← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 33

Sashe 31

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai albarka irin wannan ba.
Da daddare ne mutanen Bebeji matar Malam Ayuba, wato Inna Kubra da mutanen Babura su biyu da aminiyar Adda Hajiya Wasila suka raka ni dakina. Ina kuka sosai kamar ba cikin gidan za a bar ni ba. Addah don farin ciki sai hawaye ta ke yi, ta shige kuryar dakin ta ta yi wa Allah sujjada da ya nuna mata wannan rana. Wani dadadden buri da ta ke da shi, amma ba ta taba furtawa ba don tabbacin rashin yuwuwar sa. Yau ga Ubangiji kunfa-yakun ya ba cika mata burin ta wanda ba ta taba daga hannu akai da nufin rokon shi ba. Sai dai ta ce ya zaba mafi alkhairi.
Kowa ya watse ya bar ni ni kadai, da ma ni ba gwanar kawaye ba. Kuma ba lafiya ce ta ishe ni ba. Zazzabin ma kara zafi yake yi. Na kira Aunty a waya na roke ta ta ba ni Aasim mu kwana tare.
Ta ce, “A’ah ba zai yiwu ba, in koyi zaman gidan miji ni kadai, kuma sun yi waya da Yaya Maccido yana kan hanya, sai dai zai kai goma na dare bai iso ba”.
Gaba na ne naji ya yi wani mugun faduwa babu dalili, kamar yau zan fara ganin Maccidon. A daddafe na yi sallar isha, ko shafa’i da wutri na kasa yi sabida yadda jikina lokaci daya ya rikice.
Wayata na dauko na kira Aunty Nabeelah cikin muryar rashin lafiya, na ce, “Aunty ki zo, saura kadan na mutu”.
Ta ce, “Assha! Bar kira wa kanki mutuwa, ba ku gama cikawa Adda daki da ‘ya’yan da ku ka yi mata alkawari ba. Sannu kin ji, stress ne kawai da fargabar da kika sa wa ran ki”.
Kafin minti biyar sai ga ta ta shigo da gorar ruwa da kwayar magani, ta ba ni na sha, ta ce in kwanta in yi isasshen barci zuwa gobe zan ji garau.
Sai da na kwanta ta rufe ni da quilt, sannan ta juya ta fita.
Lokacin da Yaya Maccido ya iso na yi nisa a barci na, tun a cikin gida Aunty ta gaya masa ya kula da ni bana jin dadi, amma dai ta ba ni magani na ji sauki har na yi barci. With concern ya ce, “Ko asibiti za mu je?”
“Ba sai kun je a daren nan ba, kuna iya bari sai Monday ma in raka ta bayan ka tafi, na tabbata zata ji sauki zuwa gobe stress ne da fargabar aure.
"Fargabar aure?" Yaya ya tambaya.
Murmushi ta yi ta ce "normally 'yammata suna yin hakan in za'a musu aure, ita bata san za'a mata auren ba sai yanzu take nata fargaban".
Sanda Yaya ya shigo ban sani ba, ya kulle ko’ina, ya saki curtains ya je dakinsa ya yi wanka yana yaba yadda gidan ya koma cikin ransa. Ya san duka aikin Nabeelah ne, akwai ta da iya style, ga iya zaben abu mai kyau.
Sai da ya kimtsa tsaf shirin barci ya fesa turaren sa obsession bisa pajamas din shi, ango sosai, sannan ya nufo nawa dakin, bayan ya kashe wutar falo.
A hankali ya zauna a gefen gadon daidai kaina, yana kallon yadda nake barci cikin nutsuwa, numfashina na sauka a hankali. Ya dora hannu saman goshina da wuyana ya ji temperature din ya sauka. Ina jin sa ya russuna ya sumbaci baki na softly, da murmushi ya ce “sleeping beauty”. Tare da gyara min quilt din da nake rufe da shi, ya yi light off ya shige cikin quilt din shi ma ya kwanta, ya jawo ni a hankali ya shigar cikin jikin sa, hancin sa yana daidai tsakiyar gashin kaina. A haka muka yi barci, wani barci mai dadin da ban taba irinsa ba. Ya nemi fushin da yake ta yi ya rasa, tunda finally Adda ta yi masa abinda ya ke so ta bashi Ma'un sa.
Da asubah bayan mun yi sallah Yaya bai yi la’akari da halin da nake ciki ba. Da lallashi, da ban baki da zakakan kalamai ya samu abin da yake so, ya karbe budurci na cikin girma da daraja, komai ya faru very soft and gentle, he didn't hurt me anymore, ya yi ta sa min albarka. Ba yadda bai yi ba mu je asibiti a washegari ganin yadda na galabaita amma na ki. Ragowar kwanaki biyun da yayi ba abinda yake yi sai jinya ta, hatta Adda da Aunty Nabeelah tarairayata suke ta yi, Adda da abinici mai gina jiki Nabeelah da shigowa akai-akai tana duba halin da nake ciki da tabbatar da na sha magani.
Kwanansa uku ya koma ba don ya so ba, da niyyar yau yana komawa zai gaya wa Lubabatu auren sa, kada sai na haihu sannan ta sani, ya kara wani laifin.
****
Ba laifi ya samu tarba daidai gwargwado daga Madam din tasa, amma ‘ya’yan sa sun fi murnar dawowar sa. Bai damu ba don ya san haka take canza fuska duk lokacin da ya je Sokoton da yake zuwa yanzu akai-akai. Ya daga Ahsan yana sumbatar sa, yaron ya shiga ransa sosai sabida kamannin shi da ke ga yaron. Suna cin abinci, wanda ta sa mai aikinta ta yi masa, ta ce,
“Na ga wasu kayan yara msu kyau a cikin kayanka, a ina ka saya musu?”
Ya dan dube ta yana son tuno wane kaya ne? Lokaci daya zuciyar sa ta hasko masa Ma’u a shagon Majma’al Qimmah. Tana zabowa Ihsan da Ahsan kaya. Wani ni'imtaccen murmushi ya yi wanda bai san ya yi ba, sannan ya sosa kansa yana ta murmushin dai ya ce.
“Nasu ne”.
"Wa ya ba su? Gaskiya ko waye ya iya zaben kayan yara, i'm sure ba kai ka zabo ba”.
Ya sake sakin murmushi, ya ce, "Ko? Ashe ni ma na iya zabi?”
Ba ta gane me yake nufi ba, ta ci gaba da cin abincin ta. Sai da suka kammala ya dauko wayar sa yana danne-danne. Ba jimawa Lubabatu ta karbi alert din kudi masu yawan da bai taba ba ta kamar su ba. Da mamaki ta dago tana masa murmushi.
“Sweetie, wannan kyauta haka? Lallai an bude sabuwar plaza da kafar dama, sai kawai in sayar da motata in cika in sayi latest model.
Yana mamakin ta ya ce, “Ba kya tambayar ko na mene ne kawai daga ganin kudi ba neman karin bayani sai kashewa?”
Ta ce, “Bayanin me zan nema? Na san dai ba mistake ka yi ba”.
Ya gyada kai, “Eh ba mistake na yi ba, naki ne, na fadar kishiya ne, ki sayi duk abin da ki ke so, na ga ya fi in sayo miki kaya tunda ba kya rabo da dinkin sabon kaya”.
Lubabatu ta yi tsai da iadanunta tana duban shi, sai da ya yi shiru sannan ta ce, “Attahir, me ka ke fada ne? Kamar kishiya fa ka ce?” With affirmation ya gyada mata kansa,
“Eh na yi aure Lubabatu, kusan wata uku da suka wuce”.
Lubabatu ta yamutsa fuska, ta ce, “Idan wasa ka ke ka bari, bana son irin wannan wasan ka sani”.
Ya dauko wayarsa ya shiga lalube a gallery har ya budo hoton da yake so ya tura mata wayar gaban ta.
Da farko kamar ba za ta dauka ba, sai kuma ta sanya hannu ta dauka.
Hotonsa ne shi da Ma’u, selfie ne ya dauke su a Hilton na makka, hannayensa zagaye da wuyanta, fuskokin su na nuna irin farin cikin da suke ciki, sannan akwai alamun soyayyar da ke cikin idanun Attahir dadaddiyar ajiya ce, wato ba ta yau ba ce.
Chapter 31 · 0% Book details