Sashe 6
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kwan fitilar da na kashe aka kunna, haske ya gauraye dakin. Adda na gani rike da daya daga cikin ledojin da Yaya Maccido ya shigo da su. Ta ce, “Ma’u, kin yi barci ne?”
Na yunkura na tashi zaune, na ce, “Ina shiri dai Addah”.
Ta miko min ledar hannun ta, “Ungo nan ki ci, gasassun ‘yan shilla ne Yayan ku ya kawo min. Ni ba iya cin su na yi ba, ko za ki iya ci?”
Na karba tare da yin godiya, ta juya ta fita tana jaddada min yin addu’o’i kafin na kwanta.
Na bude ledar kamshin naman ya buge ni wanda ya ji kayan kamshi. Wato shi auren haka yake da maida mace ‘yar gata, ko me ta ke so mijin ta zai mata, zai nemo mata komai runtsi.
To ni yaushe nawa auren zai zo?
Wane ne nawa mijin?
Yaushe zan isa auren?
Tambayoyin da nake yi wa kaina ke nan wadanda ba ni da amsar su. Na san dai rayuwar Yayan mu Maccido da matar sa Lubabatu ta darsa min kwadayin yin aure a zuciyata.
*****
Satinsu biyu suka tattara suka wuce Abuja. A satin nan guda biyu mun fahimci da yawa daga halayen amaryar tamu. Don kuwa ba ta zuwa ta gaida Adda in har ba Maccidon ne ya sako ta a gaba suka shigo tare ba. Sannan ni da Muhsin da muke matsayin kannen mijin ta ba mu ishe ta kallo ba. Ni ta ma fi ba ni matsayin ‘yar aikin gidan ganin yadda ta ke sa ni ayyuka cikin gadara da bada umarni. Mun fahimci dai tana da girman kai, sannan ba ta shigo gidan da niyyar gina kyakkyawar mu’amala tsakanin ta da mu ba. Adda ma bayan gaisuwa babu abin da ke hada su.
Gane hakan da Muhsin ya yi sai ya yi gaggawar janye jikin sa daga gare ta. Ni da alhakin kula da abincin ta ke wuyana dole na ci gaba da shiga sashen nata akai-akai har suka gama kwanakinsu suka wuce birnin tarayyah.
Ranar da suka tafi Muhsin ke fadin, shi wallahi gidan ya fi masa dadi. Na ce, “Ni kuma kewar su nake, ko banza ina koyon dressing, ina kallon gayu ina kwaikwaya”.
Tsaki ya yi, ya ce, “Allah ya sauwake miki Ma’u”.
Tunda su Yaya suka tafi tsakanin shi da kowa sai dai waya. Adda ta ke kokanta min rannan muna girki,
“Yayan ku yau watannin shi hudu bai zo ba, shi da a da karkari ya yi sati biyu, kodayake ya yi aure, nauyi ya karu masa, kuma dai yana kiran waya. Amma ya dace ya zo haka don lissafin mall ya fi karfin Muhsinu, jiya yake gaya min an samu batan wasu kudade masu yawa, kuma yana zargin akantocin mall don sun ga yanzu babu idon Maccido”.
Yadda ta ke maganar cikin sanyin jiki da sanyin murya dole ta ba ka tausayi. Na rasa abin da zan ce wanda zai kwantar wa da Adda hankali, amma tabbas Yaya Maccido tunda ya yi aure ya manta da mu, ya dauke kafar sa daga cikin gidan su. Ban san dalili ba, amma na san hakan is unfair don ka yi aure ka daina zuwa ganin mahaifiyar ka da marayun kannen ka.
Wasa-wasa sai da Yaya Maccido ya kwashe watanni tara ba zuwa ba aike. Wayar ma da yake kira sai ya yi sati bai yi ba. Ba dama Muhsin ya yi korafi, yanzu Adda za ta ce tunda yana lafiya cikin iyalin sa alhamdulillah. Amma ni na sani Adda na cikin matsananciyar damuwa, ba ta son dasa wa Muhsin damuwar da za ta sa ya daina girmama Yayanshi ne.
Duk ta rame ta rage walwala. Sai dai kuma ta kara karfi wajen ibada. Sosai Muhsin ya zage ya dora wa kansa nauyin da Yayansa ya sauke na kula da mall da duk wasu kudi da ke shigowa. Kuma akantocin da ya kama da yi wa shagon almundahana ya sallame su nan take, don haka sauran suka shiga taitayin su, duk da haka abubuwa da yawa na fin karfin sa in aka yi la'akari da karancin shekarun sa.
Aunty Nabeelah ce ta kira Adda a waya daga Beirut, bayan sun gaisa sai ta kanga mata kukan jariri a waya. Zo ki ga farin ciki wajen Adda a fili ta dinga fadin, “Masha Allah, tabarakallah. Mace ko namiji?”
Nanilah ta ce "namiji ne, Atiku (Aasim)".
Wani hawaye ya digo daga idon Addah, kewar Baban nasu ta zo mata. Tun tafiyar Maccido da kin zuwansa sai yau ne ta san hawayen da ta zubar a kan Maccido ne. in lissafin da ta ke yi daidai ne watannin auren Maccido goma sha daya, wanda a ciki bai fi sau uku ta sa shi a idanunta.
Nabeelah ta ce, “Adda ya wajen su Maccido? Ni tunda ya yi aure ya manta da ni, ya daina kira na, ni in na kira shi koyaushe ya ce min yana kan uzuri zai kira ni, kuma a karshe sai dai ni in kara kiran, amma ba zai taba kira na ba. Matar kuma sau uku ina kiran ta, amma yadda ta karba min ban ji dadi ba sam, shi ya sa ban sake ba”.
Adda ta nisa ta ce, “Allah ya raya min maigida na. Maccido kuma ki yi masa uzuri kin san yanayin aikin nasa, ba waje daya yake zaune ba, koyaushe yana kan furojat (project)".
Nabeelah ta bar zancen don bai gamshe ta ba, ta ce, “Muna kan hanya zuwa jibi insha Allah, gara in zo in wankan ganyen runhu da darbejiya hankalina zai fi kwanciya duk da a asibiti an ce ba sai na yi ba”.
Adda ta ce, “Rabu da su, ku zo ku yi wankanku ku sha ruwan zafi ku gasu. Allah ya kawo ku lafiya”.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE*
Nan muka shiga shirin zuwan Aunty Nabeelah, hatta ganyen da za ta yi wankan da shi an tsinko an jibge, an sayo runhu da duk abin da za su bukata, tare za mu zauna a daki na in ji Addah, don tun asali da ma dakin ta ne na gaje.
Aunty Nabeelah ta iso da kyakkyawan balaraben jaririn ta. Tun ranar da suka zo yaron ya shiga raina sabida kyawunsa, kai ka ce ni aka haifa wa jaririn nan, koyaushe yana bayana a goye. Sau uku kawai Adda ta yi masa wanka na koya na karbe ni nake yi masa safe da yamma, in cancara masa kwalliya da kayan sa masu kyau. Aunty Nabeelah na kiranshi Aasim, to sai mu ma duka muka kama.
Satin su biyu Aunty Nabeelah na lura da abubuwa. Babu Maccido babu wayar sa bayan ta gaya masa ta haihu, kuma ta zo gida. Sannan ta lura komai Muhsin ke wa Adda wadanda a baya Yayan ke yi. Sannan Adda ba ta yi mata zancen sa, ko ita ta dauko zancensa Addah za ta waske. Me za ta ce wa Nabeelah? Maccido tunda ya yi aure ya samu mata ba ta kara ganinsa ba tun watanni ukun farko, ko me? Ba ta so ta zama uwar miji mai korafi, sannan ta san Nabeelah na da zafi ba ta so ta fahimci komai.
Ina goye da Aasim ina zagaye dakin da shi don mu samu ya yi bacci sai rigimar dare yake yi. Aunty Nabeelah da ke zaune gefen gado tana gyaran kayan Aasim ta ce,
“Ma’u zo nan”.
Na karaso inda ta ke, ta ajiye rigar yaron da ke hannun ta, ta ce, “In tambaye ki mana? Za ki gaya min gaskiya?”
Na ce, “In har na sani Aunty Nabeelah zan gaya miki”.
Ta ce, “A wata sau nawa Maccido ke zuwa gida?”
Na jinjina kai ina dan tunani cikin lissafi.
“Auren Yaya Maccido ai ya shekara, amma sau uku ya taba zuwa ba, shima bai kwana ba, tunda suka bar nan da amaryar sa, kuma yanzu an doshi watanni goma da zuwan nasa”.
Nabeelah ta zaro ido a kaina kamar ni ce Maccidon, sai kuma ta boye razanar ta da mamakin ta, ta hanyar lumshe idanunta, ta ce,
“Kada ki gaya wa Adda na tambaye ki komai”.
Kai na girgiza, “Insha Allahu”.
Daga ranar Aunty Nabeelah ba ta kara kiran Yaya Maccido a waya ba, sannan ba ta kara yi wa Adda zancen sa ba. Na ga dai suna yawan kebewa ita da Muhsin suna magana. Wankan wata daya ta yi sun murmure sun yi kyau da kiba, ita da Aasim.
A ranar da suka cika kwanaki talatin ta ce da Adda ita fa ta gama wanka, za ta je yawon arba’in Abuja, tunda ta zo ba ta ga dan uwan ta ba.
Za ka iya ganin yadda Adda ta sunkuyar da kai, tsufan ta ya fara bayyana sakamakon damuwar da ta ke ciki. Ta kasa ce da Nabeelah kada ta je tunda Nabeelah za ta nemi ba’asin hakan, amma a zahiri ba ta so ta je din. So ta ke ta ci gaba da sanya wa Maccido idanu ba tare da sun bibiye shi ba har ta ga iya gudun ruwansa.
Ashe da ma a wajen ‘ya’yan yanzu mace na maye gurbin mahaifiya da shakikai?