← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 33

Sashe 25

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A daren Yaya da kansa ya hada mana gabadaya kayan mu, don ba lallai in mun dawo mu sake sauka a dakin ba. Yaya Maccido ya yi mana shatar lafiyayyar mota, wadda za ta kai mu har Madeenah.
Tafiya zuwa Madeenatul Munawwarah daga birnin Jeddah ba tafiya ce mai sauki ba, mun wuni sur a hanya, sai dai dadin abun akwai mud’ams (gidajen cin abinci) a kan hanya ta yadda matafiyi ba zai jigata ba.
Sai dare muka shiga Madinah, yaya Maccido ya kama mana masauki a hotel din Dar At-Taqwa wanda ke kusa da Masjid Al-Nabawy.
Ba abin da muka iya sai ramuwar barci sabida gajiya, kasancewar mun yi duk sallolin mu a kan hanya, sai asubah muka taka a kafa zuwa masallaci mai alfarma, muka samu sallar asubah. A kan idona aka bude Raudha na kukkutsa yadda kowa ke yi na gabatar da sallar nafila raka'a biyu. Allah ka kara wa Manzonmu darajah da fadhilah da waseelah, ameen.
Kasancewar wajen maza daban na mata daban, ba mu kara haduwa ni da Yaya ba. Sai bayan sallahr azuhur a daki. Ya shigo mana da shinkafa-kaza da juices, laban da haleeb muka ci muka yi kat, sannan ne muka sake wanka muka koma masallaci muka samu sallar la’asar. Karfe hudu da rabi muka koma hotel Yaya ya ce, yanzu za mu kai ziyara ne wurare masu albarka, masu tsohon tarihi a musulunci.
Mun je Masjid Quba, Uhud Mountain, Baqi’a, da Masjidil Qiblatayni, sannan muka je Dar Al-madinah Meseum muka ga kayan tarihi. Washegari kuma Yaya ya kai ni shahararren shagon sutturar nan na manya da yara, wato Majma’al Qimmah. A kokarin Yaya na ganin ya faranta min, na daina kumburi da fushin dana ke yi masa ya ce in sayi duk abin da nake so a shagon.
Da farko na ce bana son komai, daga baya na yi wani tunani. Kayan yara na fara dauka masu kyau da nagarta, mace da namiji, Ahsan da Ihsan na sai wa, sai kuma Aasim din Aunty Nabeelah. Na daukar wa Muhsin jallabiyyu masu kyau da turare irin wadanda na ga Yaya ya saya yana sakawa. Har Al-Qasim na yi wa tsaraba.
Yaya bai san me na debo ba sai da aka zo biyan kudi.
Ya ce, “Duk wadannan uban kayan ina za ki kai su?”
Nan na dan saki fuska nayi masa bayani, don dai in samu ya biya duka, amma ban gaya masa da na Al-Qasim ba, na ga alama ya ji dadi sosai da tsarabar su Ahsan, amma sai ya ce,
“In suka haura kilo din kayan da aka yarje miki ke za ki biya kudin awo ba ruwa na”.
Zumburo baki na yi, na ce masa, "na yarda"

Tun daga ranar ba mu kara zuwa ko’ina ba sai Masjid Nabawy, kowacce sallahr farillah ba ta wuce mu a masallaci. Zaman mu Madinah kadaran-kadahan tsakani na da Yaya Maccido, duk yadda Yaya ya so ya rarrashe ni ya samu kaina mu shirya mu mori amarcin mu kamar yadda ya zo da niyya na ki yarda da hakan, ba na tashi tada bori da kuka na sai dare ya yi, abinda na san Yaya ba ya so ko kadan, kuma yana kokarin kiyaye umarnin Addah da ta ce kada ya sake ya takura min. Sannan da kokarin sa na son nuna min ba dalilin da yasa ya aure ni kenan ba kamar yadda ya fada min a baya. Shi yasa Yaya ya saka min ido na cigaba da yi masa duk abinda naga dama.
Tare da wasu dalilan da dama bayan wadannan, su suka taru suka sa Yaya ya daga min kafa, ya kyale ni bai kara bijiro da neman wani abu da ya danganci aure daga gare ni ba. Duk wani sauke kai da namiji zai iya don ya samu hadin kan matar sa da yake matukar so Yaya Maccido ya yi a Madinah, sai dai ba ya samun martanin komai daga gare ni ko kadan. Banza na ke masa har sai ya gaji ya rabu da ni. Da rana zamu wuni lafiya wataran har 'yar hira ina yarda mu yi, musamman in su Aunty Nabeelah sun bugo waya. Sai dare yayi zaka gane ba masoyan gaske bane, domin kuwa kai da kafa muke kwana, har gobe kallon Yaya Maccido nake matsayin Yaya na yadda yake a baya ba abinda ya canza a idanu na. Kuma na gaya masa, na kara gaya masa ba zan taba son shi ba, so irin na aure, he's never my choice. Balarabe na ke so kuma yaro. Ba zan taba son shi ba.
Tun kalamai na suna baiwa Yaya haushi har sun koma bashi dariya, wani lokacin in muna tafiya a cikin gari, ya ga wani kyakkyawan balaraben sai ya ce
"Asma'u to ko wannan ya yi? Tunda Maccido bashi da sa'a?"
Hararar sa nake kawai in kau da kai, don na lura ya maida ni mahaukaciya.
Daga ni har Yaya mun yi sumul a kwanaki bakwai, kamar da ka taba mu jini zai yi tsartuwa, mun zama wanke hannu ka taba, tabbas kasar Saudiyyah rahma ce ga kowanne musulmi.
Kwanan mu bakwai muka tattaro kayan mu muka dawo Makkah. Wannan karon a hilton na kusa da haraam Yaya ya kama mana karamin daki kwana uku. Muka sake yin umrah muka yi dawafin godiya ga Allah a bisa duk rahamomin da ya yi mana, muka gode maSa lafiyar da ya dube mu Ya baiwa Addah. Muka kara rokon Sa Ya rufa mana asiri duniya da lahira, Ya dawwamar da mu cikin kwanciyar hankali, arziki da zama lafiya.
Mun ziyarci Abraj Al-Bait Towers a Makkah. Kwanan mu uku muka dawo Jeddah, muka samu Addah ta murmure tana harkokin ta kamar bata taba kwanciya ba.
Tun daga ranar da muka dawo na ki bin Yaya mu koma masaukin mu nace ni jinya na zo kuma ita zan yi da Addah zan zauna, Addah bata yi wata-wata ba ta ce Yaya ya kyale mata 'yar ta, dama bata shirya tarewa ta nan kusa ba. Yaya Maccido ya yi fushi sosai ya rabu da ni ko dakin ya shigo baya kula ni balle ya kalli inda nake. Wai kuma sai hakan ya soma sanya ni a damuwa. Duk da haka ban bishi ba, na cigaba da zama na wurin Addah. Nabeelah bata ce komai ba.
Bayan sati daya da dawowar mu muka soma shirin dawowa gida, bayan an baiwa Addah sallama. Da sharadin zuwa check-up bayan watanni shidda. Saura kwana biyu mu taho Aunty Nabeelah ta koma Beirut.
Inda bayan sati biyu za ta tafi Abu-Dhabi ta hado lefena da kayan daki, kamar yadda Yaya ya bata kwangila, sannan ta iske mu a gida da kayan. Adda dai ta ce tarewa ta ba rana ba wata.
Ranar laraba ta shekarar dubu biyu da goma (2010) jirgin Emirate ya dawo da mu gida, ta Abuja muka sauka, da Addah cikin koshin lafiya mu kuma cikin kwanciyar hankali.

**SADAUKARWA GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*

*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*

*07030137870*
*

SOKOTO, NIGERIA.
Mun dawo mun samu gidan tsaf! Hawwa ta gyare ko’ina, Muhsin da Al-qasim su suka dauko mu daga filin jirgi. Muhsin na ta kururuta tsabar canzawar da muka yi daga mu har Addah. Al-Qasim ya canza min bakidaya domin ko gaisuwa ta da kyar ya amsa, sai da Addah ta ce da shi,
“Ana gaishe ka”.
Bayan na tabbata ya ji din.

Abin bai min dadi ba ko kadan, domin akwai sabo a tsakanin mu a baya. Daga baya na ga to me zai dame ni don Al-Qasim ya ki amsa gaisuwa ta? Ai da da yanzu ba daya ba ne. Ni din yanzu matar aure ce ina da special miji na a gefe.
Murmushi na yi wa kai na ni kadai, a rai na na ce "kamar gaske" mijin da ko gaisuwa babu tsakanin mu???
Ni kaina na san ba zan iya cewa bana son Yaya ba, na laluba a fadin kirji na da zuciya ta na rasa space na kiyayyar Maccido, sai dai wani kwantaccen so wanda ban taba sanin da shi ba sai yanzu dana ke da tabbacin ni matar sa ce, domin ba tun yau ba Maccido ke burge ni, na ke yiwa kai na addu'a da fatan samun miji kamar sa.
Baya ga laifin da ya yi min na aure na ba da sani da amincewa ta ba, na kasa manta biris din da yayi da Adda akan mace, duk da ita ta yafe masa suna sabgar su ta Da da uwa kamar da. Sannan wani irin kishi ke nukurkusa ta a kan Maccido, wanda ban taba sanin ina da shi ba, sai yanzu da ya zama miji na na zama matar sa. Kishin Lubabatu! Tunda kuwa ta riga ni mallakar Attahir da komai nasa. Ta riga ni haifa mishi 'ya'ya, shi yasa na tattara kishin hakan da haushin hakan da bacin rai na duka na dora akan Maccidon, ta sigar kafewa akan ni bana son shi ko kadan.
Chapter 25 · 0% Book details