← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 33

Sashe 28

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da wani matsanancin farin-ciki na kwana yau. Kwana na yi da tunanin Yayana-Mijina Attahir, yau na tabbata nima ina daga cikin mata masu sa'ar zuwa duniya, ban rako sauran mata ba kamar yadda a da nake tsammani.
Washegari da safe muna karyawa ni da Addah a dining Al-Qasim ya shigo gidan, ya dau wanka da karin hula kamar yadda ya saba, gaban Addah ya zo ya tsugunna ya gaishe ta, Adda ta amsa cikin far'a tareda yi masa tayin kosai da kunun da muke sha, ya dauki kosai daya a warmer ya kai bakin sa. Na ce "Yaya Al-Qasim ina kwana?" Bai juyo ya dube ni ba ya amsa ciki-ciki. Sannan ya fadawa Adda sakon da ya kawo shi. Ya bata wasu kudade masu yawa cikin leda da ya karbo mata daga banki yayi mana sallama ba tare da ya ko dubi sashen da na ke ba ya fita. A rai na nace "ka mutu da bakin ran ka, ni bani da case da kai".
A daren ranar ma raba dare muka yi muna hira ni da Yaya. Wani abun in ya fada kamar in nitse kasa don kunya. A rai na in yi ta mamaki har in tambayi kai na anya Maccido ne wannan? Cikin kwanaki biyun nan Yaya Maccido ya bi ya sukurkuta ni da soyayyar sa, ba abinda na ke so irin in bude ido in gan shi gabana.
Amma na san ganin nasa shine abu mafi wahala gare ni a halin yanzu, bani da idon da zan dubi Yaya Maccido, idan na tuna irin hirarrakin da ke fita daga bakin sa.
Washegari Juma'ah har karfe goma na safe ban fita falo ba, Adda ta aiko Hawwa kira na in karya kumallo har sau biyu ina cewa gani nan, amma ko motsawa daga bargo na na kasa. Fargaba ce fal a rai na game da zuwan Yaya don na san na yi masa alkawarirrikan da na san bazan iya cikawa ba. Kuma na san rigima ce kawai za ta kawo shi.
Wajejen karfe sha daya Adda ta shigo har dakin da kanta ta same ni, tace "Ma'u lafiyar ki kuwa? Kin san Maccido na hanya shine tun jiya baki sanar da ni ba?" Kara shigewa na yi cikin bargo na nace "ni ban sani ba Adda". Harara ta tayi ta ce "kada ki sani din, ki tashi a bargon nan haka ki nemar masa abinda zai ci, kin san ba ya son abincin 'yan aiki ni kuma yau ba dadin jiki na nake ji ba" cike da fargaba na bude bargon na ce "Adda ina ke miki ciwo?" In da abun da ke daga min hankali a duniya, to ciwon Adda ne. Ko da kuwa na farce ne. Adda ta ce "ba wani abu bane babba, dan zazzabi nake ji, amma na yi wa Al-Qasim waya zai taho min da magani anjima". Ta juya ta fita tana fadin "na fada miki ki bar gadon nan haka ki tashi ki nemar masa abin da zai ci, ki kuma nemi wani abu ki sa a cikin ki".
Tsaye nake jikin island din kicin ina tunanin me zan dafawa Yaya? A karshe na yanke shawarar gasa masa kifi manyan karfasa da Al-Qasim ya kawo jiya, nan na soma hada spices din cire karni da kayan hadin da zan wa kifin, sannan na dora ruwan zafi a wuta da nufin in yi masa tuwon acca da miyar egusi.
Aikin da ya dauke ni awanni biyu, sannan ne na samu na yi wanka, na ci abinci, sassaukar kwalliya na yi don kada Adda ta gane ina dokin zuwan Yaya Maccido a yau fiye da kowacce rana a rayuwa ta.

*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
07030137870
Chapter 28 · 0% Book details