Sashe 4
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Gaba dayanmu muka daga kai muka dube shi. Maccido ne daga Cuba, Maccido (Tahir) Atiku Dogondaji, kamar yadda cikakken sunansa yake. Fari ne ba sosai ba, ya fi kyautuwa a kira shi wankan tarwada. Akwai abubuwa da yawa a tare da Maccido da ba duka maza Allah ya mallakawa ba. Yana da wani irin sassanyan kyau, wanda a kallo na farko ba za ka ganshi ba, abin da za ka gani shi ne, ilhama da cikar halitta.
Duk inda ake neman maza su amsa sunan su, to a sanya Maccido cikin su, ko shi kadai zai wakilci guda dari.
Maccido mutum ne wanda ba shi da fara’a ko kadan, sannan ba ya wasa ga na kasa da shi, very responsible person, sannan ba ya son duk wata harka in dai akwai shiririta a cikin ta. Shi din wani irin mutum ne mai matukar tsantseni da taka-tsan-tsan cikin mu’amalarsa da kowa. Ba ya shiga sabgar da ba tashi ba, kuma ba ya son a shiga tasa.
Babban sirrin Maccido shi ne iya daukar wanka da iya diresin, wadanda suka taru suka cakude suka ba shi wata irin kyakkyawar suffa wadda kafin ka samu mai irinta sai an tona. Maccido Taheer ya mallaki duk wasu nagartattun halaye da ake so namiji ya siffantu da su, kai dai barshi da shan kamshi da rashin fara’ar sa.
Wani tsalle da muhsin ya yi daga kujerarsa sai ga shi makalkale da Yayansa Maccido,
“Brother da ma kana hanya amma shine ba ka gaya mana ba?”
Dan murmushi ya yi yana yi wa Adda sannu da gida kamin ya samu gefen kafafun ta ya zauna, ya dora hannunsa kan tafin kafar ta.
“Ka sauka lafiya Maccido, ya ya hanya kuma ya ya karatun?”
Ya dukar da kai ya ce, “Na zo lafiya Addah, da fatan na same ku lafiya, saidai karatu akwai matsala. Adda na samu carryover har biyu, abin da ban taba samu ba a tarihin karatu na. Wani irin faduwar gaba nake yawan yi. Ga yawan yin zurfi a tunani. Sannan Adda haka kawai sai nake fama da anxiety wanda ban san dalilin sa ba”.
Hawaye suka ciko idon Adda, ta kauda kai daga kallon Maccido. Cikin sanyin murya ta ce, “Ka je ka yi wanka da sallah, ka zo ka ci abinci sai mu tattauna ko?. Yanzun akwai gajiyar zaman jirgi tare da kai na sani”.
Sai da Maccido ya yi duk abubuwan da Adda ta lissafa sannan ta runtse ido ta gaya masa duk abubuwan da suka faru a bayan sa.
Maccido shidewa ya yi na wucin gadi, iyakar firgita da tashin hankali irin wanda dan Adam ke kasancewa a ciki, a lokacin da ya samu labarin gushewar mahaifi. Mahaifin ma irin Alhaji Atiku, wanda shakuwar da ke tsakanin sa da ‘ya’yansa ta zarta ta uba da ‘ya’ya kadai, su ne abokan sa kuma aminan sa. Sannan ya bugu da mutuwar Uncle din sa da maidakin sa Nene, wadanda akwai kyakkyawar alaqa ta soyayya tsakanin su da shi tun haihuwar sa.
Adda har zuwan kawunninsa daga Dogondaji da yadda ta kare da su sai da ta labarta masa. Maccido ya yi kuka har ya ba uku-lada. Kwanan sa bakwai ya kulle kan sa a daki, ba ya zuwa ko ina, abinci ma can Muhsin ke kai masa.
Hakika ya shiga wani hali wanda biro ba zai iya rubutawa ba. Nabeelah kan kira shi su yi kukan su mai isarsu. Komai na duniya ya fice masa a ka, karatun ma ya soma tunanin kin komawa. Gani yake a yanzu shi ne gatan uwar sa da ‘yan uwan sa. Ga marainiya Ma’u wadda ta karu a cikin su, takalihun ta dole ya dawo hannun sa. Ya kan tuna soyayyar mahaifi na gare shi don haka ya sha alwashin rike ni cikin su kamar yadda zai rike Muhsin.
Da kyar Adda ta lallashi Maccido ya koma makaranta bayan karewar hutun sa. Da lallashi da ban-baki, da kalaman karfafa wa Adda tasa shi ya gyara takardun sa.
Ya kuma ci gaba da karatu da wata irin himma wadda a baya ba shi da ita. Apart from course din da yake yi, watau "Architecture" sai ya kara da Business Administration, ba don komi ba sai don ya samu sani kan ilmin kasuwanci, ya zo ya tallafi dukiyar da mahaifin su ya wanzar da rayuwar sa ya tara musu. Gaba daya rayuwar sa ya fuskanci neman ilmi ka’in da na’in, don ya san yanzu shi ne kadai gatan da zai yi wa kansa da mahaifiyar sa da marayun ‘yan uwan sa.
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE*
10/09/2023
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
~HISABIN NAFS~
((3)) *BAYAN SHEKARU UKU*
Abubuwa da yawa na ci gaba sun faru cikin shekaru ukun da suka biyo baya ga iyalin marigayi Atiku Dogondaji. Aunty Nabeelah ta kammala karatun ta da ta ke yi a Beirut (Lebanon) ba ta tashi dawowa ba sai da guzurin miji balarabe dan asalin kasar Lebanon. Sunanshi Fa’iq, malaminta ne a makaranta wanda soyayya mai karfi ta shiga tsakanin su, wannan ya samo asali da matukar kokari irin na Aunty Nabeelah. Ya biyo ta har Sokoto tare da waliyyansa.
An kai ruwa rana da su Baffa Bilya kafin su amince su aurar da Nabeelah ga Fa’iq don cewa suka yi in ta tafi bata za ta yi. Sai da Fa’iq ya alkawarta kawo Nabeelah gida duk karshen shekara, haka duk mai son ganinta zai dauki nauyin zuwan sa gare ta, sannan suka amince aka daura auren. Fa’iq ya dau Nabeelah suka koma Beirut.
Yaya Maccido ma ya gama nasa karatun ya samu tayin aiki iri-iri da construction companies daban-daban, amma a karshe ya zabi ya yi aiki da Julius Berger Nigeria, suka barshi a babban reshen su na birnin Tarayya, Abuja.
Tun daga lokacin ne ganin sa ya yi mana tsauri. Ya tattara duk dukiyar da mahaifin su ya bar musu ya bude musu wani katafaren shopping mall kusa da Al-madina, ya dauki amintattun yara ya zuba, Muhsin ne manajan wajen duk da karancin shekarun sa. Ko dama can Muhsin haziki ne kuma yana da sha'awar kasuwanci. Shi yasa nauyin da Yaya Maccido ya dora masa bai gagare shi ba.
Duk wata ribar shagunan na tafiya kai tsaye account din kowannen su adadin hannun jarin sa. Babu abin da ba a samu a mall din tun daga suttura da kayan abinci na kwalam, da duk abin da Dan Adam ke bukata, kasancewar wajen fuskar jama’a ne, nan da nan sunan MACCIDO MALL ya yi fice a garin Sokoto, kayan su unique ne don Adda ta sa hannu tunda tuntuni ta saba da kasuwanci.
Allah kuma ya sanya musu albarka a cikin neman su, asirin wannan family a rufe yake ruf, duk yadda suka yi tunanin rayuwa za ta juya musu baya a bayan ran Atiku Dogondaji hakan bai kasance ba, Allah ya bawa Adda Da daya tamkar da goma, wato Maccido (Attahir), wanda a shirye yake ya sadaukar da rayuwar sa don ingantuwar rayuwar mahaifiyar sa da ‘yan uwan sa.
A wannan shekarar ne Yaya Maccido ya zo wa da Adda bukatar yana so ya yi aure. Adda ta tambaye shi ko ya samu matar ne? Ya ce, eh, ya samu a can Abuja kanwar abokinsa ce Usman, sunanta Lubabatu. Adda ta ce, “Yan wane gari ne?”
Ya ce, “'Yan Birnin Kebbi ne”.
Shiru Adda ta yi na dan wani lokaci tana nazari kafin ta ce.
“Maccido ba mu da kowa ni da ‘ya’yana, daga Allah sai kai. Matar duk da za ka aura ya kamata ka tantance ta, ka yarda da tarbiyyar ta da dattijantakar gidan da ta fito. Wadda za ta so mu ta zauna da mu tsakani da Allah. Wadda za ta taimaka maka wajen kula da marayun ‘yan uwanka. Ba wadda za ta kawo canji komai kankantar sa cikin abin da ta zo ta taras ba. Idan ka yarda ka amince ita Lubabatun ta mallaki duka wadannan, to muna maraba da ita”.