Sashe 5
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ya dade yana tauna magananun Addar sa, yana aunawa a bisa ma'auni na hankali da tunanin sa, don ganin ko Lubabatun sa ta mallaki wadannan qualities da Adda ta jero? Ba zai iya cewa ba! Abin da ya sani kawai shi ne, Lubabatu ta yi daidai da ra’ayin sa, ta mallaki duk abubuwan da yake so a diya mace. Ga kyau ga aji, ga gayu kamar rainon sarauniyar Ingila.
Sannan ga ta da ilimi don masters ke gare ta. Ba ya tunanin tana da wani aibu don kuwa abotar su da Usman ta dade. Ya san gidan su babban gida ne, sauran halin mutum ai ba za ka sani ba sai in ka zauna da shi.
Gadan-gadan Yaya Maccido ya sa kai ga neman auren sa. Har ya je Dogondaji ya gaya wa su Baffa Bilya. Kafin ka ce me ye wannan magana ta kankama. An kai kudi an yi tambaya, har an ba shi mata. Tsakani na da Yaya Maccido da ma tun fil’azal babu sakewa, babu sabo, babu wata doguwar mu’amala mai nisa. Iyakaci na da shi in ya shigo cikin gida ne mu gaishe shi ni da Muhsin ya sa kai ya wuce dakin Adda, in kuma tare da Addar ya same mu, sai in ba su wuri bayan mun gaisa. Wani lokacin Adda kan sa ni in dauko masa abinci daga dining don ba ya son zama a kan tebir ya ci abinci, ya fi so ya zauna gaban Adda yana ci suna hira. Wannan ita ce alakar da ke tsakani na da Yayana Maccido.
Shekaru biyu baya, Adda ta sa ya kai ni wata sakandire ta kudi na dora karatu na. A halin yanzu ina aji biyar na babbar sakandire.
Kada ku dauka ko yanzu akwai soyayya tsakani na da boko, har yanzu ina nan jiya i yau, don ma dai Muhsin ba ya bari na haka. Kullum da yamma sai ya sa na dauko littafi na ya tisa min abin da aka koya mini. Amma kan ba ya daukar komai. Kullum ni ce ta karshen aji ko ta biyun karshe. An so a yi min repeating a shekarar da zan shiga SS 2, Adda ta je har makarantar da kanta ta bude bakin jaka, ta kuma ba su hakuri. Ita dai burin ta in samu ko da kwalin kammala sakandire ne, ko da ba zan shiga jami’a ba.
Bikin yaya Maccido ya zo, aka yi biki na kece raini a Sokoto da Abuja. Bikin diyar Sanator Abdu Gwadabe.... Lubabatu Abdu Gwadabe da Arch. Attahir Atiku Dogondaji. Yaya Maccido ya sayi apartment a Gwarimpa mai daki uku da falo. Ranar na ji yana gaya wa Adda iyayen amarya sun ce gidan ya musu kadan, ya je ya kama haya a Maitama mai faluka uku suke so.
Adda ta kalle shi a shekeke! Ta ce, “Ko bayan raina ban yarda ka zauna gidan haya ba, alhalin kana da naka. Ni ban yarda da rainin arziki ba. In za su zauna a wanda Allah ya ba ka shi ke nan, in bai musu ba, to fa babu dole ta yi ta zama a gaban iyayen ta”.
An kai ruwa rana kafin su yarda su je su yi jeren. Muna kitchen ni da Addah muna hada abincin dare, na ji Adda tana kwafa. Kafin cikin takaici ta ce,
“Ma’u, tun ba a je ko’ina ba na fara sunsuno gagarumar matsala cikin auren Maccido, sai dai Allah ya kade fitina”.
Nan ta ke ba ni labarin maganar gida.
Na ce, “Ni kuwa tunda na ga matar rai na yake son ta Adda, kyakkyawa ce sosai, ga ta da gashi har kafadun ta”.
Adda ta harare ni, ta ce,
“Ai nan ku ka fi kauri ‘ya’yan zamani, kyale-kyalen duniya, wanda dukkan shi mai gushewa ne. Amma mutanen da suka fito fili suka raina arzikin ka, ai babu alamun alheri a tattare da su”.
Ranar lahadi aka kawo amarya Sokoto. An yi wa baki abinci na alfarma wanda zai ishe su komin yawan su. Bangaren Maccido na gidan aka sauke su wanda Yaya Maccido ya gyara sosai. Sai dare suka shigo da amaryar wajen Adda tana tare da abokan arzikin ta da mutanen Dogondaji, aka yi abin da ake kira ‘amana', aka yi addu’o’i na nema wa ma’auratan zaman lafiya da zuri’a dayyiba sannan suka koma sashen Yaya Maccido.
Washegari ‘yan rakiya suka juya Birnin Kebbi, sai amarya da ‘yar aikin ta wata budurwa banufiya. Kwana uku na yi ina hidimar su don duk abin da za su ci Adda ta dora shi a wuya na. Ta kan ce "in dai a kan girki ne ba ni da haufi a kanki Ma’u. Ko Maccido ya sara miki duk miskilanin sa, ya ce, kin iya girki sosai”.
Da daddare bayan na shigar musu da dinner na yi sallama dakin Aunty Lubabatu. Tana gaban madubi tana kwalliya, da alama daga wanka ta fito. Gashin nan da nake so ya sha gyara sai sheki yake a dokin wuyan ta. Ta amsa min sallamar ba tare da ta juyo ba daga shafa hodar da ta ke yi. Na ce,
“Aunty zan je in kwanta ne, ban sani ba ko da abin da ku ke so bayan abinci?”
Ta ce, “Ina son gasassun ‘yan shilla wallahi, bana son cin abinci da daddare”.
Na yi dan jim! Kafin na ce, “Ga shi ba mu da ‘yan shilla sai manyan kaji, ko in nemi karama a ciki in gasa miki?”
Ta yamutse fuska, ta ce, “Kai anya? Barshi kawai in Tahir ya dawo ya nemo min. Na gode”.
Na koma sassan mu can na samu Muhsin yana kallon kwallo a falo. Ya ce, “Ma’u me ku ka dafa ne?”
Na ce, “Sai abin da ka ke so. Abinci har kala uku na yi wa amare”.
Ya kyabe baki, ya ce, “Ni fa sam wannan matar Yaya Maccidon ba ta yi min ba. Mace ba fara’a ba haba-haba da jama'a. Ko da na kissa ne. jiya fa da na shiga ina jin shi yana yi mata bayanin ko wane ne ni, amma sai cewa ta yi, "sannu fah!" (Ya fada yana kwaikwayon muryar ta), daga haka ta ta kara kallona ba”.
Na yi dariya na ce, “Yanzu kuma duk abin da na sha wahala na girka mata ta ce ba ta so, ya yi nauyi, gasassun ‘yan shilla ta ke so, kuma ba mu da su”.
Ya ce, “Mijin ta ya zo ya nemo mata. Ni gara su tattara su tafi su bar mana gida. Haka kawai a dinga sa ki wahala, ke girkau ce?”
Adda ta leko daga kofar dakinta da hijab a kanta, da alama sallah ta idar, ta yi masa dakuwa, ta ce, “Ungo nan. Kun zauna kuna gulma, akwai sa’anku cikin su? Na ce akwai sa’an ku?”
Ba shiri daga ni har Muhsin muka bar falon, kowa ya yi dakin sa.
Na canza kayan jiki na na sa na barci na canza bedsheet dina, ina kokarin bude labulaye don rage karfin A.C da ta cika dakin, na ga Yaya Maccido na shigowa cikin motar sa kirar Cadillac. Sai na samu kaina da son tsayawa in ga fitowar sa don ni dai haka kawai yake burge ni, ga kyau ga wata irin nutsuwa, ga aji, sannan ga wani irin kwarjini na musamman da Ubangiji ya mallaka masa.
Ya fito sanye cikin shadda filtex fara kal! Sai walainiya ta ke yi cikin hasken farin kwan fitilar da ya haske harabar adana motocin, hannayen sa rike da fararen ledoji. Kai tsaye cikin kasaitaccen takun sa ya wuce ta gefen tagar daki na zuwa cikin gida.
Wajen Adda ya fara zuwa kamar yadda ya saba bai jima ba na ga wucewar sa zuwa nasu sassan, wanda dole ta gaban tagar daki na za'a wuce. Iska ta kado min sassanyan turarensa Escada Magnetism. Na samu kaina da fadawa bisa kwayar kujerar sofa da ke daki na yayin da wani tunani ya bakunce ni.
“Matar sa ta yi sa’a”.
“Matar sa is a lucky person”.
“Matarsa ta ji dadi a rayuwar ta”.
A lokaci guda na tambayi kaina dalilin wannan bahagon tunanin? Inda ba tare da bata lokaci ba zuciya ta ta halarto min da amsa;
“Yaya Maccido yana BURGE NI!”.