Sashe 24
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
*YIWA KAI HISABI*
((13)). Washegari a dakin ban da kuka ba abinda nake yi kwance akan gado. Tun asubah dana yi sallah na koma gado na kudundune na bude sabon shafin kuka, zuciyata ta kasa karbar wanan al'amarin da sauki har zuwa yanzu. A jiya na dauka mafarki nake, idan gari ya waye zan farka in ga ba haka bane. Amma da garin Allah ya waye, na tabbatar babu zancen mafarki cikin aure na da Maccido.
Don haka na bude sabon shafin kuka. Har karfe goma na safe ina abu daya, Yaya yana kwance a doguwar kujera yana fama da ciwon kansa da zazzabi. Ya kama kansa bai shiga sha'ani na ba. Ko asibiti yau ya kasa fita. Banza yayi min kamar bai san ina yi ba. Daga ni har shi ba wanda ya dubi abincin karin kumallon da aka kawo mana. Sai wajejen azahar ya ga bani da niyyar tashi balle in yi wanka, ya samu yayi wanka ya shirya amma idanun sa jazur sabida zazzabi da ciwon kai, ya dube ni a wahale da murya mara amo ya ce.
"In kin ga dama ki tashi ki shirya mu tafi asibiti, ina jiran ki".
Ai jin za'a tafi wajen Addah, nan da nan na mike na fada wanka a gurguje, da na fito ko mai ban shafa ba na zuba Abayat dina baka wuluk na nade kaina da veil din ta, ina so in ce masa na shirya, amma bana so ya ji amon murya ta, ya dauka ko na fara saduda da auren sa ne, yana zaune tallabe da kansa da yake jin kamar zai fice daga gangar jikin sa sabida tsabar ciwo. Ko kadan ban ji tausayin sa ba, a raina nace alhaki na ne ya kama shi yake ta ciwo ba wani abu ba. Shi da kan sa ya fahimci na shirya din ya mike yayi gaba na bi bayan sa.
Sanda muka iso Adda na cin abincin ta na musamman wanda asibitin ke bata, Aunty Nabeelah na gefen ta tana yi mata hira suna dariyar su, Aasim na barci a kan kujera.
Dukkan su kallon mu suka yi admiringly Aunty na fadin,
“Me ku ka zo yi? Ba na ce yau ka bari sai dare ku zo ba?”
Yaya ya karasa gaban Addah ya kama hannunta ya sumbata ya ce,
“Barka da rana Addah, ya karfin jiki?”
“Jiki sai hamdala, kullum lafiya karuwa ta ke, na gode Allah ya yi muku albarka bakidayan ku”.
Ya juya ga Aunty ya ce "nima zan ga Doctor ne, shi yasa muka fito, jiya da fever da headache na kwana sosai, amma yanzu da sauki, bari in je in dawo". Ina ta hararar Yaya, amma ya ki yarda ya kalle ni. Aunty ta ce,
“ko dan paracetamol baka sha ba?"
Ya ce "bana shan magani ban ga likita ba, ina zuwa yanzu". Ya juya ya fita, suka bi shi da kallo fuskokin su dauke da 'yar damuwa.
Addah ta juyo gare ni ta ce,
“Ma’u dawo nan kusa da ni”.
Na koma kusa da Adda na zauna, na ce, “Bari in kira Muhsin ku gaisa Adda, kwana biyu ba mu gaisa da shi ba". Na hau neman waya ta a jaka ta amma sai na tuna na baro ta a daki tana caji.
Sai da Yaya ya dawo rike da ledar magungun sa don kada Adda ta fahimci bama magana na yi ta maza na ce.
“Yaya ba ni aron wayar ka”. Ba tare da na yarda mun hada ido ba.
Ya daga idanunsa da suka kada sabida zafin zazzabi ya dube ni, karo na farko da muka hada ido tun daren jiya, jikina na ji ya yi bala'in sanyi, cikin sanyin murya ya ce.
“Ki shafa min maiko?”
Da sauri na nuna masa tafukan hannu na.
“Allah ka ga hannuna sumul yake”.
Addah ta ce, “In za ka ba ta, ka ba ta, bana son jan rai”.
Ya ciro ta daga aljihun gaban rigar shi ya miko min.
Ina laluben lambar Muhsin kira ya shigo wayar. ‘My Wife’ shi ne sunan da ke yawo a fuskar wayar. Ban san lokacin da na katse kiran ba, aka sake kira na katse shi, haka ta ci gaba da jerawa mijin ta kira ina katsewa babu dalili. Kuma da yake wayar a silent ta ke, Yaya bai san ina yi ba. Ni kaina bansan dalili na na yin hakan ba, ji nayi nan duniya ba wanda nake jin haushi irin Lubabatu.
Yaya ya fita don ya nemo mana abinci, na ja gefe na bar Addah da Aunty suna hirar su, na tsinci kadan daga hirar tasu hirar kayan lefe ne da kayan daki da za'a yi min wanda Aunty za ta je Abu-Dhabi ta auno komai zuwa Nigeria. Na shiga gallery din Yaya babu komai sai hoton iyalin sa. Inda na gane shi ba mai yawan daukar hoto ba ne. Duk wani hoto na Lubabatu sai da na goge shi tas, amma ban goge na yaran ba, haka wanda suka dauka shi da ita duk sai da na bi na yi marking na goge tas. Cike da mamakin karfin hali irin nawa.
Yaya ya shigo da ledojin abincin 'Mud’am Furouj Faqeeh', Aunty ta karba ta shimfida ledar cin abinci a kasa wadda suke hadowa cikin abincin, ta juye komai bisa ledar ta ce mu zo mu ci mu duka.
Ita da ma Addah ba ta cin komai sai wanda aka ba ta a asibiti bisa ka’ida.
Muka sauka mu uku muka zauna bisa kilishi muna cin abinci, Addah sai kallon mu ta ke yi zuciyar ta na yi mata dadi. Haka take so ta gan mu, haka take buri. Wato Allah ya hada mata kan marayun ta. Ta roki Allah cikin zuciyar ta ya kara hada kan mu, ya kara soyayya da kaunar juna a tsakanin mu.
Aunty ta ce da Addah, “Auren Maccido da Ma’u shi ne YI WA KAI HISABI. Maccido ya yi laifi, kuma ya yi wa kansa hisabi da auren Ma'u. Hisabin da ya yi wa kowa dadi. Allah ya sa albarka a auren ku, Ya kade fitina, Ya hada kan matan ka, Ya ba ka ikon yin adalci a tsakanin su”.
Yaya da sauri ya amsa, “Amin-amin Yaya Nabeelah. Kin manta ba ki ce Allah ya kawo wa Addah yara kurkusa ba”.
Da sauri na bar cin abincin na sunne kaina cikin gwiwoyi na, Aunty ta harare shi ta ce,
“Ai muna da yara, Ihsan da Ahsan, duk da rowar su ku ke yi wa Addah”.
Ya ce, “Ai shi ya sa na ce ki yi addu’a Allah ya kawo wadanda za su zauna kusa da ita, har sai tana korar su tana cewa, sun ishe ta”.
Addah ta ce, “Ni ba zan taba korar su ba”.
Haka suka yi ta hirarsu suna nishadi, Yaya ya sha magungunan sa bayan mun gama cin abinci, na yi addu’a cikin raina, Allah ya sa wannan farin cikin da ke kan fuskokin su ya dore har karshen rayuwar su, don na lura wannan shine farin cikin Addah, wato hadin kan 'ya'yan ta.
Tunda Yaya ya dawo sallar isha Addah ta ce mu tashi mu tafi, duk wannan sakewar da ke tsakani na da Addah yanzu ta kau, kunyar ta nake ji sosai. Muka yi musu sallama, sannan muka fito muka tari Ajrah muka koma hotel.
Ina tsaye jikin mudubin dogon yaro ina kallon ramar dana yi cikin kwana daya kacal, na ji shi yana waya yana fadin,
“Na kashe miki waya? Da yaushe aka yi hakan? To shi ke nan tunda haka kika ce na kashe din, don Allah kada ki fasa tafiyar, dawowa ta kuma babu rana sai uwata ta samu lafiya”.
Ya jefa wayar gefe yana tsaki. Sai kuma ya dauko ta ya shiga binciken ta, ya shiga call log din sa, gallery din sa da akwatin sakonninsa nan ya fahimci komai.
Kaina a kasa irin na marasa gaskiya na bi ta gaban sa zan wuce, sai ji na yi Yaya ya damko ni, na ce, “Wayyo Allah na, zaka karya ni" Ya ce, “Sannun ki, wato shi ne ki ka hada ni fada da matata ko? Ki ka goge min texts din ta da hotunan ta masu sanyaya min zuciya daga bakaken kalaman ki, bayan ke kin ce ba kya so na? To a wane dalili? Ina son sani".
Na yi fuska sosai, sai ka rantse da Allah ba ni na yi ba, nace "a wane dalili kuwa? Kawai gani na yi sun cika wayar ba space. Amma ka yi hakuri, ni daga kai har ita ba kwa gaba na". Wani irin miskilin murumushi Yaya Maccido yayi. Ya girgiza kai yana ta mamaki, wai ‘yar wannan Asma’un ta san kishi, tun yanzu ma ke nan, ranar da suka hadu ashe ya shirya abin da a baya bai taba tunani ba. Bai ce min komai ba ya sake ni yana ta murmushi wanda na kasa gane dalilin yin sa.
Irin kwanciyar jiya, ita aka yi yau ma, yana kujera ina gado, ya tada kai da hannayen sa. Ya lumshe ido yana tunanin ta inda zai bullowa wannan hutsuwar Asma'un.
*** *** ***
Yau ma sai azahar muka shiga asibiti, jikin Addah sai hamdala yau ta sauko daga gadon ta je toilet da kanta, duk da har yanzu a zaune ta ke sallah.
Yaya Maccido ya ce da Addah da Aunty tunda jikin Addah ya yi kyau gobe ni da shi za mu tafi ziyarah Madeenah. Za mu yi kwanaki bakwai. Aunty na dariya ta ce, “Ka fadi gaskiya dai, ziyara ko honeymooning?”
Ba kunya Yaya Maccido ya ce,
“Duka biyun, ai ana jifan tsutsu biyu da dutse daya”.
Na dago kai gabana na dukan uku-uku jin abinda Yaya ya ce, bansan sanda na ce "gaskiya Adda ni ba inda zani". Addah ta ce "ba'a kin zuwa Ziyarar Ma'aiki, burin kowanne musulmi kenan, kiyi hakuri ku je".
Haka tayi ta lallashi na har na amince zan je amma ta gargadi Yaya kan kada ya takura min kan duk abinda na ce bana so.