Sashe 11
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar wata lahadi na dawo Tahfiz na ga wata bakuwar tsaleliyar mota a kofar gidan mu. Sai sheki da daukar ido take yi. Wannan ya tabbatar min baki ne muka yi. Ban bi ta falo ba ta kofar kicin na bi zuwa daki na na cire hijab na canza kayan jiki na daga uniform zuwa na gida, na kishingida ina hutawa kafin lokacin sallar magriba ya yi.
Kukan jariri na ji duk ya cika gidan, ba shiri na zabura na fito don tantance daga inda nake jin kukan. A daidai kofar shiga falon muka gabza karo saura kadan na fadi, na yi saurin kama marikin kofa. A hankali na cira kai don ganin da wa na gabza karo, idanuna suka sauka a kan Yaya Maccido. Yana sanye da wata danyar shadda milk colour wadda aka yi wa aiki da zare ruwan kasa turarre, kansa da hula ita ma ruwan kasar ce. Ba laifi wanan karon ya dan yi haske, amma ramar sa tana nan, kuma kyawun halittar sa koyaushe kamar karuwa yake. Kallon sa na tsaya yi na kasa cewa komai. It’s exactly one year rabon sa da gidan nan, don haka zuwan na shi ya dan sa ni a kokonton anya shi ne?
Tsaki ya yi ya wuce yana fadin, “Be careful in kina tafiya mana!”.
Wani irin lumshe ido na yi wanda ban san lokacin da na yi shi ba. Kamshin turaren Yaya Maccido da nake matukar so har cikin tsokar zuciyata. Ina nan tsaye na kasa tabuka komai, Addah ta fito za ta wuce ta same ni a wurin a tsaye.
“Me ki ke yi tsaye a bakin kofa? Ki shiga mana? Kin yi ‘ya, tun dazu suka sauka”.
“Adda, waye ya haihu?”
Ta ce, “Lubabatu”.
Da hanzari na na fada falon Adda, ido na ya sauka a kan Aunty Lubabatu rungume da jaririyar ta. Ta sha kwalliya kamar wata matar gwamna ba matar Maccido ba. Tana gani na ta sha bula. Na karasa da farin ciki na ina fadin.
“Aunty sannun ku da zuwa, ba ni babyn in gan ta”.
Kamar ba za ta bayar ba, sai kuma ga Yaya Maccido ya sako kai falon, sai ta miko min ita. Na zauna a gefe rike da cute jaririyar ina ta kallon ta. Tsabar farin ciki na manta cewa Yaya Maccido ba abokin hira ta ba ne, amma ban san sanda na ce,
“Wallahi Yaya da kai baby ta ke kama, komai da komai”.
Zan iya cewa, wannan ne karo na farko da Yaya Maccido ya yi min murmushi a duniya, tare da cewa, “Ni kuma tun sanda aka haife ta da ke ta ke yi min kama, musamman hancin ku”.
Na washe baki, dadi kashe ni!.
Aunty lubabatu ta balla min harara, shi ma ta balla masa tasa, ta ce, “Allah ya sauwake. Ni ‘ya ta ba ta kama da kowa daga uwar ta sai uban ta”.
Fuskar Yaya Maccido ta muzanta da kalaman Lubabatu, amma bai ce komai ba, ni kuma uwar ‘yan kankanba na mike zan tafi da baby daki na. Da sauri Aunty Lubabatu ta ce, “Kawo ta…”.
Yaya ya dago kai daga kan wayar sa ya dan dube ni, ya ce,
“Je ki da ita, in ta yi kuka kya kawo ta…”.
Ai kafin ya rufe baki na yi waje, rungume da baby, ina ji Yaya na fadin.
“Wannan abin da ki ke yi Lubabatu ba daidai ba ne. Kanwata ce fa!”
Duk da ban kalle ta ba na san gatsine da kyabe bakin da na lura tun zuwan mu gidan ta dabi’ar ta ce ta yi. Ta ce,
“Ai fa na ga Muhsin ne ya sha nono ya sakar mata. Ni irin wadannan jajibe-jajiben dangin bana yarda da su. Gara ma ka canza mata suna daga kanwar ka zuwa dangin-dangaro".
Da sauri na karasa ficewa ban san amsar da Yaya Maccido ya ba ta ba. Na wuce ta kicin inda Addah ta tsaya tare da Hawwa mai aikinta suna hada wa su Yaya abinci. Adda ta dube ni ta ce, “Taufa! An yi ‘ya yau raino sai inda mai ya kare”.
Dariya na yi na wuce zuwa daki na ina ta lelen ‘ya ta. Ji nake kamar ni na haife ta. Kuma wani ikon Allah sama da wajen awanni biyu ba ta yi min kuka ba sai baccinta ta ke a gado na. Kafin uwar ta ta biyo sawunta ta amshe abar ta wai za ta ba ta nono.
A bakin Adda na ji sunan yarinyar Ihsan. An ce tsakanin Da da mahaifi sai Allah, wannan haka yake, duk laifin nan da Yaya Maccido ya yi wa Addah farin cikin ganinsa da na haihuwar Ihsan ya shafe komai. Sai nan-nan ta ke da su, ta ce min sati biyu za su yi. Ni da Hawwa ne muka je muka gyara ko’ina na sassan Yaya Maccido muka shigar musu da kayan su da duk abin da za su bukata.
A zaman nan nasu na sati biyu na aikatu sosai da hidimar abincin su da rainon Ihsan. Uwar ta na yakice ni, tana min kora da hali, tana nesan ta ni da ‘yar ta, amma ni din kamar mayya na like wa Ihsan. Ko ba komai yarinyar jini na ce, kuma son yara a jini na yake, shi ya sa sam bana damuwa da wulakancin Lubabatu, har wankin kayan Ihsan ni nake yi in shanya, in sun bushe in kwashe in shigar mata da su. Canza mata diaper akai-akai da yawan ba ta ruwan zam-zam da Adda ta ce a dinga ba ta, duk da uwar ta bata so a bata ruwa..
Suna gama sati biyun su suka hada inasu-inasu suka koma Abuja. Dama kamar akan kaya suke. Gidan mu ya koma yadda yake, don kewar yarinyar komawa na yi kamar an yi min mutuwa. Muhsin ya yi ta tsokana ta, wai in rabu da Adda mu yi auren mu, mu haifo namu a daina yi mana kwalele da ‘ya’yan mutane.
Na ci gaba da zuwa makaranta da Tahfiz da yamma. Daga aji biyar Muhsin ya bar sakandire, ya zana Waec da jamb, kuma cikin ikon Allah ya haye. Ya samu gurbin karatu a jami’ar DanFodiyo inda zai yi nazarin tsimi da tanadi (Economics).
Ni kuma a sannan na shiga aji shidda da kyar da sudin ludayi. A wannan lokacin makerin budurci ya gama kera ni. Na zama budurwa sosai, amma ba ni da cika ido, ga ni nan ‘yar daidai, komai nawa ya yi daidai da inda Ubangiji ya halicce shi. Ni kaina na san babu ni a jerin kyawawan mata, amma ina kokarin gyara kaina irin na ‘yammatan da suka san ciwon kan su.
Addah kan ce, kwarai na ke da tsafta kamar Nabeelah, kuma kamanni na da Nene yanzu sun fi na baya fitowa sosai.
Tun zuwan su Yaya Maccido lokacin haihuwar Ihsan da komawar su ba mu kara jin duriyar su ba. Adda na lissafe da watanni daidai har guda goma sha biyar.
Da farko yana kokarin kiran waya lokaci-lokaci ya gaishe ta har ya kanga mata gwalantun Ihsan a wayar, amma daga baya wayar ma ta gagara.
Lubabatu kuwa ba ta taba kiran Addah ba ko don gaisuwa tun auren ta da Yaya. A yadda take-taken ta ya nuna shi ne, ita irin matan nan ce wadanda in sun auri namiji shi kadai suka aura. Ba ruwan su da kowa nasa including wadanda suka yi silar zuwan shi duniya.
Amma duk da haka yana kula da MACCIDO MALL daga can inda yake, lokacin da Muhsin ya samu gurbin karatu a Danfodiyo abubuwan za su yi masa yawa, don haka ya nemi Yayan da ya nemo masa mataimaki amintacce, wanda zai iya handling dukkan ayyukansa na manager.
Akwai wani abokin yaya da suka yi karatun sakandire tare da ya biyo ta hannunsa yana so Yayan ya samar masa aiki tun da jimawa. A wannan lokacin sai ya nemo shi. Bayan dogon bincike da amincewa juna dukkanin su, ya yarda zai zama mataimakin Muhsin.
Al-Qasim Ka’oje ke nan, wanda shigowarsa cikin harkar mall ba mall din kadai ya taimakawa ba. A sannu ya shiga ran Addah sabida hankalin sa da nutsuwar sa. Ga shi da biyayya kamar ita ta haife shi, sai ya shigo sosai cikin harkokin gidan mu yake taimakawa ta kowanne fanni, sannan ya zama tamkar wakilin Yaya Maccido wajen harkokin cikin gida, da kula da gidan don Muhsin yanzu ta kansa yake a jami'a. Shi Al-qasim yana yawan kiran Yaya Maccido su yi magana, ba ya jira sai Yayan ya neme shi, duk abin da ake ciki a kan harkar kasuwancin da abin da Adda ke bukata yana kokari ya ga ya sanar da shi tunda ganin sa yanzu ya gagare mu.
Al-qasim shi yake kai Adda asibiti yanzu sakamakon ciwon sugar da hawan jini da ya same ta rana daya. Yawanci in zai kai ta ganin likita da safe suke zuwa, lokacin ni ina makaranta. Har cefanen wata na gidan Al-Qasim ke yo wa, wataran a aljihunsa yake sayo abubuwa ya kawo, musamman fruits, mutum ne shi mai yawan ALHERI sosai, ga shi da ilmi don Muhsin ya ce min masters gare shi, kuma a yanzu haka yana karatu part-time na PhD dinsa a Open University.
Tun shigowar Al-Qasim al’amuran gidanmu abubuwa da yawa suka gyaru mana, matsaloli da yawa suka kau. Addah kullum ce min ta ke,
“Na yi dan da ya maye min gurbin Maccido!”.
Ni haka kawai ban cika sakewa ba idan yana gidan. Ya cika kallo, ni kuma bana son kallo. Daga baya na lura ni kadai yake yawaita kallon. Wannan abu na matukar kular da ni, a kan me zai maida ni dubarudu ba dama in zauna sai ya debi lunkuma-lunkuman idanun sa ya yi ta lafta mini yana maida ni unease?
Rannan na yi wa Adda korafi.
“Wannan dan naki ya cika kallo wallahi”.
Adda sai cewa ta yi,
“Ke da wane idon ki ka kalle shi, har ki ka san ya cika kallo?”