← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 33

Sashe 2

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na taso cike da dokin, ranar zuwan Adda Kilishi. Ta kasance uwa mai yawan kyautata mini ta kowanne fanni, ta kasance ‘yar uwa ta gari ga dan uwan ta, wato mahaifi na. Ta zame masa uwa da uban da ba su tashi da su ba. Zumuncin ta abin a bada labari ne, domin ba ta bambanta ni da ‘ya’yan da ta haifa, tun ina mitsitsiya ta na fahimci wannan bangaren na Yayar mahaifi na Kilishi.
An ce akwai wadanda zumuncin su shi zai kai su aljannah, bana tantama ciki har da Adda da mahaifina malam Adam, don dai ni tun da nake a duniya ban taba ganin ‘yan uwa masu son juna fisabilillahi kamar su ba. Duk da mahaifi na ba mai karfi ba ne wannan ba ya hana duk sallar idi ya dinka wa Maccido kayan sallah irin wadanda ya dinka wa kansa. Haka nan yana yi masa kiwon tumaki garke guda a nan kangon bayan gidan mu, wadanda ya fara ne da ba shi tunkiya mai ciki, ta yi ta hayayyafa, Maccidon ya ce Baba ya kiwata masa ita, don gidan su ba wajen kiwo.
Baba ya soma yi wa Yaya Maccido wannan kiwon ne tun yana da shekaru goma a duniya, Allah kuma ya albarkace su, domin a yanzu sun zama garken awaki na raguna da tunkiyoyi da ‘ya’yan su. Har zuwa yau Baba bai taba gajiya da kiwon da yake yi wa Yaya Maccido ba. Baba ne kurum yake kiransa da sunansa na asali, wato Attahir, amma a bakin ‘yan gidan su da iyayen sa da abokan sa "Maccido" ne a bakin kowa.
Ina aji daya a babbar sakandire wadda sau biyu ana min maimacin aji (repeating) kafin in samu in shiga siniya sakandire, a hakan dai nake kukkulla makarantar maganin zama a gida, kada a ce bana karatu. Ni tunda nake ban taba daukar littafin makarantar boko da nufin in duba abin da aka koya min in na dawo gida ba, sannan bana yin aikin gida (home work ko assignment) yadda aka ba ni shi haka ake karbar littafin ba tare da na rubuta ko ‘alif’ ba.
Duka na sha shi wajen malamai har ya yi yawan da bana jin shi a jikina, sai a yi min bulala bakwai a tafin hannuna ban yi ko hawaye ba. Sau ba adadi hukumar makarantar mu ta sha kiran mahaifi na a kan matsala ta, abin da yake cewa kullum shi ne,
“Watakila Ma’u ba ta da abinci a boko, tunda ta shiga firamare ma har ta gama haka ta ke, ku yi min alfarma ta ci gaba da zuwa makaranta tana shiga aji, in ba ta koyi karatu ba, ta koyi rayuwa da cudanya da jama’a”.

Ina mamakin saukin hali irin na mahaifi na. Idan na duba sai in ga ita ma Adda Kilishi ai haka ta ke. Saukin kansu yayi yawa akan 'ya'yan su. A fili suke nuna mana soyayyar su garemu.
A daidai wannan lokacin ne rannan na taso daga islamiyya, tun daga nesa na ga santaleliyar motar da ta sanar da ni cewa, Adda ta zo gari, don haka na kara da gudu-gudu, sauri-sauri na isa gida. Amma abin mamaki direban ta Malam Hussaini ne kawai a zauren gidan mu babu walwala ko ta kobo a tare da shi. A gurguje na gaishe shi na afka tsakar gida ina kiran,
“Oyoyo Adda”.
Sai dai a raina na yi mamakin dalilin da Malam Husaini yau bai yi min kirarin da ya saba yi min ba cikin raha a duk lokacin da muka hadu, wato; “ASMA’U FARA ‘YAR SHEHU”. Ni kuma na kan amsa masa da cewa, “Wannan Asma’un baka ce. Babu digon fari ko dis a jikin ta”. A duk lokacin da na fadi hakan, Malam Hussaini ya yi ta dariya ke nan.
Turus! Na ja na tsaya ganin Nene na zuge katuwar jakar matafiya, Baba ma yana tsaye da tasa dirkekiyar jakar yana kara gyara kayan ciki. Fuskokin su sun yi min kama da na Malam Hussainin Adda da ke soro. Wato fuskokin su dauke suke da matukar alhini. Na karasa jiki a sanyaye na ce,
“Nene, ina za ku? Ina kuma Adda?”
Nene ta dago ta dube ni, fuskarta ba yabo ba fallasa, ta ce, “Ba ta zo ba, mu ne za mu je mata. Je ki ajiye jakar makarantar ki canza kaya ki zo mu tafi, yanzu za mu dauki hanyar Sokoto”.

Tunda muka dauki hanyar Sokoto daga Bebeji babu mai magana a cikin motar, Nene da Baba jan carbi kawai suke yi, yayin da Malam Hussaini ke tuki cikin kwarewa da kula da ladubban tuki. Ni dai sai sake-sake nake, ina so in tambayi abin da ya faru, babu fuska, don ko a junansu ba sa hira. Wani mummunan tunani ya fado min a rai, ko dai wani abu ne ya samu Adda? Abin da zai taso Nene da Baba a wannan yammacin zuwa Sokoto, hakika ba karamin abu ba ne.

*KYAUTA NE GA TAKORI'S LOUNGE*
*SUMAYYAH ABDULKADIR* *(TAKORI)*

TUKUICI NE ga makaranta littatafai na.
```Yiwa Kai Hisabi```
((2)). A wancan lokacin Najeriya lafiya lau, babu matsalar ‘yan fashi, babu ta ‘yan garkuwa da mutane, babu ire-iren wadannan abubuwan. Ina miki bayanin abin da ya faru ne ga ni Asma’u shekaru ashirin da biyu a baya, wani lokaci ne da kasarmu ke zaune lafiya cikin lumana da kwanciyar hankali.
Babu irin tunanin da ban yi ba, amma na kasa rike kwakkwara guda daya in ce shi ya faru, wanda ya janyo mana tafiyar dare haka zuwa Sokkoto birnin Shehu. Tsananin addu’ar da Baba da Nene ke yi, shi ya kawo mu Sokkoto lafiya.
Addar da nake tunanin wani mummunan abu ya same ta da ita na fara yin tozali a makeken falon ta, sai dai da ganin ta ta ci kuka har ta gode Allah, ta rame ta yi fiyat cikin kwana daya. Sai da muka kwana muka wuni na fahimci abin da ya faru, Baban su Muhsin ne ya yi hatsarin jirgin sama daga Port-heartcourt zuwa Sokoto, ko gawarsa ba su samu ba, an tabbatar yana cikin fasinjojin, jirgin nasu ya fado ne ya kone kurmus.
Ya tafi ya barta da marayu guda uku, da tarin dukiyar da ba su san ya ya za su yi da ita ba. Maccido karatu yake a kasar 'Cuba' (country in the Carribean) yayin da Nabeelah ta ke Beirut din Lebanon tana nata karatun, Muhsin ne kawai a gaban ta.
Da wannan tashin hankalin su Adda suka wayi gari. Lokacin da ta ga Baba na sai ta daura kai a kafafun sa ta yi ta rasgar kuka. Kuka ta ke mai tsuma zuciya, mai dauke da amon girman maraicin da ya same ta. Alhaji Atiku Dogondaji, miji ne wanda har a aljannah ta ke fatan Allah ya tashe su tare. Ya rike Adda da daraja da mutunci, bai taba la’akari da zurfin ilminsa ya wulakantata ba, ko ya ce zai auro wadda ta yi boko ta fi ta wayewa ba. Ya yi musu komai a rayuwa ita da ‘ya’yan ta, don haka rashin sa tamkar faduwar wani babban gini ne wanda yake katanga abar jingina a gare ta da ‘ya’yan ta.

An yanke shawarar ba za a gaya wa Maccido rasuwar mahaifinsa ba, saboda a daidai lokacin jarrabawa yake yi. Amma ranar kwana biyar da afkuwar al’amarin Nabeelah ta iso. Suma ta rika yi ana yayyafa mata ruwa tana farfadowa. Ko ba ka yi wa wannan family din farin sani ba, dole in ka ga halin da suka kasance a wannan loakcin ka tausaya musu.
Mai rangwamen damuwa a cikin gidan, Muhsin ne. Ya yi damuwar, amma ta kwana biyu ya ware ya shiga harkokin sa. Duk inda ya yi muna tare, kamar tip da taya. Tun sati daya da rasuwar su Nene suka so komawar mu gida Bebeji, amma Adda ta hana, sai da muka kara sati. Da za mu koma kuma ta ce, ni a nan za'a bar ni. Gidan ya yi mata fadi da yawa, don washegarin ranar Nabeelah ma za ta koma makaranta.
Ai kuwa ba kunya na sa kuka kan ba zan zauna ba. Aka yi a ka yi na ce kafata kafar Nene. Da haushi ya ishi Nene, sai ta tsinka min mari. Na kuwa bare baki ina kara rusa kuka. Adda ta jawo ni jikin ta tana lallashi na a lokaci guda kuma tana yi wa Nene fadan saurin hannun ta. Mene ne abin duka? Ta ce, “Ma’u ba za ki zauna da ni ba?”
Cikin kuka na ce,
“Adda, to yaushe za ki maida ni wajen Nene?”
Tana goge min hawaye ta ce, “Insha Allahu idan Nabeelah da Maccido sun gama karatu sun dawo gida zan maida ke wajen Nenen ki Asma’u. Kadaicin ya min yawa, ina bukatar mai debe min kewa, ba kya tausayi na ne Ma'u?”
Duk sai jiki na ya yi sanyi, duk da nake yarinya karama na san Adda abin tausayi ce a wannan lokacin, amma na fi so in yi zamana gaban iyaye na, duk da na san zan samu gata da jin dadi ne fiye da wanda nake samu a gidan mu. Ni wannan ba ya gabana, na fi so kullum na bude ido in gan ni gaban Nene na da Baba.
A daren ranar a dakin da Nene ta sauka na kwana, mun raba dare tana min fada, ta bari ta koma nasiha. Ta ce, Adda ba ta cancanci abin da na yi mata dazu ba, kauna ce da soyayya ta sa ta ce in zauna a wajen ta, ba don ba ta da ‘ya’ya ba. Ta yi min nuni da halin da Adda ke ciki, tana son wani makusancin ta ne a kusa da ita. Ta ce in zauna gaba gare ta in hidimta mata, in mata biyayya iyakar iyawa ta, don ba ni da wanda ya fi-ta a duniya bayan mahaifi na.
Chapter 2 · 0% Book details