Sashe 22
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali ba tare da sun ankara ba na dinga ja da baya a hankali, har na bude kofa na fice daga dakin.
Da sauri-sauri nake tafiya a gefen titi bana ko ganin gabana, ina tafe ina kuka da hawaye shabe-shabe ban damu in share ba. Ban damu da kallon da mutane suke min ba. Ni na ce ina son Yaya Maccido? Ko kuwa shi ke nan don ya maida ni kaza yana neman hanyar shiryawa da mahaifiyar shi sai ya kare a kaina? Ni me zan ci da mai mata da ‘ya’ya? Allah na tuba kuma mijin Lubabatu? In rasa wanda zan aura in auren zan yi sai ragowar wata? Ai wallahi ko auren zan yi ni ma sai dai na auri yaro, kuma balarabe irin na Aunty Nabeelah… mijina ni ni kadai, ba mijin wata ba. Ban da karya mai mace kamar Lubabatu, me zai ci da ni, in ba yaudara da rainin hankali ba???
Tunanin da nake ta yi ke nan ina tafe ina gursheken kuka, ban ankara ba na ga wata farar ajrah ta sha gabana, saura kadan ta take kafafu na.
Yaya Maccido da Nabeelah ne suka bude kofofin motar suka fito suka sha gabana, na dage riga ta zan taka da gudu, Maccido ya damke ni.
"Ke kina da hankali kuwa? Ko kin dauka a Nigeria ki ke?”
“Daga turu na fito”. Na fada cikin karajin kuka ina fiffizgewa daga hannun sa.
Aunty Nabeelah cikin mamaki ta ce,
“Ma’u ba za ki nutsu ba? Kina so ki jawo mana jami’an tsaro ne?”
Hararar ta na yi da jikakkun idanuna, na ce, “Ai komai ke ce sila, kin bi bayan kanin ki kun zalunce ni, ni na ce miki ina son shi? Akalla a ba ni hakki na na dan Adam a tuntube ni kafin a daura min aure? Ko kuwa don shi shi ne shafaffe da mai, ya gama yi wa Adda cin kashin sa sannan ya zo ya yi abin da yake so a kaina?”
Ji ka ke taaas! Yaya Maccido ya dauke ni da wani lafiyayyen mari. Na sa hannu na dafe kunci na ina jin kamar fatar fuskata ta daye.
“Ashe ba ki da kunya? Auntyn ki ke gaya wa haka? An aure ki ba da sanin nakin ba, don Allah ki je ki maka ni a kotu a fidda miki hakkin naki”.
Na rushe da kuka.
“Don an ga ni marainiya ce ba uwa ba uba… wayyo Nene, wayyo Baba…...”.
Yaya Maccido bai tsaya sauraro na ba da kwarmaton da nake yi, don har na fara tara musu mutane, ya danna ni a motar da suka zo, Aunty ta shigo mai motar ya ja. Na ga za a wuce asibiti ba su shiga ba na kara rusa kuka.
"Ni ku sauke ni wajen Addah, babu ni babu ku. Ai ba zaman ku nake ba”.
Aunty dai kallona kawai ta ke tana mamaki, in wani ya ce mata ni ce wannan ba idanun ta ne ya gane mata ba, lallai za ta musa. Ashe haka nake??
Hotel din mu muka nufa, Aunty Nabeelah ta kama hannuna muka fito har zuwa lokacin kuka nake yi wurjanjan. A reception muka jira Yaya Maccido ya je ya kama wa Aunty daki ya dawo muka rankaya ta cikin lifter zuwa sama.
Ya bude dakin muka shiga dukkan mu, Aunty ta zaunar da ni a gefen gado. Ta zauna kusa da ni, yayin da Yaya ya tafi kujera ya zauna. Ta kira sunana a tausashe,
“Asma’u!”.
Ban amsa ba, amma na dago na kalle ta da rinannun idanu na da suka kada suka yi jajawur.
“Kina so ki mayar da farin cikin Adda bakin ciki?”
Da sauri na girgiza kai ta ce, “To why this? In kin bi komai a hankali ai ni mai yi miki duk abin da ki ke so ce. Maccido bai isa ya shiga tsakanin mu ba, ki kwantar da hankalin ki, ki gaya min duk abin da ki ke so na yi miki alkawarin in bai fi karfin iko na ba zan yi miki”.
Ai jin haka na ce, “Aunty kawai ki ce masa ya sake ni, wallahi bana son shi!”.
Aunty tana hadiye dariyar da ta zo mata ganin Yaya Maccido ya yi tsumuu! Ta ce, “Saboda me ba kya son nasa?”
Babu ko kunya na ce, “Ni me zan yi da shi? Mutumin da matar sa da ‘ya’yan sa watakila ma ya fara furfura”.
Duk yadda Aunty ke hadiye dariyar ta sai da ta sake ta wannan karon. Ni kuwa na ci magani, don zuciya ta daya nake magana, ta daura hannunta bisa nawa ta ce,
“Ma’u ba kyau cin fuskar miji fa!”.
Na zumburo baki na ce, “Kada ki kara cewa miji na, mijin Lubabatu dai, ni me zan ci da shi? Wallahi Balarabe nake so irin naki”.
Da sauri yaya Maccido ya mike ya bar dakin, fuskar sa kamar hadarin da ya nausa ya yi gabas. Aunty Nabeelah ta dinga kyalkyala dariya, ta ma rasa me za ta ce mini. Na mike ina fadin,
“Aunty tashi raka ni dakin sa in kwaso kayana, da ma kamar a kan kaya nake zaune a dakin. Don ya raina min hankali ya ce ba shi da kudin kama daki biyu, ina ya samo na wanda ya kama wannan?”
Aunty ta ce, “Um-umh Ma’u, an dai gama shan soyayya shi ne don an gan ni za a wani ce za'a kwaso kaya? To ba da ni ba, ba ruwana”.
Kuka na sa mata da karfi ina fadin, “Ni wallahi babu soyayyar da mukai, kullum fada muke yi! Kuma ba gado daya muke kwana ba”.
Ta ce, “Fadan soyayya ba?”
Na ce, “Wallahi na kiyayya”.
Aunty ta koma serious ta ce, “Ma’u, ki nutsu mu yi maganar fahimta. Maccido yanzu ko kin ki ko kin so mijin ki ne, duk kuma abin da ki ka yi masa na kyautatawa ko akasin ta, mala’iku suna rubutawa. Don haka ki shiga hankalin ki, in ke wata mai wayo ce wannan tafiyar dama ce ki ka samu da za ki mori mijin ki ke kadai, ki shiga jikin sa, ki mantar da shi kowacce diya mace. Amma don sakarci har kin fara zancen a raba daki. Ma’u miji ne Allah ya kashe ya ba ki daga sama don haka kar ki yi wa Allah butulci. Wallahil azeem Maccido na son ki, sai da na shaidi wannan kafin in yarda in shige masa gaba ga auren ki. Ga shi dan uwan ki, wanda ya san ciwon ki, ya san mutuncin iyayen ki. Na miki alkawarin muddin ina raye ba za ki taba da na sanin auren Maccido ba.
Ma’u ba kya jin tausayin Addah? Ba za ki so ki zama tsanin da Dan ta zai dawo gare ta ba? Ki haifa mata jikoki ki bata ta raina a daina yi mata rowar ‘ya’yan Maccido? Ma’u in ba ki yi wa Addah wannan aikin ba, wa zai yi mata shi da zuciya daya?”
Jiki na ya dan yi sanyi da kalaman Aunty Nabeela. Amma hakan ba zai taba sawa in karbi wannan auren ba. Ta dora hannu a kan kafadata ta ja ni jikin ta a hankali cikin sigar rarrashi.
“Maccido abun tausayi ne Ma’u, saura kadan mace ta kai shi wuta. Ki zama mai aikin jihadin ceton soyayyar uwa da Da. Ba ruwan ki da matar sa, tana Abuja kina Sokoto, me zai dame ki da ita?”
Zuwa wannan lokacin Aunty Nabeelah ta dan kashe min jiki. Abin da na ki yarda da shi har yanzu shi ne Maccido na so na. Zan yi kokari in gane hakan da kaina komai daren dadewa kafin in yarda da hasashen Aunty Nabeelah.
Ta mike ta ce, “Ban zo don in rashe ba, na zo ne don in karbe ki jinya, ke kuma ki yi amarci yadda ya kamata. Mu je toilet da kaina zan yi miki dilka da halawa, sannan in yi miki wankan turaren da na zo da shi takanas, sabida ke”.
Duk abin da ta fada din kuwa sai da ta yi min. Ina kumburi ina komai sai kara kwantar min da hankali ta ke yi da tausasan kalami da misalai kala-kala. Ta dauko wasu tablets masu kama da magungunan supplement ta ba ni, ta ce in hadiye su. Sai da ta tsaya a kaina ta mika min ruwa, ta tabbatar na hadiye din. Ta bude jakarta ta fiddo wani lallausan swiss lace da aka yi wa dinki senegalese ta ce su zan sanya, sannan ta sake feshe ni da turare ta yi min daurin kai very cute da shi. Ta ja baya ta kalle ni sosai ta ce,
"saura light make up".
Dan karamin akwatin kwalliya ta dauko a kayanta ta zaunar da ni a gabanta ta yi min sassaukan make-up. Albarka ta shiga sanya min kamar wata uwa ta sannan ta kama hannu na bayan ta rufa min babban gyale kalar adon leshin ta kira wayar hannun ta.
“Kana ina Maccido?".
A kasalance ya ba ta amsa,
“Ina daki, kaina ke ciwo, sai dare zan maida ku wajen Addah din, may be kafin nan na samu kan ya sarara min”.
“Nawa ne lambar dakin naku?”
“104”.
Daga haka ta maida wayar jakar ta, ta kama hannuna muka fita.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
Ta lifter muka bi zuwa kofar dakin. Ni dai kallon komai nake kamar a majigi. Majigin ma na cikin mafarki. Wai yau ni ce Aunty Nabeelah zata kai dakin miji. Mijin kuma Maccido, Maccidon ma wanda na sani, na yi wa farin sani, wanda a baya ban taba mafarkin wata alaka a tsakanin mu bayan gaisuwa ba.
To shi sha’anin Ubangiji haka ya ke. Matar mutum kabarin sa, ashe Allah ya riga ya rubuta min Attahir a matsayin miji, babu makawar hakan komai daren dadewa.