← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 33

Sashe 30

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

******
Kamar yadda Addah ta ce, sai ta hada mana kasaitacciyar walima don wadanda ba su samu labarin auren ba cikin ‘yan uwa da abokan arziki su sani. Don haka da ta fahimci Yaya hakurin sa ya kare dole ta soma aikawa mutanen arzikin ta, ‘yan uwan su Yaya na Dogondaji, abokan arziki na Bebeji wadanda suka yi zaman mutunci da iyaye na. Ta tada dan aike har garin Babura ta jihar Jigawa ko za'a samu saura cikin dangin mahaifiya ta Nene Zainabu.
Dan aiken Adda ya dawo da kyakkyawan labarin an samu mata uku wadanda suka tabbatar masa suna da alaka da Zainabu matar Adamu Bebeji, daga gidan dagacin Babura aka raka shi wajen Inna Asabe, wadda kanwa ce ga kakar Zainabu, sai Abuwa wadda mahaifiyar su Nene ce ta rike ta har ta yi mata aure duk da babu alakar jini a tsakanin su.
Sai Jummai matar Baban Nene, amma ta tsufa sosai ba za ta iya zuwa ba, amma Inna Asabe da Abuwa sun tabbata za su zo in har za a dauki nauyin kai su Sokoto. Wannan bai damu Addah ba, burin ta ya kasance ina cikin dangin uwa da uba, don haka ta yi alkawarin tura direba ya dauko su tun daga Babura har Sokoto.
Kafin Aunty Nabeelah ta iso, kayan da ta auno ne suka fara isowa. Bayan kwana biyu ta biyo bayan su, Yaya tunda ya tafi bai kira ni ba yana ta fushin sa amma yana kiran Adda, yanzu kam Adda har gajiya take da wayar Yaya, Allah kenan, dama ya ce yana tare da su hakuri.
A satin nan kwata-kwata ban cika lafiya ba, ciwon fargabar aure ake cewa ko me? Kai ka ce wani waje za'a kaini ba cikin gidan mu ba, ji nake kamar zan yi da Adda, na dai san rayuwar kuruciya ta kare mini, ina dai daurewa ne ganin hankalin kowa yana kan hidimar da ya sa gaba. Aunty Nabeelah ke tambayar Yaya Maccido ko ya gaya wa Lubabatu maganar auren sa? Kai tsaye ya ce, Bai gaya mata ba, ya fi so sai na tare tukunna, sabida ya san halin ta ba za ta bar shi ya zauna lafiya ba. Shi kuma yanzu ayyuka sun masa yawa, ga na kamfanin su ga kasuwancin malls din su. Wadda a yanzu ya fadada na Abujan ya kara gina plaza a kusa da waccan, ya bada hayar shagunan.
Aunty ta ce, “Gara ka fada mata, in ta samo labarin a wani wuri abun ba zai yi muku dadi ba. Kuma ka hada mata kayan fadar kishiya, ko ka ba ta kudin a hannun ta”.
Duk da haka Maccido bai yi wa Lubabatu zancen ba don suna ‘yar dadi kwana biyun nan tunda ya dawo, ta yi missing dinsa sosai, don bai taba tafiya ya dade haka ba tare da ita ba.
Aunty Nabeelah da kawayenta na Sokoto suka shiga sassan Maccido na cikin gidan, suka sa aka fidda komai, da ma babu abin da yake mallakin Lubabatu, ba ta zo da komai nata Sokoto ba, don ta san ba wurin zaman ta ba ne, sai dai ta zo da yawo in ta ga dama.
Zo ki ga inda ake jere mai aji, da ma kuma Yaya Maccido ya sa an yi furnishing gidan gaba daya, har bangaren Addah. Gida ya koma tamkar sabo, kai ka ce ba a taba zama a cikinsa ba.
Bayan sun gama kafin, Adda ta sa malamai suka yi saukar alqur’ani a cikinsa. Washegari aka yi kasaitacciyar walimar da Addah ta shirya ta mata zallah, aka yi laccoci masu muhimmanci, sannan aka yi ta rabon kabakin takeaway da sovaneours, kowa ya tafi gida very excited don bai taba zuwa walima mai albarka irin wannan ba.

*YIWA KAI HISABI*

*SUMAYYAH ABDULKADIR (TAKORI)*
Chapter 30 · 0% Book details