← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 33

Sashe 16

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Girgiza kai na yi hawaye na bilbilowa daga ido na, hawayen da bansan yadda zanyi in tsayar da su ba, me yake so in ce masa? Horon yunwa da ya fara yi min ne ba zan iya dauka ba? Ko kuwa bana son jin ni da shi mun kadaice a wuri guda irin haka, babu mutum na uku a tsakanin mu ban saba ba?
Hawaye na suka kara yawa. Murmushi ya yi, ya dauko ledar KFC ya aje a gabana, da kansa ya bude min ya bincire min hancin gwangwanin fanta.
Ya ce, “In kin yi hakuri ai ba zan ci in hana ki ba, ina magana da Madam dina ne, daga yau kada ki kara fita waje ba tare da ni ba, larabawan nan ba hankali ne da su ba”.
Na kasa cin komai sabida ya tsaya min a ka. Ya gane hakan, amma ya ki matsawa, kallo na yake daga sama har kasa, ka ar yau ya soma gani na a gaban sa, kallon da na tabbatar Yaya Maccido bai taba yi min kwatankwancin sa ba tunda aka haife ni, bai taba yi min kallo na biyu ba, amma yau kallon da yake yi min har ya zarce ka’idar musulunci.
Yanke shawara na yi a raina, gara in shige toilet, don in kubutar da kaina daga wadannan mayatattun idanun na Maccido. Ina mikewa na yi taku biyu sai ji na yi ya fizgo ni na fada jikin sa. Kadan ya rage in saki fitsari sabida razana da tsabar firgita.
Rungume ni sosai Maccido ya yi yana sakin wata irin ajiyar zuciya, abin da ya dauke ni ya shilla wata duniya da ban taba ziyarta ba ke nan. Duniyar da ta fi kama da ta yawo a kan gajimare, domin har bayana yake bubbugawa da hannunsa daya, yayin da ya sarke na hagun cikin nawa. Tunda nake ban taba jin lallausar hannu irin na Maccido ba.
Ganin komai nake kamar cikin mafarki, amma nan take kwakwalwata ta koma cikin hankalin ta. Adda ta sha gaya min, duk namijin da zai nemi taba jiki na, to dan iska ne, kuma ba mutuin kirki ba ne, in guje shi kuma in zo in gaya mata.
Da karfin gaske na janye jiki na daga cikin na Maccido na zura toilet a guje na banko kofar.
A jikin sink na tsaya ina regaining consciousness tare da hango abin da ya faru cikin dakikar da ba ta wuce goma ba. Ni ce rungume jikin Yaya Maccido ba mafarki na yi ba, al’amarin mai kama da almara ya faru da gaske. Kamshin turaren da jiki na ya koma yi na obsession (by CK) ya kara tabbatar min da hakan.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Na ambata har sau uku. Da ma malamin islamiyyar mu ya ce, “Idan mace da namiji suka kebe, to tabbas shaidan ne na ukun su”. Wato don ya ga babu idon kowa a kan mu shi ne zai aikata wannan zaluncin a gare ni? Zan kuwa ba shi mamaki, duk girman sa da ke idanuna wanda da ma yanzu rawa yake, sabida tsanar dana yi masa akan laifuffukan sa ga Addah zan yakice shi in nuna masa na san abin da nake yi, kuma na san mutuncin kaina. Ina masa kallon mutumin kirki ashe shi ma in ya samu faraga dan duniya ne?
Ina jin bude kofar sa da fitar sa, na wanke fuskata a sink na fito. Kazar na dauka na gyara zama na afka mata babu sassauci. Addah na wani daki na musamman suna kula da ita, sai dare suka turo ta bisa gado zuwa dakin mu suka kwantar da ita a kan gado. Da alama ta sha alluran barci don barci ta ke yi sadidan.
Ban kara ganin Yaya Maccido ba sai karfe tara na dare agogonsu na can. Ya canza kayan jikin sa, da alama wanka ya yi. Ina daidai kan Addah rike da hannun ta sanda ya shigo, ledojin hannun sa ya ajiye ya karaso inda muke. Na kuwa tattare fuska na hade girar sama da ta kasa.
“Ba ta tashi ba?” Ya tambaye ni.
Juyar da fuska na yi wani gefen ban ce masa komai ba.
Ya ja kujera ya zauna a gaban Addah yana karanto addu’o’i yana tofa mata.
“Ga abinci can ki je ki ci”.
“Na koshi”. Na yi saurin bada amsa.
Ya daga fararen idanunsa ya kalle ni, kallon sakan biyu, kafin ya ce cikin muryar bada umarni.
“Asma’u, na ce ki je ki ci abinci”.
Sai na samu kaina da kasa musawa wannan karon, domin ya murde fuska ya koma Maccidon sa da na sani.
Shinkafa ce da gasasshiyar qibdah (hanta), na zauna na soma ci ba don yunwa ba, sai don bana son wata magana kowace iri ce ta sake hada ni da Maccido.
Wayar sa ce ta yi kara, sai ya dauka ya yi magana, sai na ga ya kalle ni ya wani bata rai, kafin ya ce, “Zo ki karba”.
Na tsame hannuna daga cikin abincin na je na amshi wayar na kara a kunnena. Aunty Nabeelah ce.
“Hello Ma’u, ya ku ka sauka, ya kuma jikin Addah?”
Na ce, “Aunty lafiya kalau. Addah dai tunda muka zo suke mata allurar barci wai sai jibi za a yi aikin”.
Ta ce, “Ina nan ina shirin tahowa, sai nan da kwana shidda. Ki yi hakuri da Maccido kin ji?”
Dan murmushi na yi, na ce, “Aunty ke ma kin san ba wani shiri muke ba, me ya sa aka hado ni da shi, bayan ga Muhsin?”
Aunty Nabeelah ta yi ajiyar zuciyar da na jiyo ta, ta ce, “Sabida shi ne babba. Abin da zai yi Muhsin ba zai iya ba. Sannan kin ga yana so ya yi amfani da damar ya yi repenting kurakuran sa ne. Ya kula da mahaifiyar sa. Alhamdulillah tunda mun samu Allah ya juyo mana da hankalin sa sai mu ba shi dama. Shi ma ya samu ladan mahaifiyar sa da yake ta batawa. Kin ga dukkan ayyukan da ke gabansa ya ajiye su ya taho, kuma za ku kwashe a kalla wata guda bayan aikin Addah kamar yadda likitocin suka ce.
Ke dai tsakaninki da shi ai gaisuwa ce, sai kuma ki yi masa biyayya tunda gaba yake da ke”.
Na so in ce, “Aunty dazu ba rungume ni ya yi ba… kuma hakan haramun ne”. Amma ina dago idanuna na dubi saitin da yake, sai na ga ya kafe ni da ido yana min kallon mind yourself. Kafin ma in yi magana Aunty Nabeelah ta ce, “Baban Aasim ya shigo, zan kira ki gobe insha Allahu”.

**SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
*

*YIWA KAI HISABI*
Chapter 16 · 0% Book details