Sashe 18
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Haka muka kare wunin ranar ni da Yaya kowa na danne-danne a wayar sa. Idan mun yi kuskuren hada ido ya harare ni. Sosai na takura da zama da shi a dakin. Lokaci-lokaci nurses da doctors na shigowa su yi aikin su a kan Addah.
Da aka kira magriba ya fita, bai dawo ba sai da aka idar da sallar isha. Hannunsa rike da abincin da za mu ci. Ya zauna yana cin nasa, ni kuma na adana nawa don bana jin yunwa.
Sai karfe goma na dare ya mike zai tafi. A lokacin ina waya da Muhsin yana ta ba ni labarin abubuwan da ke faruwa a gida da mall. A fusace Yaya Maccido ya ce,
“Wallahi in ba ki daina hirar wofi da Muhsin ba zan raba ki da wayar nan, don shi ba shi da hankali gobe za'a yi wa uwar sa aiki mai matukar hatsari, amma ya zauna yana surutun banza maimakon ya je masallaci ya yi ta addu’a. Ke kuma shashasha shi ne ki ka biye masa. Kashe wayar nan ki je ki yi alwallah ki kama abin da ya fi alkhairi”.
Da sauri na kashe ba tare da na yi wa Muhsin sallama ba.
Yaya Maccido bai san halin Muhsin ba ne. Shi ba shi da sa abu a rai, ko sanda mahaifin su ya rasu makokin kwanaki biyu ya yi ya ci gaba da harkokin sa da abokan sa. Har polo suka je ranar sadakar ukun Baban su. Naturally haka halinsa yake, ba abin da ke daga masa hankali.
Washegari tun karfe bakwai na safe Yaya Maccido ya iso, ya yi wanka ya yi fresh da shi. Ya zuba wata farar voile mara nauyi, wadda aka yi wa dinki tazarce, links din hannunshi da botiran kayan na silver ne, ya yi matukar kyau kamar saurayi mai tashen ashirin da takwas. Ni ma na shirya cikin bakaken jallabiya na nade kaina da mayafin su.
Karfe takwas daidai na safe aka shiga da Addah dakin tiyata inda za'a yi mata aiki don raba ta da kidney stones. Ni da Yaya dafe da gadon da aka gungurata a kai har zuwa kofar theatre room din. Muka dawo jikin tagar dakin muka jingina, zuciyar kowannen mu ta yi nauyi.
Ban san tunanin da Yaya ya yi ba, sai ji na yi ya kama hannu na ya rike gam! Kafin ya ja ni mu soma tafiya. Sai bin sa nake tamkar rakumi da akala, mamaki na neman zauta ni. Ajrah (taxi) ya tare mana a bakin titi, ya ce a kai mu birnin Meccah.
Muna bayan mota mai Ajrah na ta sharara gudu daga Jeddah zuwa Meccah. Ban tambayi Yaya komai ba don na fahimci yana cikin wani hali na aikin nan da za'a yi wa Addah. Na fahimci babban tashin hankalin sa bai san matsayin sa ba, Addah ba ta yafe masa da bakin ta ba, idan ta mutu ta bar shi, ina zai sa ransa?
Sai da muka isa Haraam yake gaya min dawafi za mu yi, bakwai sau bakwai, mu roka wa Addah samun lafiya.
A sanyaye na ce, “Mu yi umrah kawai gabadaya mu huta”.
Ya ce, “Na fi so in yi umrah tare da Addah, amma mu fara din, in Allah ya tashi kafadun ta sai mu dawo tare mu sake yi”.
Mun yi umrah, mun yi safah da marwah, mun yi nawaafil a maqama Ibraheema Musally, sannan mun yi dawafi bakwai sau bakwai mun yi wa Addah addu’a wadda muka sakankance an amsa kawai, sabida alkawarin Ubangiji ne, duk wanda ya zo da bukatar sa wannan wajen ya sakankance cewa an amsa.
Ko abinci ba mu iya mun ci ba muka sake hawa Ajrah muka dawo Jeddah.
A lokacin muka samu an yi aikin lafiya. A fili na saki hamdala, Yaya ya yi wata irin ajiyar zuciya. An kai Addah daki na musamman inda za ta zauna tsawon kwana bakwai ba tare da kowa ya shiga ba sai likitocin ta. Duka kulawar ta tana wuyan malaman jinyar asibitin. Mu da ganin Addah sai bayan kwana bakwai.
Dakin mu na farko muka koma inda Yaya Maccido ya umarce ni da in tattara komai nawa mu wuce masaukin sa. Mu da dawowa nan sai bayan kwana bakwai din, amma zai dinga zuwa kullum da safe ya ji ci gaba da ake samu a lafiyar Addah.
Ina tattara kayana, amma hankali na ya rabu biyu. Hotel fa za mu koma daga ni sai Yaya! Wannan ko a musulunci ba mu da hurumin sa ko da ciki daya muka fito, dukkan mu baligai ne. Dai-dai misali inada ilmin addini na. To bai ba ni damar da zan yi masa tambaya ba, don haka na rika bin umarnin sa in ga irin hankalin sa.
Ai kuwa na ga abin da ya hargitsa min hankali domin kuwa na fahimci dakin da ya sauka a Al-Jamjoum Fundak nan ya kawo ni. Ya aje jakunkunan mu ya juyo ya dube ni na ci uban birki a bakin kofa. Wani miskilin murmushi Attahir ya yi, ya ce,
“In kin gaji da tsayuwar, sai ki shigo ki rufe kofar”. Ya shige toilet abinsa.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* *07030137870*
```HISABIN NAFS```