Sashe 32
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani irin ihu Lubabatu ta saki tare da hada wayar Attahir da bango, ta kuwa tarwatse nan da nan kowanne part ya kama gabansa.
Ba karamar razana Ihsan da Ahsan suka yi ba. Lubabatu ta yi kukan kura ta yi kan Attahir,
“Gara in kashe ka kafin ka kashe ni…”.
Wuyansa ta kai wa damka, duk kokarinsa na bambare hannayenta daga jikinsa ya kasa. Ya ce, “Lubabatu kashe ni, ya fi min alkhairi da inda ki ke leading rayuwata… kin raba ni da uwata kin raba ni da ‘yan uwana, kina kokarin ja na jahannama. Kada ki dauka duk shige-shigen da ki ke yi domin ki halakar da ni ban sani ba. Na yi shiru ne ba don tsoro ba sai don ni ma ina da nawa target din. Wanda shi ne auren ‘yar uwata, yawon bin bokaye don Allah kar ki fasa ki ci gaba, wa man yatawakkal alallahi fa huwa hasbuhu.
Na auri ‘yar uwa ta Asma’u, ruwan ki ne ki kama girman ki mu zauna lafiya ruwanki ne ki hana kanki kwanciyar hankali, ki ci gaba da shige-shigen da zai fishshe ki. Rana dubu ta barawo… rana daya ta mai kaya.
Ban auri Asma’u da nufin tozarta ki ba, sai don ra’ayin kaina da samawa mahaifiyata farin cikin da ki ka kasa bata, girman da ki ka kasa bata, da ‘ya’yan da ki ke rowanta mata.
For your good information ku biyu ne matana yanzu. Ba ni da niyyar hada ku gida daya a halin yanzu, amma ban san me gobe za ta haifar ba…”.
“Ubanka za ta haifar Attahir, na ce ubanka za ta haifar. Ka yi kadan ka yi min wannan tozarcin. Ka je gida an tsaface ka an hada ka da wannan dangin dangaron don a ga bayana, to uban kuturu ya yi kadan wallahi. Na fi karfin in hada miji da kowa balle wanan ‘yar matsiyatan.
Ban da soyayya kai ka san ba ka isa ka aure ni ba. To haka nake so ka sa a ranka ni kadai za ka rayu da ni da an ki da an so. Ka gaya wa Nabeelah ni murucin kan dutse ce, ban fito ba sai da na shirya, don na san duk wannan munafurcin nata ne.
Idan ka ga ka rayu da wata mace ba ni ba, to ka tabbata a lahira ne, in ka yi dacen shiga aljanna kenan...”.
Hankade ta ya yi ya mike don ya lura ta soma fita daga saiti, kwayar idonta bakidaya sun juye. Taku ya soma yi zai wuce zuwa dakinsa don ba ya so ya sake tanka mata. Ya gama fadin mata duk abin da yake son fada mata shekara da shekaru ya kasa. Tsoro da dabaibayin da ke kansa bai ba shi dama ba.
Yanzun ma har mamakin kansa yake, yadda rana daya ya juye ya koma Maccidonsa na ainahi. Bai san cewa sujjadar UWA ba ce cikin talatainin dare da zafin hawayenta da jajircewar ta wajen kai wa Allah kukanta ba tare da gazawa ko gaggawa ga son saukar ijaba ba.
Lubabatu ta dauki kofin da ya gama shan shayi da shi ta wulwula shi zuwa ka Maccido. Bai same shi a ko’ina ba sai a keyarsa. Ya tarwatse a wajen wanda hakan ya yi sanadiyyar nutsewar wani bangare na kwalbar cikin tsokar naman kansa, jini kuma ya balle kamar an kwance famfo.
Ihsan ta saki kuka ganin jini na zuba daga kan Babanta, ta yi kansa tana kiran sunansa. Hannunta ya kama sannan ya kai hannu ya dafe wajen ya juyo ya dubi Lubabatu.
“You are just wasting your time, bakin alkalami ya riga ya bushe, don kuwa Asma’u da kusa haifa wa Ahsan kannai”.
Ya suri mukullin motarsa kan kujera ya sunkuya ya dauki Ahsan da ke ta kuka ya kama hannun Ihsan suka fice. Bangaren mai rainonsu ya kai su, ya ce ta kula da su zuwa safe. Sai salati ta ke ganin jini na malala daga kansa. Take ta hada biyu da uku ya ba ta ma’ana, ko dai Madam zai yi wa kishiya ne? A kan yadda ta san uwar dakin nata a kan kishi har da su ‘yan aiki za ta aikata fin haka.
Ya dauki mota jiri na dibansa zuwa private clinic mafi kusa, aka yi masa treating ciwon aka cire wadda ta nitse, sannan aka yi masa dinki.
Kin komawa gidan ya yi sai sha biyu na dare, a tunaninsa ta yi barci, amma yana shiga falo ya jiyo tashin muryarta tana waya cikin kuka…
“Yadda ki ka rusa rayuwa ta Allah ya rusa ta ki Nabeelah. Allah ya sa balaraben ya sako ki. Ki gaya wa uwarku na ci dubu sai ceto, na dade da sanin mugun nufinta a kaina da wannan mummunar yarinyar da ta ajiye a gabanta… to na ga aure na shaida ina jiran ganin ranar shigowar ta gidana, wallahi sai dai ku dauki gawar ta inyaso ni ma a kashe ni…”.
Banka kofar ya yi ya shiga dakin, wayarsa ce a hannunta. Ya fizge wayar ya duba ya ga kiran na tafiya, kuma sunan Aunty Nabeelah ne. Ya daga hannu ya wanka mata mari, ya sake wanka mata.
“Nabeelah sa’ar ki ce? Yayata uwa daya uba daya?”
Ya kankance ido yana mata wani kallo da ba ta taba gani cikin kwayar idon sa ba.
“Uwata ki ke bai wa wannan sakon Lubabatu? Uwar da ta kawo miki ni duniya na shagaltu wajen bauta miki na manta da ita, amma ba ta taba korafi a kanki ba, sai ni don na yi auren da duk cikin su babu wanda ya sanya ni? To ina so ki sani na auri Asma’u ne don ina sonta ba don wani cikin su ya cusa min ita ba. Ke kuma na aure ki ne don kare kaina daga zina, amma tun farko Asma’u nake so ba ta isa aure a sanda ni na isa ba. Hope this information is enough and clear ki yi deciding za ki iya ci gaba da zama da ni ko a’ah?"
Lubabatu ta yi masa wani sakaran kallo, “Ina zan je? Ai aurenmu takalmin kaza ne, da ma haka ake so in tafi, don na tsokale wa kowa ido, to ba inda zan je, zama daram. Zaman yakin kwatar kai, inyaso mai karfi ya kwace Maccidon. Kada ka dauka soyayya ce za ta zaunar da ni. Zan zauna ne don in hana ku kwanciyar hankali in kuntata rayuwar ku yadda ku ka kuntata tawa…”.
Murmushi ya yi irin na mazan da suka san kansu.
“Karyar banza karyar wofi, kin ce soyayyar ta kare ko?” Ya fada yana takowa zuwa inda ta ke. Ta gane abin da yake shirin yi wanda kuma a take zai wargaza dukkan karfin zuciyar ta. Sai ta yi wuf! Ta kasan hannunsa ta fice dakin da gudu tana kuka. Attahir ya yi murmushi wa kansa ya daga murya yadda za ta jiyo shi.
“Ai na so ki tsaya a tantance aya da tsakuwa, ta nan za mu gane ta inda karewar soyayyar ya fara. Kin ci darajar haihuwar ‘ya’ya biyu, wallahi yau da sai na kumbura miki mukamikin da ke wa Yayata rashin kunya”.
Tun daga wannan ranar gidan ya rikice ya koma wani dan karamin sansanin yaki. Lubabatu ta hana shi kwanciyar hankali ko na second daya. Duk kayan amfaninsa ta lalata, ta kwankwatsa kayan kallo da glassan windows, ta zama kamar wata sabuwar mahaukaciya. ‘Ya’yanta ba ruwan ta da su, komai nasu ya koma hannun mai rainonsu, abinci sai dai ya saya a waje ya kuma ci a wajen in yana so ya tsirga masa.
Abubuwa suka taru suka addabi Attahir, ga hidimar mall ga ta Maccido Plaza, ga ta ‘ya’yansa in ya dawo gida, sannan ga tarin ayyuka a ofis. A daidai wannan lokacin ne kuma Julius Berger Nigeria suka kara masa matsayi zuwa construction manager, ya ga cewa in ya ci gaba da rayuwa da Lubabatu a haka watarana stress za ya kayar da shi, don haka ya gaya wa yayanta Usman duk halin da yake ciki da ita, shi kuma bai yi wata-wata ba ya gaya wa Baban su.
Lubabatu ta gama tsiyatakunta na yau inda ta debi ruwa bokiti-bokiti ta kwara a gadon Attahir ta fito za ta koma dakinta, ta ji sallamar Babanta da yayanta Usman.
Tana ganin su gabanta ya fadi, don ta san Babanta ba ya zuwa gidajen su. Jikin ta ya ba ta Attahir ya gaji ya kai karar ta ne. Ilai kuwa, Usman ya fiddo sharbebiyar bulala daga leda ya mika wa Baban, za ta gudu Usman ya damko ta. Baban ya yi mata dukan kawo wuka, ya lallasata ko’ina a jikinta ya yi birdin-birdin, sannan ya koro mata warning din cewa, idan ta kai Attahir bango ya sake ta, kada ta sake ta doso gidansa.
Daga wannan lokacin ne Maccido ya samu saukin Lubabatu, amma sai ta daina shiga duk wata sabgarsa, ta maida shi shi da babu duk daya cikin gidan, sannan ta guntule alakarta da ‘ya’yanta, ta bar wa mai raino.
Don haka ne gidan duk ya zame masa kurkuku, Allah-Allah yake ya samu sarari ya arce Sokoto. Ni ma din ba ya samun wata kulawa daga gare ni a waya, ina can ina fama da kaina, imagine laulayin ciki mai wahala, gaskiyar Muhsin Yayan sa is a sharp shooter. Karshe sai dakin Adda na koma da zama gabadaya, don Aunty Nabeelah ta dade da komawa Lebanon.
Kafin ta tafi ta ba mu labarin wayar cin mutunci da Lubabatu ta yi mata, duk da Maccido ya ba ta hakuri, Adda kuma ta ce kada ta kula ta zafin kishi ke damunta, ta yi haushin kaza huce kan dami.
Ranar wata juma’a ya samu sararin ayyukansa. Ya sa Nanny Maria ta hada masa duka kayan yaran a babbar trolley dinsu. Lubabatu na daki tana ta kitsa sharri a waya da kawaye ya kwashe yaran ya taho da su Sokoto ba da saninta ba.
Ba ta gane ba sa gidan ba sai yamma lis, jin shirun su ya yi yawa, da ko ba za ta kula su ba sai sun shigo inda ta ke. Ta kwala wa Maria kira ta zo,
“Ina yara ban ji motsin su ba?”
Maria ta ce, “Oga ya kwashe su ya tafi da su tun safe ba su dawo ba, kayan su duka ya kwashe”.
Lubabatu ta zame wa Maria kamar zautacciya, Maria ta sha mari hagu da dama kan don me tun lokacin ba ta zo ta gaya mata ba ta bari aka kwashe mata ‘ya’ya aka kai wa makiyanta? Ta je daga yau ta sallame ta.