← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 33

Sashe 13

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

BAYAN WATANNI SHIDDA
Bayan watanni shidda na zana waec, neco da jamb da taimakon Malam Sa’ad ta karkashin kasa. To sai dai ko da sakamako ya fito ban ci jamb din ba, ita ma waec din credit hudu na samu. Duka gidan babu wanda bai jinjina min ba tare da tabbatar min da cewa, na yi abin kirki, na yi kokari kada in bari gwiwa ta ta sage. In bari shekara mai zuwa in sake maimaitawa.
Al-Qasim kuma ya ce, kafin zagayowar shekarar za mu ci gaba da karatu da Malam Sa’ad, kuma zai dinga koyar da ni ilmin na’ura mai kwakwalwa. Ya sayo dankareriyar kwamfutar kan cinya laptop ya kawo min matsayin gudunmuwar sa.
Zuwa wannan lokacin kowa ya gama fahimtar inda Al-Qasim ya sa gaba a kaina. Ni din ce dai ban taba sanya wa raina komai ba, na dauka yana hidima da ni ne kawai a matsayin aikin sa da yake karbar albashi a kai kamar yadda ya ke kula da komai na gidan.
Domin zuwa yanzu ya zama personal assistant din Yaya Maccido, wanda duniya ta gama bude wa kofofin arziki ko ta ina. Ya zama babban director a Julius Berger, ya dade da barin gidan sa na Gwarimpa ya gina wani a Apo. Sun koma shi da gimbiyar tasa da ‘yar su wadda aka ce ta kusan haihuwar cikinta na biyu. Duniya ta yi mata yadda ta ke so, komai ya yi acan-acan.
Maccido ya zama nata ita kadai, daga ita sai ‘ya’yan da ta ke zubo masa.
Na san a rayuwa in Adda na da damuwa, to ta Maccido ce, wanda ya cire ta daga kan hanyarsa. Tsakanin ta da shi gaisuwa a waya sai kuma in ya bushi iska ya leko bayan watanni masu yawa. Ita kuwa Lubabatun ma tun zuwansu haihuwar Ihsan ba ta kara zuwa Sokoto ba. Ta zama Abuja -Woman, daidai da burin ta.
Ranar wata asabar Yaya Maccido ya bugo wa Adda waya ya sanar da ita haihuwar Lubabatu, an samu da namiji. Yanzu haka suna can gidansu Lubabatun ita da yaran a garin Birnin Kebbi a can za ta yi wanka. Yaya ko tunanin ya dauko su ita da jaririyar ya kawo wa Addah ta ga jikan ta bai yi ba, sai a hoto ya turo mana hoton sa.
Aunty Nabeelah rannan da suka yi waya da Adda bata san ina toilet din ta ina jin su ba, ina ji tana share hawaye tana labarta mata irin banzatar da itan da Maccido ya yi, tsakanin ta da shi sai waya, ba ta isa ya tako ta ganshi ba balle ‘ya’yan sa.
Aunty Nabeelah ta ce, “Addah ke ma kina da laifi, tunda na ga take-taken yarinyar nan Lubabatu tun farko na nusar da ke kan ki dauki mataki, ki kuma sa a taya ki da addu’a a kan Maccido, amma ki ka ce ke ba za ki yi kutse cikin rayuwar sa da iyalin sa ba. Sannan ba za ki sa wani ya yi miki addu’a a kan dan da ki ka haifa ba.
To Addah zamani ya canza... Kina barci ana yi miki minshari, dan hakin da ki ka raina sai ya tsole miki ido. Sai yanzu da abubuwa suka fi karfin control za ki koka? Ai kawai ki ci gaba da hakurin ki kuma dage da addu’a, amma Maccido ya yi mana nisa”.
Aunty Nabeelah ta fada tana share hawaye ita ma. Tana tuna kuruciyar su mai dadi da kanin ta Maccido.
Tun daga ranar damuwa ta ci gaba da taba lafiyar Addah a hankali-a-hankali. Ta soma ciwuka a tsaitsaye tana danne shi da karfin ran ta. Kullum jarumta ta ke ta nuna cewa lafiyar ta kalau, amma a zahirin gaskiya ba ta da lafiya.
Muhsin da ya zo weekend don yanzu ya tattara ya koma hostel ya takura mata kan ta je asibiti, ta dage ita lafiyarta kalau, amma kuma kullum a kwance ta ke wuni a daki, ko falo ba ta iya fitowa. Al-Qasim ma ya yi ya yi a je asibiti, amma Addah ta ki.
Ciwo sosai ya ci karfin Addah wanda aka rasa gane kansa da gindin sa, ya zamana ko sallah ba ta iya yi sai a zaune. Al-Qasim ne ya dauko likita mace ya kawo har gida don ta duba ta.
Likitar ta dudduba ta, sannan ta dauki jinin ta ta ce akwai gwaje-gwajen da za ta yi a asibiti kafin ta san hakikanin me ke damunta. Ta takurawa Addah aka wuce da ita asibiti don cikin ta da za a yi wa scanning sabida kukan ciwon ciki da ta soma yi.
Kafin result din gwaje-gwajen Addah ya fito Addah ta daina shaida wanda ke kanta. Daga ni har Muhsin da Al-Qasim mun kasance cikin madaukakin tashin hankali. Hankalin mu bai kara tashi ba sai da sakamakon gwajin ya fito inda suka sanar da mu Addah na fama da ciwon koda ne. Akwai bukatar a yi gaggawar yi mata aiki a cire stones daga cikin kodar ta.

https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d
Chapter 13 · 0% Book details