← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 33

Sashe 21

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A Ajrah (taxi) muka tafi filin jirgi bayan ya tabbatar na maka niqaabi sai ka ce mutanen takari. Muna zuwa jirgin wanda ya taso daga Lebanon yana sauka. Sai da aka bata lokaci kafin Aunty Nabeelah ta iske mu, da gudu na sheka na rungume ta. Aasim da ke gefe ya shiga ture ni yana kiran sunan Babar sa.
Dariya muka yi, na rusuna na sunkuce shi dan lukuti da shi, kamar ba jaririn da na sha rainon sa ba. Sai Larabci yake yi accent din Lebanon. Yaya ya tura trolley din ta muka nufi inda taxi suke.
Yaya da mai Ajrah suna gidan gaba, ni da Aunty Nabeelah da Aasim muna baya, sai kallo na ta ke yi kamar yau ta fara gani na. Tana yi tana murmushi. Wanda na kasa gane ma'anar sa.
Na ce, “Aunty, wannan kallon fa?”
“Ina kallon yadda kani na ya iya kiwo ne, gabadaya kin yi kyau. Kin zama kamar balarabiyar Maghrib”.
Na rufe fuska ina dariya, na ce, “Aunty ai kullum fada muke yi”.
Wani takadarin murmushi ta yi, ta ce, “za ku yi mai dalili ne, wannan na rashin dalili ku ke yi”.
Ban dai gane abinda Aunty Nabeelah ke nufi da hakan da ta ce ba.
Daidai lokacin da muka shiga farfajiyar asibitin Doctor Sulayman Faqeeh. Tun kafin Yaya Maccido ya fito na bude kofar bangare na na fice dauke da Aasim. Ina kallon su suka tsaya gefe suna magana wadda ban san me suke tattaunawa ba. Daga baya suka shigo muka jera gabadaya zuwa dakin V.I.P da aka sake maida Addah.
Ina murda kofar dakin gabana ya yi wani irin muguwar yankewa ya fadi, sakamakon kalmar shahada da na jiyo Addah na furtawa cikin wata irin murya da ban taba jinta da ita ba.

*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI 07030137870*

```HISABIN NAFS```

(YIWA KAI HISABI)
Adda muka taras na zaune a kan gado, jingine da filo sai salati take a fili, salatin da tun daga waje ya tsorata mu, ya sa muka karaso dakin da gudun mu. Na karasa da hanzari na rungume Addah ta. Hawayen farin ciki na zubo min. Farin cikin ganin cewa lafiyar ta kalau. Ga ta zaune akan kafafun ta. Amma tabbas salatin da muka tsinkayo tun daga waje tana rafkawa ya bala'in tsinka mana zuciya dukkan mu.
“Ma’u na, Ma’un Addah, sannu da kokari kin ji? Allah ya baki ladan jinya”.
“Adda, yau farin ciki zai kashe ni, kin samu lafiya, Allah abin godiya”.
Aunty Nabeelah da Yaya Maccido suka karaso gaban gadon, Aasim yana hannun Yaya Maccido, idanun Maccido duk sun raina fata. A sanyaye ya ce,
“Addah, sannu da jiki, Allah ya sa kaffara ne, Allah ya kara lafiya”.
Ta amsa ba yabo ba fallasa tana mai kawar da kai daga gare shi. Tare da daure fuska. Aunty Nabeelah ta kama hannun Yaya Maccido ta rike cikin nata ta ja shi suka karasa gaban gadon Addah. Su duka biyun suka tsugunna a gaban ta bisa gwiwoyin su. Cikin sanyin murya Nabeelah ta soma magana da tattausar muryar da duk mai imani dole ya tsaya ya saurare ta.
“Addah, Maccido ya yi laifi, laifi kan laifi kam ya yi shi. Tun kina alkunya har bacin ran ya fito fili, ya kuma shafi lafiyar ki. Maccido mutum ne dan adam kuma ajizi kamar kowa, wanda bai fi karfin sharrin shaidan da rudin duniya ba, har ma da iblisanci irin na mata.
Addah yau ga Maccidon ki a gaban ki, ya kawo kan sa matsayin mai laifi a gare ki, yana mai amsa dukkan laifukan sa. Fatan sa kawai ki yi hakuri ki manta komai, ki yafe masa. Ki kuma ba shi dama ya gyara kurakuren sa.
Tun ranar da ya iso ya same ki cikin halin da ki ke ciki, sakamakon wayar da Muhsin ya yi masa, tun kafin lokacin dama yana cikin damuwa da nadamar da ya rasa ta yadda zai bi ya gyara wannan kuskuren na kaurace miki, ya ce shi kansa in za'a kashe shi bai san dalili ba, ya shiga tunanin hanyar da zai wanke zuciyar ki, ya kuma zama kullum ko ba ya nan wani bangare nasa yana tare da ke wanda zai hana ki yin kewar sa da tunanin sa ko iyalin sa.
A kan haka ne Maccido ya yanke shawarar auren Ma’u, Asma’un ki….”.

Daga ni har Adda da ta sunkuyar da kai a firgice muka dago muka dubi Aunty Nabeelah. Wata irin firgita da ban taba yin irin ta a rayuwa ta ba. Idanu na suka yo waje bakidaya ina son jin ainihin me Aunty Nabeelah ke nufi???
Ba ta damu da reaction din mu ni da Addah ba ta ci gaba da bayanin ta hankali kwance, murmushi dauke bisa kyakkyawar kamilalliyar fuskar ta.
"A ranar da ya kira ni ya gaya min, na ce ban yarda ba in har ya san ba son Ma’u yake ba, ya kyale ta a hankali za ta samu mijin ta. Sannan Ma’u yarinya ce ba za ta iya zama da kishiya ba. Balle hamshakiya irin matar sa, wadda uwar sa ma ba ta dauke ta a bakin komai ba.
Maccido ya gaya min duka hujjojin sa kuma na amince da su. Ya ce bai zo neman auren Ma’u don ya faranta miki kadai ba, sai don yana bukatar karin auren sabida matsalolin cikin gida da yake fuskanta daga matar sa, sannan ya hanga ya duba babu wadda zai aura ya wanke zuciyar ki, ya yi miki ramakon duk abin da ki ka rasa daga suruka da jikokin da ba a bari kin shaqu da su ba irin ASMA’U.
A takaice ma dai a kan karan-kansa yana son ta Addah, tuntuni, tun tana kankanuwa. Lokacin da yake son yin aure bata isa aure ba, shi ya sa ya nemo aure a waje, amma wannan niyyar tana nan cikin ran sa.
Na gamsu da dukkan bayanan sa Addah, ya kuma ce min zai dauke ki zuwa asibiti a Jeddah, yana so a daura aure kafin ku tafi don Ma’u ce mai jinyar ki, kuma bai kamata ya tafi da Ma’u irin wannan tafiyar babu aure tsakanin su ba.
Na ce hakan ba zai zamo gaggawa ba? Ya ce ai shi so yake duk ranar da ki ka bude ido, ki gan shi da Ma’u matsayin matar sa, watakila ya ci alfarmar hakan ki yafe mishi dimbin laifukan sa gare ki.
Adda kin ji yadda muka yi da Maccido. Na amince da duk abin da ya ce, na ce ya je ya samu Baffa Bilya ya gaya masa komai, sai su je Bebeji su nemi Malam Ayuba da ki ke yawan ba ni labari, wanda ki ka ce shi ne aminin Baban Ma’u tun daga kuruciya har girma. Su kai masa sadaki a daura aure.
Muhsin shi ya jagoranci su Baba Bilya zuwa Bebeji, ba su sha wahalar samun sa ba duk da ya tsufa, bayani kadan suka yi masa ya sa kukan farin ciki sabida wannan karramawa da suka yi masa na ba shi waliccin auren Ma’u.
Shi ya ja su zuwa gidan Hakimin Bebeji ya yi masa bayanin Ma’u, shi ma sosai ya ji dadi, don ya ce Baban Ma’u mutumin sa ne, duk Juma’ah sai ya zo ya gaishe shi. Kasancewar ranar juma’a ce sai Hakimi ya bada sanarwa cewa bayan sallar juma’a akwai daurin auren ‘yar Malam Adamu mai goro.
Aka yi daurin auren cikin farin ciki na zukata masu yawa, Baban su Ma’u ya sha yabo da addu’a daga bakin jama’ar garin Bebeji kamar yadda Muhsin ya labarta mini”.
Ta sa hannu cikin jakar hannunta ta fiddo wani dan akwati tana murmushi, ta dora wa Addah a kan cinyar ta,
“...Addah ga sadakin Ma’u. Muhsin ya gaya mini kin sha ce masa 'sisinan gwal' shi ne sadakin Ma’un ki…”.
Ta bude akwatin ta kama tafin hannun Addah ta dora mata.
Kuka ne ya kubuce wa Addah Kilishi, ta kamo hannun Nabeelah ta kamo na Maccido ta ja su jikin ta ta rungume su.
“Allah ya yi muku albarka baki dayan ku, yau na san na haifi ‘ya’ya, wadanda ko bayan raina za su rike min marainiyar ‘yar dan uwana da amana da daraja da kauna. Barakallahu fi-kum”. Ta sake kecewa da kukan farin ciki.
Chapter 21 · 0% Book details