← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 33

Sashe 1

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*

*SHIMFIDAR LABARIN*

((1)). Sunan da na taso da shi tun haihuwata shi ne MA’U. Cikakken sunana na usul Nana Asma’u Adam Bebeji. Ma’u ya bi ni ne daga bakin mahaifiya ta Nene tun ina karama. Mahaifi na Malam Adamu bafullatanin garin Bebeji ne, wata babbar alkarya a kananan hukumomin jihar Kano. Yayin da mahaifiya ta Nene Zainabu ta fito daga kauyen Babura ta jihar Jigawa.
Nene baka ce amma doguwa kyakkyawa, wadda ta yi tashen manema a zamanin kuruciyar ta, a karshe dai Allah ya yi ta zama rabon mahaifi na, wanda cin kasuwa ne ya kai shi Babura kamar yada ya saba duk ranar kasuwar garin. Ya ganta a kasuwa tana tallan fura, farat daya ta shiga zuciyar sa, ya sa kai da gaske wajen neman aurenta da karfin sa, har Allah ya ba shi sa’a, ya sure ta zuwa mahaifar sa, Bebeji.
Sana’ar mahaifi na shi ne kasuwancin goro, da wannan sana’ar ya dogara tun yana saurayi har zuwa shekarun girman sa. Sana’ar goro ta karbe shi don har Shagamu yake zuwa ya auno goro, ya kai shi kasuwannin gari-gari, kuma da ita ne ya raine mu ni da kanwa ta kwalli daya, Arifah. Mu biyu Allah ya bai wa iyayen mu kamar yadda shi ma mahaifinmu su biyu ne kacal a wajen iyayen su, shi da Yayar sa, Adda Kilishi.
Tsakanin mahaifi na da Adda Kilishi akwai ratar shekaru masu dan dama, sai da ta yi shekaru bakwai a duniya sannan aka haife shi.
Ba zan manta ba Baba ya sha gaya mana yadda Adda ta yi ta wahala da shi yana yaro, duk inda za ta goya shi ta ke ta tafi da shi, sannan ba yaron da ya isa ya taba mata shi. An yi mata auren wuri, wanda ya janyo rabuwar su domin shekarun ta goma sha hudu ta yi manemi daga garin Sokoto, mai suna, Atiku, abokin sa ya zo gani a garin Bebeji suka hadu kuma cikin dan lokaci suka aminta da juna. Iyaye kuma suka amince da nagartar sa bayan dogon bincike suka aura wa Adda Kilishi Atiku Dogon Daji, ya tafi da ita Sokoto garin iyayen sa. A lokacin yana aiki da ma’aikatar sadarwa ta kasa, wato Ministry of Communication and Digital Economy .
Alhaji Atiku Dogondaji ya dade yana aiki a can, ko da suka maida shi jihar Rivers, wato Port-Hearcourt bai tafi da iyalin sa ba, a Sokoto ya bar su, Adda ta ba ni labari cewa duk karshen shekara yana daukar hutu ya zauna cikin iyalin sa kuma duk bayan watanni ukku yake zuwa Sokoto.

Tun ina goye Adda Kilishi ke hidima da ni, sutura da kayan wasa kamar ba a kauye nake rayuwa ba. Akai-akai Adda ke zuwa daga Sokoto ta yi wa iyayena goma ta arziki, ni kuma ta yi min sayayyar suttura da kayan wasa da ta saba kawo min duk zuwan ta Bebeji. Adda ba ta dogara da mijin ta kadai ba, tunda ya kasance ba ta yi zurfi a karatun zamani ba, tana aji uku na karamar sakandire aka cire ta aka yi mata aure, kuma mijin ba ya bukatar ta ci gaba, ya ce nashi karatun ya ishe su, sai ya ba ta jari ta ke kasuwanci. Sana’ar Adda atamfofi ne da lesissika da mayafai na mata, sana’ar ta karbe ta don har shaguna gare ta manya guda biyu a kasuwar (Dan Jabalu). Tana yo odar kayanta ne daga waje ta zuba a shagunan ta, kuma Allah ya ba ta nasibi sosai a wannan harkar.
Iyakar kulawa da tarbiyya muna samunta ni da kanwata Arifah a wajen iyayen mu, da yayar mahaifinmu Adda Kilishi. Kuma haihuwar Arifah bai ture gwamnati na daga wajen Adda ba, gatan da nake samu a wurin ta Arifah ba ta samu. Allah bai yi Arifah mai tsawon rai ba ce, shekarun ta biyar ta kamu da cutar kyanda (bakon-dauro) wadda ta yi ajalin ta.
Duk shaquwar da ke tsakani na da Adda ba abin da na tsana irin zuwa wurin ta a Sokoto, ba don komai ba sai don halin ‘ya’yan ta. Babbar wato Nabeelah cin zalina ta ke yi, shi kuma Yaya Maccido (Attahir) mai bin Nabeelah yana da tsanani akan ilimin boko, daga ni har Muhsin autan Adda wanda shi ne tsara na cikin ‘ya’yan ta don shekaru biyu kawai ya bani bakar wuya muke sha a hannun su.
Don haka ne daga baya da na yi wayau idan Adda ta zo ta kuma fara shirin tafiya, to fa za a neme ni ne a rasa har sai ta bar gari. Tun ba ta gane ba har ta gane gudun zuwa gidan ta nake. Rannan ta zaunar da ni don jin dalili cikin lallashi, inda na sadda kai na gaya mata gaskiya, karatun Yaya Maccido ne bana so. Maccido ga bulala in ya koyar ba ka iya ba. Ni kuma a rayuwa ta Allah ya halicce ni da kin karatun boko.
Ranar da na gaya wa Adda dalili na na kin gidan ta ta dade tana jan hankali na cewa; Maccido so yake mu zamo masu hazaqar karatu irin nasa, mu dinga ciyo kyaututtuka na ban mamaki a makaranta irin wadanda kullum yake ciyowa, mu zamo zakaran gwajin dafi cikin tsararrakin mu kamar yadda yake. Ba da nufin takura mana yake yi ba.

Sunan Sultan Of Sokoto Mohammad Attahiru aka sa wa Yaya Maccido, dalilin da ya sa iyayen ke kiransa Maccido ke nan. Mohammad Attahiru shi ne Sarkin Musulmi na goma sha uku a Seat of Caliphate. Iyayen sa na fatan ya dauko halayen sa da soyayyar sa da gudummuwar sa ga addinin musulunci, shi ya sa suka sanya masa sunan sa.
Kamar yadda na fada a baya, daga Adda har mahaifina Malam Adamu Allah bai ba su yawan haihuwa ba. Daga ni sai Arifah Allah ya nufe su da haifa wadda ita kuma ba ta yi tsawon rai ba. Ita kuma Adda daga Nabeelah da muke kira Aunty Nabeelah sai Yaya Maccido, bayan haihuwar Maccido sai da Adda ta kwashe shekaru goma sha biyu ba ta sake haihuwa ba, har ana tunanin haihuwar shi ke nan ta kare, sai kuma Allah ya kawo, Muhsin.
Duk cikin ‘ya’yan Adda Muhsin shi ne mai kirki, shi ne bai yo halinsu na mugunta, cin zali da takura wa dan Adam ba. Watakila wannan ne dalilin da ya sa na fi shakuwa da shi, watakila kuma don shi ne kusan sa’a na (tsara) na shi ya sa na fi son sa da kaunar sa.
Na taso a gaban iyaye na cikin samun ingantacciyar tarbiyyar addinin islama, da kuma samun cikakken gata wanda bai sa ni na kauce wa tarbiyya ba.
Allah da ya halicce ni shi ya sanya min kin karatun boko, wahala yake ba ni, bana fahimtar sa ko kadan, kullum ni ce ta-kashin aji, ni ce mai daukar ta karshe a duk jarrabawar da ake yi mana tunda na fara firamare har na gama ta.
Kuma da ya kasance iyaye na ma ba masu ilmin zamanin ba ne sai hakan bai taba damun su ba, domin kuwa ina bada himma a karatun islamiyya, itama ban iya hada baki ba saidai hadda, shekaru na goma sha biyu na haddace rabin Alkur’ani. Sauran littattafan addini kuwa idan ina ja ina tarjama a haddace tsammani za ka yi diyar wani shehin malami ce ni.
Idan ana maganar kyau na san ba za a lissafa da ni ba. Kyawu na kadaran-kadahan irin na mahaifiya ta. Babu muni, sannan babu kyau na bada labari. Baka ce ni, doguwa, mai dan kauri, wanda kalar fata ta ya fiddo zahirin kasancewa ta cikakkiyar bahaushiyar Kano jikar Barbushe da Tsimbirbira.
Gashin kaina yana da cika da karfi, amma babu tsayi, idan aka yarfa min kitso yana da ban sha’awa, domin ba ka ganin kyawun gashina sai idan an yi min sabon kitso kanana. Babu wanda nake bari ya taba min kai sai Nene (sunan da nake kiran mahaifiya ta Zainabu) kuma sunan ya bi bakin kowa, duk shiyyar mu da Nene ake kiranta.
Lokaci-lokaci mu kan je Babura inda dangin mahaifiya ta suke, iyayen ta sun dade da rasuwa, amma akwai birbishin dangi na iyayen nata da iyalinsu a raye.
Chapter 1 · 0% Book details