← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 33

Sashe 10

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Bayan ya koma dakin barcin su da kamar mintuna talatin Aunty tace inje in dauko mata kofi a kitchen din zata sha magani. A hankali na bude kofa na fita ina taku cikin sanda kada su ga na shigar musu kitchen, na dauko kofin na dawo zan wuce ta kofar dakin da suke naji tashin muryar Yaya, kamar an ce da ni in tsaya.... kawai na tsaya jin yana magana kamar zai yi kuka.
"Amma Lubabatu kina tsoron gamuwar ki da Allah kuwa? Tun shekaranjiya nake bin ki akan ki bani hakki na kina wulakanta ni, kawai saboda 'yan uwa na sun zo gidan ki, ke su waye ba kya kawowa daga gidan ku na taba nuna miki bacin rai ko bakin halin da kike nuna min?
Kinsan dai bani da kamar su duk fadin duniya dole su zo inda nake. Lubabatu in ban zo wajen ki ba matan titi kike so inje in nema? Kin san dai ina jure komai cikin tarin wulakancin ki, amma banda wannan horon naki.... Don Allah Lubabatu ki min rai...zan iya mutuwa kafin safe....".
Ji nayi ya karasa maganar muryar sa na rawa. Yana rufe baki ta bishi da mugun tsaki. "Ai na gaya maka this is your punishment, gobe ka sake basu fuskar zuwar mana gida, wannan Nabilar mai idanun munafurci a cikin idon ta na gane bata kauna ta. To sai dai ta mutu amma bata isa ta fidda ni daga gidana ba don ni wargi ce daidai kungurun kowa, wallahi ta dade bata zo ganin kwaf gida na ba......".
"Duk na ji Sweetheart, mun yi miki laifi nida 'yan uwa na, but pls don't punish me that way......Bani da wannan juriyar kin sani.....". Da dan banzan sauri na daga kafa na bar wajen zuwa dakin mu, jiki na babu inda ba ya rawa, ban san me yake rokon ta yi masa ba amma na san bai kamata ba tsayawar da na yi.
Kwana na yi da abun a raina, yana ci min rai, ashe Yaya Maccido duk kwarjinin nan nasa a cikin gida kwallo ake da shi kamar ball ko gare-gare abin wasan yara? Sai na samu kaina da mugun jin haushin Lubabatu, don ta samu Allah ya bata miji kamar Maccido shine take wulakanta shi? To ita meye matsalar ta da 'yan uwan sa ne? Me muka tare mata???
Bani da wanda zan gayawa abinda na ji ba tare da yayi min fada ba, don haka na bar abun a raina amma ya kasa bace min a zuci.
Washegari ba mu sa Lubabatu a idon mu ba har muka shiga mota, Yaya kam tunda ya dawo masallaci bai koma nasu dakin ba yana tare da mu har muka shiga mota. Kamar ba za su rabu ba shi da ‘yan uwan sa, haka Muhsin ya ja motar ya bar Yaya with nostalgia (begen gida).
Tunda muka kamo hanya Aunty da Muhsin ke tattaunawa a kan abin da suka gano gidan dan uwan nasu. Ina ji suna shawarwarin abin da za su fada wa Adda da wanda ba za su fada mata ba. Tunda aka fita garin Abuja barci ya yi awon gaba da ni. Ba ni na farka ba, sai da muka shiga Kaduna.
Mun wuni sur! A kan hanya, sallah kadai ke tsaida mu. Sai kuma in mun samu gidan cin abinci mai kyau mu tsaya mu saya. Har Allah ya kawo mu gida Sokoto lafiya.

*** *** ***
Allah sarki Adda! Murnar da ta yi na dawowarmu lafiya tana da yawa.
Bayan kwana uku muka shirya muka raka Aunty Nabeelah Dogondaji wajen dangin mahaifin su, ba mu kwana ba a ranar muka dawo, Aunty Nabeelah ta soma shirin koma wa Beirut.
Ana gobe za su tafi na sha kuka sabida Aasim, Aunty tana ta tsonakata wai ya kamata Addah ta yi min aure in je in haifo mata yaro mu yi ta raino. Addah ta ce, “Mai auren Ma’u ai sai ya shirya, don da sisin gwal za a biya ni sadakinta”.

Washegari Aunty ta koma Lebanon.
Chapter 10 · 0% Book details