Maccido ya shigo ya sha wanka ya dauki walwali cikin shadda getzner. Da na kalle shi sau daya, ban kara marmarin maimaitawa ba, sakamakon cewa kwarjini, haiba da kamalar sa masu cika idanu ne. Ba kowacce mace ce zata iya jurar hada idanu da Maccido ba.
Ko gama gaisawa da Aunty ba su yi ba, a gurguje ya ce, “Zan kai Lubabatu asibiti, wai tun jiya ba ta ji motsin baby ba”.
Aunty ta hadiye malolon bacin ranta ta ce,
“Hakan yana da kyau, sai kun dawo”.
Sai bayan wajen awa daya da fitar su wajejen karfe goma na safe muka ji motsin ana share-share. Zuwa lokacin yunwa ta ci ta cinye mu. Har karfe sha daya na safe ba breakfast din da aka ce ‘yar aiki za ta zo ta ba mu. Yunwa ta ci mu ta cinye don mu a gida karfe takwas mun karya kumallo.
Aunty na kwance tana bai wa Aasim nono, ni kuma na yi wanka ina shiryawa. Ta dau wayarta ta kira Muhsin.
“Muhsin, kana ina ne?”
Ya ce, “Aunty ina hotel din da Yaya ya kai ni, na shirya yanzu zan taho”.
Ta ce, “To don Allah ka tsaya ka samar mana wani abu a hanya, har yanzu ba mu karya ba”.
Bai tsaya bincike ba, ya ce,
“To, in sha Allahu”.
Muhsin ya iso mana da takeaway muka zauna muka ci mu duka uku. Shiru-shiru babu masu gidan har bayan azahar. Aunty ta ce da Muhsin ya tashi mu kama hanya, ita ba za ta kuma kwanan gidan Maccido ba. Muhsin ya yi ta tausar ta, ya ce, yanzu in mun tafi tafiyar dare za mu yi, ta yi hakuri goben da muka yi da Addah za mu koma mu yi asubanci mu kama hanya.
Masu gidan ba su shigo ba sai karfe hudu na rana. Yaya Maccido rike da manyan ledoji, Lubabatu ta biyo bayansa ta kalli Aunty da murmushin keta ta ce,
“Sannun ku fah!”
Aunty ba ta amsa mata ba, ta ce, “Mun biya gidan friend dita ne daga asibitin, ina fatan Rose ta ba ku abinci?”
Daga ni har Aunty babu wanda ya amsa ganin haka ya sa ta tura katon cikin ta ta yi gaba tana yi wa Yaya wani shu’umin kallo.
“Dear ina jiran ka in kun gama, ka tausa min kafafun nan, ka ga duk sun kumbura”.
Ta wuce ba tare da ta kara kallon kowa ba. Shi kuma kunyar Aunty ta hana shi amsawa.
Ya ajiye ledojin hannun sa ya zauna kusa da ‘yar uwar sa, sannan ya janyo su ya soma bubbudewa. Sayayya ce ya yo mana har da ta banza, kowa ledar sa daban. Sannan ya mika wa Aunty ledar takeaway din gasassun kaji da fresh milk, ya ce,
“Ku ci da hakuri, Lubabatu ta ce ba ta so Asma’u na shigar mata kitchen jiya ta lalata mata abubuwa”.
Aunty ba ta san sanda ta kira sunansa da karfi.
“Attahir!”
Da sauri ya dube ta, ta ce, “Kicin din nata ya ci abu kazan-kazan uban sa! Ma’u ba faqiriya ba ce, ba ta kuma fito daga fatararren gida ba. Bar ganin dazu ta kira ta bagidajiya ta kuma kore ta daga kitchen na yi shiru, to ba tsoro ba ne, gudun magana ne, gidan ku kuma yanzu za mu bar muku shi ba sai anjima ba.
Insha Allahu wani cikinmu bai sake takowa gidan ka Maccido, mun bar wa Lubabatu! Sannan ina mai shawartar ka da ka dage a kan ibadah, ka gyara ibadar ka. Akwai gyara a cikin mu’amalarka da Ubangijin ka. Wallahi Maccido ba kalau matar nan ta barka ba.
Gidanka kuma yanzu za mu bar shi ba sai an jima ba, ko kai ka saura da wa Addah, daga yau ta yafe ka, mu uku mun ishe ta za mu yi mata komai. Sai dai ka kasance cikin kokonton hanyar shigar ka aljannah”.
Aunty ta mike ta sunkuci Aasim tana hawaye. Muhsin ya ce, “Aunty don Allah ki yi hakuri da yau da goben duk daya ne, ki dauki abubuwa da sauki, abin duk bai kai ga haka ba”.
Yaya Maccido kansa na kasa bai ce komai ba. Ya rasa abin da yake masa dadi, ya rasa me suke yi shi da Lubabatu wanda yake fusata Aunty haka. Shi bai ga laifin Lubabatu ba tunda gidan ta suka zo suka same ta babu sanarwa. Ya san Lubabatu ba ta karbar wasu baki in ba nata ba, ai ta yi kokari ma da karbar da ta yi musun, a dai halinta da ya sani.
“Ku yi hakuri, abun bai kai haka ba, Lubabatu fa ta yi kokari da har ta bar ku kuka kwana gidan nan, ita bata karbar baki in ba ita ta gayyato su ba.”.
Yaya Maccido ya fada cikin sanyin murya.