← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 33

Sashe 17

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

((9)). Na mike na kai ma Yaya Maccido wayar sa, ya ce, “Gobe zan hada miki waya, way ata ta daina shiga hannun ki bakauyiya kawai, kada ki lalata min. Dubi duk kin shafa min maiko a jiki”.
Ni dai ban ce komai ba, na je toilet na wanko hannuna da bakina. Sanda na fito yana shirin barin dakin.
Ya ce, “Zan je supermarket me ki ke so?”
Kaina a kasa na ce, “Sai dai in rubuta maka”.
Ya jingina da kofar dakin, ya ce, “Ok, hurry”.
Jakata na jawo, na dauko jotter da biro. Da rubutuna mai kama da na ‘yan firamare na rubuta masa duk abin da nake bukata, pad ce ta karshe wadda na rubuta ina runtse ido cike da kunyar kaina.
Ya karba yana dubawa, sai da ya tattara hankalin sa ya gane abin da na rubuta. Ya sa takardar a aljihun sa ya fice.
Niki-niki ya dawo da ledoji, har ma abin da ban ce ba in dai ya san zai min amfani a zaman da za mu yi, ya siyo min. sannan ya sayo min ice-cream.
Hannuna da nashi ya miko min ledar ice-cream din, ya ce, “Ki sha, ko ki sa a fridge kada ya yi melting (kada ya narke)”.
Har raina na ji dadin karamcin da ya yi min, na kuma ce a raina, ashe Yaya in ya ga dama yana da kirki?
Har karfe goma sha dayan dare yana zaune yana ta buge-bugen waya, har Ihsan sai da ya yi magana da ita. Kamar in ce ya ba ni yarinyar, sai kuma dai na yi shiru.
Ina ji ya yi magana da Al-Qasim da Muhsin. Ban san me Muhsin ya ce masa ba, ya ce, “Wallahi ba zan ba ta waya ta ba, maiko ta ke shafa min, gobe zan hada mata tata sai ku yi ta yi”.
Ya mike yana kallo na kai tsaye daga tsakiyar idanun sa.
“Zan je na kwanta Asma’u, sai da safe”.
Yadda ya siranta muryar shi ya ba ni mamaki. Na dago a hankali sai ido na cikin nasa. Da sauri na kawar da kai sabida ba zan iya jure kallon da nake gani cikin idon sa ba. Mamaki da tu’ajjibi kamar su kashe ni.
“Sai da safe Asma’u”.
Ya sake fada da irin muryar dazun, sannan ba tare da ya jira amsawa ta ba ya juya ya fita, ya rufe min kofar.
Gani na yi in na zauna ina mamakin Yaya Maccido mai halaye irin na wahainiya, to kuwa zan kwana a zaune. Yau na wuni da Maccidon da ban taba wuni da shi shekaru goma sha tara ba. Yau na ga bangarori da yawa na Maccido, wadanda ban taba sani ba. Karewa ma yau har a jikin Maccido na kwanta. Na girgiza kai tare da mikewa na dauro alwala, na zo na dasa sallah, sai dai kuma na rasa abu na biyu da zan roki Ubangiji bayan samun lafiyar Addah. Sabida tunani na na yau bakidaya Maccido Tahir ya cukurkuda shi.
A gaban Addah na kwana, zaune a kan kujera kaina bisa gadon ta, hannu na rike da hannun ta. A haka barci mai nauyi ya dauke ni, sai kiran sallar asubahi na tsinkaya daga dan nesa da mu. A hankali na zame hannuna daga na Addah wadda ke ta barci, amma ta kan motsa lokaci zuwa lokaci. Na gyara mata kwanciya sannan na dauro alwala na tada sallah.
Da na fito na tadda nurses da doctors sun shigo suna kanta, don haka sallahta na tayar. Fatan mu Allah ya sa a yi aikin nan cikin sa’a.
Sai karfe takwas Yaya Maccido ya shigo, a hannunsa ledojin karin kumallon mu ne. Ciki-ciki ya yi sallama, ni ma ciki-cikin na amsa masa. Kai tsaye wajen Addah ya dosa wadda ta bude ido tana kallon mu tarr! Amma ba ta iya ce mana komai, sai wasu siraran hawaye da suka biyo ta gefen idon ta.
Gaba dayan mu muka yi kanta da sauri ni da Yaya, ya ce, “Addah, me ki ke so?”
Ni kuma na ce, “Addah, ina yake miki ciwo? Ko in kira likita?”
Girgiza kai ta yi, sannan a hankali ta lumshe idanun ta. Kafin ta kai hannu ta kama hannuna ta dauke kanta daga duban Maccido. Ya kara dawowa saitin da ta maida fuskar ta. Addah ta sake dauke kai daga gare shi, wannan abu ya tada hankalin Maccido kamar ya fashe da kuka. A kan gwiwoyin sa ya gurfana ya kama hannun Addah ya kankame ya soma magana cikin rawar murya.
“Addah…. Na sani… ni din mai babban laifi ne… laifin da ya cancanci kowanne irin hukunci daga gare ki. Sai dai kuma ina so ki sani, na gane kure na, a yau kuma ga ni na zo na gurfana a gaban ki ina mai neman yafiya da afuwar ki. Ina mai daukar miki alkawarin ba zan sake yin nesa da ke ba. Na sani cewa, na ba wa neman duniya da hidimar iyali na muhimmanci fiye da ke a baya. Ina rokonki Addah ba don hali na ba, ki yi duba ga dumbin alfarmomin ku na iyaye ga mu ‘ya’yan ku ki yafe min Addah, ki ba ni dama in gyara kuskurena ta hanyar da hakan ba za ta sake faruwa ba.
Na zo miki da kyakkyawan albishir Addah, wanda na tabbata zaki ji dadin sa, duk don in wanke laifi na daga zuciyar ki, wanda nake so ki dubi alkhairin da ke cikin sa ki yafe min Addah…”
Hawaye ya zubo daga idanun Addah, ba ita kadai ba, dukkan mu babu wanda hawaye bai zubowa ba. Ni dai nawa na tausayin su ne su duka, da farin cikin kalaman da yake gaya wa Addah a yau, na kuma tabbata nadamar nan da yake fadin ya yi, da gaske ya yi ta. Domin za ka iya ganin ta zane baro-baro cikin fararen kwayar idanun sa, wadanda suka rine da hawaye suka koma light brown masu sheki, sai walainiya suke cikin duhun labulayen dakin da kuma hasken fitila da ba a kunna ba.
Addah ba ta yi wani nuni da ke nuna ta yi na’am da kalaman bakin sa ba, ko ta san me yake fadi, a hankali ta lumshe idon ta ta koma barci. Ni kuma na koma gefe na dau daya daga cikin ledojin abincin da ya zo da su na soma ci. Ina ganinsa ya ja kujera gaban Addah ya zauna yana kallon ta with so much affection, ba ya ko kiftawa. Sai da wayarsa ta yi kara ya tashi, ya fita don ba ya so maganar sa ta tada Addah daga barcin da ta samu.
Sai bayan azahar ya fita, ya dawo sanye da jallabiya mai gajeran hannu ruwan madara, wadda na tabbata a nan garin ya saye ta. Kamshin jikin sa ya canza daga turaren obsession ya koma amfani da oud abyad. Bakin balaraben Saudiyyah Yaya Maccido ya koma daga zallar baturen sa na baya. ‘Yar farar ledar da ke hannunsa ya miko min.
Hannu biyu na sa na karba da na fahimci kwalin karamar waya ce iphone mai shegen kyau da tsada.
Na ce, “Yaya, na gode. Amma ban san ya ake amfani da ita ba”.
“Ki koya a hankali". Kawai ya ce ya karasa yana taba wuyan Addah.
Sai juya waya nake a hannu na, ina mamakin wai wannan tsaleliyar wayar tawa ce ni Ma'u. Ko Muhsin da Al-Qasim tasu ba ta kai aji da mukamin tawa ba.
Sai ji na yi kira ya shigo cikin wayar. Da sauri na ce, “Yaya…”.
Sai kuma na yi shiru ganin ya juyo yana harara ta. Wayar na mika masa ya nuna min inda zan danna, na yi maza na amsa fuskata fal murmushi da na ji Aunty Nabeelah ce.
“Larabawan Jeddah, ya ku ka kwana? Kaifa haalikum! Ya jikin Addah?”
Na ce, “Alhamdu lillah aunty, bikhairin wa aafiyah, ya ya Aasim?”
Ta ce, “Ai ya shiga kindergarten yanzu ba zaman gida. Maccido ya gaya min ya saya miki waya”.
“Eh Aunty, ki taya ni godiya, ni in na yi masa magana harara ta yake yi”.
Dariya Aunty Nabeelah ta yi, ta ce, “Harara as in how?”
Na ce, “Harara sosai, kamar wadda ta yi masa laifi”.
A hankali nake magana yadda na tabbatar ba ya ji na. A rashin sani na yana da karfin ji, tsaf yake jin duk abin da nake fada a kansa.
Aunty dai ba ta bar dariya ba, ta ce, “Ina fata dai yana kyautata miki, duk abin da ki ke so yana sayo miki?”
Na san in na ce Yaya ba ya yi min abubuwan da ta ambata din na yi masa karya, watakila har Allah ya tsaida ni hisabi da shi a kan hakan. Don haka na ce da Aunty Nabeelah,
“Ba ni da wannan matsalar da shi, ya sayo min komai har da wanda ban ce ina so ba, yana da alkhairi sosai”.
Murmushi Nabeelah ta yi, ta ce, “To masha Allah, don’t mind hararar sa tunda dai ita ce kadai matsalar sa”.
Ba jimawa kiran Muhsin ya shigo, na amsa da kaina don na rike inda Yaya ya nuna min dazun.
Ya ce, “Ma’u na ta yi waya, ta zama babbar yarinya, ya jikin Addah kuma ya aka ji da sabon wuri?”
Na ce, “Wato da karamar yarinya ce tunda ba ni da waya ko?”
Ya ce, “Eh mana!”.
Na yi dariya na ce, “Addah gobe da safe za a yi aikin ta, sai a ci gaba da taya mu addu’a. Ashe Baban Ihsan ba laifi yana da kirki, kai dai bar shi da harare-harare”.
Dariya Muhsin ya saki, ya ce, “Allah ko? In ya ji ki ya kwace wayar sa babu ruwa na”.
Na ce, “Ina Al-Qasim?”
“Ga shi a gefe na”.
“Ba shi mana mu gaisa”.
“Ya ce ba zai yi magana da ke ba”.
Cikin mamaki na ce, “Sabida me?”
Muhsin ya yi wani irin murmushi, ya ce, “Abin sirri ne. Ki shafa min kafar Addah in samu albarkar ta”.
Har muka kashe waya ni da Muhsin ina ta mamakin wai yau Al-Qasim ne ya ce ba zai yi magana da ni ba, ni din da a da ba wanda yake son kulawa iri na. Duk da share shin da na ke yi. To me na yi masa???
Chapter 17 · 0% Book details