← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 33

Sashe 29

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Maccido-Tahir ba shi ya iso ba sai gefen magriba, ya shigo a gajiye likis rataye da babbar rigar sa da wayoyin sa biyu a hannun sa. Tun da naji muryar sa na kule a uwar dakin Adda amma har can sassanyan masculine turaren sa obsession ya bi ni yana sanar da ni zuwan sa. Duk abin da suke fadi shi da Adda ina ji, hirar iyalin sa suke yi da hirar 'Maccido Mall' na Abuja da plaza din sa. Yana gaya mata irin nasarorin da ake ta samu da kalubalen da suke fuskanta. Ko motsi na Maccido bai ji a gidan nan ba don haka sai zuba ido yake yi don ganin ta inda zan bullo, amma ya yi kawaici bai tambayi Adda ba har lokacin sallah yayi duk suka tashi daga hirar, ya fita masallaci Adda kuma ta shigo dakin don ta daura alwalla a toilet din ta da ke cikin dakin.
Nan ta same ni a kwance bisa gadon ta, ta ce "amma Ma'u an yi shashasha, yanzu mijin na ki ya kamo hanya tun daga Abuja har Sokoto saboda ke, shine kika buya uwar daki? To abincin wa zai kai masa?" Na mike daga kwanciyar na ce "Adda ni ba waje na ya zo ba fa, abincin yana dining na ajiye tun dazu" Adda ta ce "wannan kandararren girkin naki? Maccido ba zai ci shi ba, gara ki je ki dumama masa a microwave, na tabbata a haka kika ajiye shi" na fita ina fadin "toh Adda zan dumama, amma sai na yi sallah".
Da na idar da sallah na kwashe abincin nayi kitchen na kunna na'urar dumama abinci, ba jimawa na gama na mayar dining. Ina kokarin barin bangaren cin abincin Yaya Maccido ya shigo falon.
Wata irin kunya ce ta kama ni kamar in narke a gun, kamar yau na fara ganin Maccido, na yi kasa da kai, ban san yaushe Yaya ya tako ya iso gaba na ba. Ratar da ke tsakanin mu bai fi taku biyu ba. Ya kira suna na a hankali "Asma'u" amma na kasa dagowa. Hannu ya sa ya dago haba ta ban san sanda na rufe idanu na ba.
"Me zan samu Asma'u ga ni na zo? Kin sani kuma sabida ke na zo? Ina alkawarin mu?"
Motsin kofa muka ji duk muka juya a tare, Al-Qasim ne ya shigo da sauri ya koma yana fadin "excuse me please......". Yaya ya yi murmushi ya ja hannu na muka bar falon zuwa daki na. Rufe kofar yayi da mukullin dake jikin ta ya ja ni muka zauna a gefen gado na. Ni dai iya abinda zan iya tantancewa kenan sai tsintar kaina nayi a hannun Yaya Maccido yana sarrafa ni duk ta yadda ya ke so. Al'amuran na Yaya sai gaba suke yi suna kara rikita duk wata nutsuwa da na mallaka. Kwata-kwata ya manta a inda muke waje ne da kowanne lokaci Adda ke iya shigowa. Ilai kuwa ba'a jima ba Adda ta soma kwankwasa kofar dakin tana kiran suna na. Ba karamin rudewa nayi ba na kwace kai na daga hannun Yaya. A hankali ya ce "relax Asma'u, Adda ta san kina tare da mijin ki ne, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki" Ina! Mikewa na yi jiki na rawa har sai da na baiwa Maccido dariya. Da gudu na shige toilet don bazan iya facing Adda ba despite all those hot kisses daga Dan ta Maccido. Gani na ke kamar da ta ganni zata hango abinda ya faru. Shi kuwa Yayan kansa tsaye ya karasa ya bude kofar.
Hararar sa Adda ta yi sannan ta ce "turomin Ma'un" daga haka ta bar bakin kofar.
Da kuka na fito ina fadin "Yaya me yasa ka shigo min daki? Yanzu da wane ido zan dubi Adda?" Dariya sosai na bashi ya kwaikwayi murya ta ya ce "da idon da kika sanya mata Da a daki kina ta sumbata" na kara rushewa da kuka, Yaya ya janyo ni a hankali ya sanya cikin jikin sa, ya lullube ni da tsayi da fadin sa. Ya dora habar sa tsakiyar kaina. A hankali ya ke bubbuga baya na da hannun sa, ya ce.
"Ban san me Adda ke nufi da ni ba, ta ce sai ta ga dama zaki tare, ni kuma hakuri na ya kare Asma'u" zamewa na yi daga jikin sa zan fice da sauri har ina tuntube. Kunya kamar in yi yaya. Da sauri Yaya Maccido ya sha gaba na, looking at me affectionately.
"Ina alkawarin da mu kai na cewa in na zo za ki ce min Maccido?"
Tafuka na nasa na rufe fuska ta ga hawaye shabe-shabe "don Allah Yaya ka yi hakuri" ya ce " ai baki isa ba, ba ki zuwa ko nan da can sai kin cika alkawarin nan, Maccido ko Attahir, sai kin fadi guda daya".
Ganin da gaske Yaya ya ke bazai barni in fita ba ga Adda na can tana jira na dole na runtse ido na ce "Attahir, ka bude min kofa in fita" da murmushi mai kyau Yaya ya ke kallo na kafin ya ce "saura daya alkawarin".
Zaro ido na yi waje don na tuna alkawarin da na yi masa, wanda giyar so ta kwashe ni na yi masa a waya wanda sirri ne a tsakanin mu, bayan kuma alkawari ne dana san bazan taba iya cika shi ba.
Ina ji ina gani Yaya ya cigaba da hargitsa duniya ta yadda ya ke so ya ke muradi da wata irin zazzafar soyayya. Ya dauke ni ya shilla a duniyar da shi kadai ya san irin ta. Al'amarin da ya dauke mu lokaci mai tsaho. Gabadaya mun manta da kiran Adda, itama bata kara zuwa ba, amma tana can cike da fargaba da tsoro, tsoron kada Attahir ya tabbatar da auren sa gaban ta. Ta dade da fahimtar ba wani abu da ya shiga tsakaninmu a Jeddah, haka har muka je Madinah muka dawo. Soyayyah ce 'yar usli mai tsafta Attahir ke gwadawa Ma'u, soyayyar da ya tabbatar wata diya mace bata taba samu daga gare shi ba.
Shi da kansa ya ankarar da kan sa cewa... this is not the right place.... and not the right time... dole ya kyale ni na fita wajen Addah duk ba cikin nutsuwa ta ba. Kallo daya ta yi min ta dauke kanta tace in je in yi serving Yaya abinci tun da ya iso bai ci komai ba, daga haka ta bar mana falon da ta ga Yaya Maccido na fitowa shima.
Adda na shiga dakin ta Aunty Nabeelah ta kira, ta ce ta zo haka su yi shirin tarewar Ma'u. Ita bazata iya da mu ba. Attahir ya zo muna ta mata rashin kunya a gida, Aunty ta yi dariya sosai ta ce insha Allah tana tafe sati mai zuwa.
Yaya na gama cin abinci Al-Qasim yayi sallama kan sa a kasa. "Come and join us" inji Yaya. Sosa kai ya shiga yi cike da kunyar abinda idanun sa suka gane masa dazu "I'm okey Master". Yaya ya goge bakin sa da tissue ya mike ya dube ni na sunkuyar da kai, ya ce.
"Zan ga Al-Qasim ki shiga daga ciki".
Har karfe goma na dare suna tare a falon suna lissafe-lissafe da kasafce-kasafcen su cikin kwamfuta. Da barci ya fara fizga ta Yaya bai shigo ba na mike na ce "Adda zan je in kwanta barci nake ji". Gadon ta ta nuna min "yi a nan, yau anan za ki kwana". Ban gane hausar Adda ba sai da Yaya Maccido ya zo yana yi mata sallama zai je ya huta, ya ce "Asma'u har ta koma dakin ta ta kwanta ne?" Adda ta yi fuska ta ce tana cikin daki na tana barci" Yaya ya tsaya ya kasa tafiya, ta sake hade fuska ta ce "wani abu?" Da sauri ya juya yana fadin "mu kwana lafiya Adda, dama sako zan bata" Adda tayi murmushi ta ce "da safe ka bata". A zuciyar ta ta ce "ba dai a gabana ba, ka yi hakuri har in kawo maka ita".
Ina ganin kiran Yaya nata shigowa na ki dagawa sabida kunyar Adda.
Washegari Yaya da fushi ya shigo gidan, da na gaishe shi sama-sama ya amsa, Adda ta yi masa tayin karin kumallo ya ce ba yanzu ba. Daga baya ya kira Al-Qasim ya zo ya dauke shi suka tafi mall. Bai dawo ba sai can yamma. Ya same mu nida Adda muna girkin dare a kicin. A jikin cabinet din kicin din ya tsaya fuska a daure ya ce "Adda sannu da gida" ta ce "kai kuma sannu da yawo ba ci ba sha. Ma'u shirya masa abincin gashi har na rana ya kusa tadda na dare" juyar da kai yayi gefe ya ce da Adda "ni ba na jin yunwa, gobe da sassafe zan wuce Adda saboda Monday in shiga ofis akan lokaci". Adda ta ce.
"Allah ya kai mu lafiya".
Zuciyata ta yi ba dadi da biris din da Yaya yayi da ni, da kuma jin gobe zai koma. A sanyaye na ce "sannu da dawowa Yaya". Harara ta ya yi ya bar kicin din, Adda tace "wuce ki bishi falo ku gaisa sosai ki bar min aikin, na ga alama fushi ya ke yi, ban san tsakanin ni da ke wa ya yi laifin ba".
Murmushi na yi. Na wanke hannu na a sink na tsane da karamin tawul, sannan na bi bayan Yaya.
Ban same shi a falo ba, haka dakin Adda na duba ban gan shi ba. Kwata-kwata ban kawo yana daki na ba, na shiga kai na tsaye da niyyar in dauki waya in kira shi inji inda ya ke.
Anan na sameshi zaune bakin gado na ya hada tagumi da hannuwa bibbiyu. A hankali na taka na isa kusa da shi na zauna. Lokacin da ya juyo muka hada ido, sai da zuciyata ta girgiza da abinda na hango cikin idanun sa. It's nothing but pure love wanda babu surki a cikin sa. Gabadaya ya kara rikita mu daga ni har shi da deep kisses din sa masu tsayawa a zuci. Al'amuran sa masu ban mamaki ne. Ban iya fadin halin da Yaya Maccido ke ciki a wannan lokacin, gabadaya ya manta da fushin da yake yi.
Adda ta taho dauke da tray ta shiryo masa abincin ta biyo shi da shi ganin har zuwa lokacin bai shigo ya ci ba, abin ki da uwa akan cikin dan ta. Da bata gan shi a falo ba ko dakin ta ta nufo daki na da abincin. Ai kuwa Adda ta yi kyakkyawan gani. Mu dai sai ji muka yi an ja kofa an rufe. Abinda ya maido da hankulan mu daga ni har Yaya. Na kife fuska cikin tafuka na na rasa inda zan sa kai na. Shi kuwa Yaya murmushi ya yi, ya mike yana gyara karin hular sa.
"...... Asma'u that's what i want ai, ta san cewa ina bukatar mata ta...kada abin nata ya koma daukar hakki".
Sai da ya kara jimawa kafin ya bar dakin kamar ba zai tafi ba. Ban san yaya suka kare ba shi da Adda. Ni kam har washegari da safe da Yaya ya shigo don yi min sallama zai wuce ina cikin bargo kudundune na kasa fitowa, balle in hada ido da Adda. Yanzu ne na san Adda ta zame min suruka ta hakika, na kuma san abinda ya sa kunya da nauyi ke shiga tsakanin mata da iyayen mijin su.
Bayan tafiyar Yaya wuni guda sur ina kaucewa haduwa da Adda cikin gidan, na zama daga daki sai daki. Ita da kanta da ta gaji da rashin gani na ta biyo ni da abinci har daki. Sai da na yi kwana uku ina buyar wa Adda kafin na saki jiki na mu cigaba da harkokin mu cikin gidan kamar yadda muka saba.
Yaya Maccido in bai kira ni sau hudu ba a rana zai kira ni sau uku. A wannan dan tsukin ba abinda Adda ke yi irin tsananta Addu'a a kai na da Maccido, tana mai godewa Allah da Maccidon ta ya dawo mata, har ma fiye da baya. Yadda ya ke kula da ita da dukkan al'amuran ta da lafiyar ta sai ya ke tuna mata da mahaifin sa marigayi Alh. Atiku Dogondaji. Kullum addu'a take yi tana karawa kan Allah ya zaunar da mu lafiya, ya kara soyayyar Ma'u a zuciyar Attahir, ya kare mata shi daga dukkan abin ki, da sharrin duk wani mai sharri.
Chapter 29 · 0% Book details