← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 33

Sashe 7

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Adda ta ce, “Da ma Dogondaji ki ka tafi wajen dangin ki, da ya fi miki, bana so ki je ki dora musu hidima”.
Aunty Nabeelah ta yi wani irin murmushi ta ce da Addah, “Can din ma zan je in na dawo kafin in koma. Bar ni in duba dan uwana rabin raina”.
Adda sai ta mike da nufin barin wajen, Aunty Nabeelah ta ce, “Ina neman alfarmar rakiyar Ma’u, kin san ta fi ni iya kula da Aasim”.
Addah ta ce, “Lala-lalah! Ma’u ba ta taba tafiya mai nisa ba, kuma kin sani ba hutu suka yi ba”.
Aunty ta marairaice, “Don Allah Addah wallahi zan kular miki da Ma’un ki, insha Allahu lafiya za mu je mu dawo, kuma gobe juma’a za mu tafi mu dawo lahadi. Zan koya mata karatun da ya wuce ta na islamiyyar".
Muhsin ma ya saka baki.
“Ai ni in babu Ma’u babu ni a tafiyar, na fi so kullum tana gefe na in ina tuki, don ma ba ni da kudi ne da na fara biyan Adda toshin Ma’u”. Ya fada yana sosa keya da mukullin motar shi.
Dariya Aunty ta yi, ta ce, “Da kun bada perfect match gaskiya. Kai 18 years, ita 16 years, ku tara ‘ya’ya before 20 years ku cika wa Addah daki da su su taya ta hira”.
Na galla masa harara tare da zumburo baki, “Allah ya sauwake in aure ka, me zan yi da dan ball?”
Ya ce, “Yarinya ball aji ce yanzu, da Adda za ta ba ni dama da har Manchester sai na je na buga ball”.
Adda ta yi tsaki, “Ku bana cikin shiririta, kada in kara jin wannan maganar, dukkan ku yara ne kuma karatu nake so ku yi, in ba za ka taimaka mata wajen ganin ta maida kai ga karatu ba, to kada in kara jin wannan maganar”.
“Mun tuba Adda, mun bi Allah mun bi ki!”. In ji Muhsin.
“Addah, don Allah mu tafi da ita?” In ji Aunty Nabeelah tana marairaicewa.
“Ku je Allah ya kiyaye hanya. Amma don Allah Nabeelah ki kama girman ki, kada ki je ki yi halin yara na sanki sarai”.
Murmushi mai ciwo ta yi, ta ce, “Insha Allahu Adda zumunci ne kawai zai kai mu”.
Tuni na tsallake su na tafi na soma hada mana kaya. Aunty Nabeelah ta shigo ta tadda ni har na zuge jakar ta da tawa da ta Aasim.
Ta ce, “Aiki ga mai kare ka…”
Dariya na yi, na ce, “Don ba ki san yadda nake son zuwa Abuja ba ne Aunty Nabeelah, in ga Aunty Lubabatu mai gashi. Sosai nake son ta wallahi”.
Aunty ta ce, “Wace ce haka?”
“Matar Yaya Maccido mana!”.
Tsaki ta yi, ta ce, “Allah ya shirye ki Ma’u”.
Ba mu isa Abuja ba sai yamma lis, duk da cewa mun yi asubanci, kuma gudu sosai Muhsin yake yi. Gaba daya mun yi wujiga-wujiga. Aasim sai tsala kuka yake yi sabida gajiya da ciwon jiki.
Muhsin ya dauke kan motar ya shiga unguwar Gwarimpa, gidajen su Yaya Maccido na daga farko-farkon unguwar. Bai tsaya ba sai a kofar apartment din wanda ke dauke da fenti ruwan madara da ruwan kasa. Kananan gidaje ne a cikin estate masu kyau da tsari. Kusa da Cadillac din Yaya Maccido Muhsin ya adana motar sa, sannan ya kashe. Gabadaya muka yi hamdala ta godiya ga Allah da ya nufe mu da isowa lafiya.
Aunty ta ciro wayar ta a jaka saura kadan cajin wayar ya muta, ta kira lambar Yaya Maccido. Sai da ta yi ta burari tana sake kira ba tare da ta kosa ba, kamin ta samu ya daga wayar da sassanyar sallama a bakin sa.
“Ga mu a kofar gida”.
Kawai ta fada ba tare da ta amsa sallamar da ya yi mata ba.
Ya ce, “Kofar wane gidan?”
A gajarce ta ce, “Naka”.
Ta kashe wayar tare da jefa ta cikin jakar hannunta.
Muna ganin sanda aka zuge labulen falon aka tabbatar akwai bakuwar mota a kofar gidan, kafin entrance door din ta bude. Yaya Maccido ya fito sanye da jallabiyya fara kal mai gajeren hannu, kafarsa slippers ne mai kalar fari shi ma. Ido na kura wa Yaya Maccido, yana karasowa inda muke.
Zuciyata na ji tana bugawa da sauri-sauri (at a speedy level) sakamakon ganin wata irin rama da baki da ya yi. A lokacin da ya iso gaban motar mu ba zan iya ci gaba da kallon shi ba, runtse idanuna na yi na sunkuyar da kaina ina tambayar kaina, wace irin rashin lafiya ya yi haka?
Ita kanta Aunty Nabeelah jikin ta ya yi sanyi, ta yi saurin balle murfin motar ta fito ta rufe ta jingina jikin motar tare da harde hannayenta a kirji tana kallon shi yana doso ta.
Muhsin ma ya fito, amma ni sai na gyara zamana ina kallonsu daya bayan daya. Ya iso gaban Nabeelah kamar za su hade don kusancin da ke tsakanin su, ya ce,
“Baki haka unexpected?”
Duk wani tanadi da Nabeelah ta yi na cin mutuncin Attahir ta neme shi ta rasa. Duk wasu muggan kalami da ta shirya fada masa sun subuce daga bakin ta. Kallon sa kawai ta ke kafin ta kai hannu ta dafa kafadar sa.
“Maccido!” Ta fada a hankali.
Dan murmushi ya yi kafin ya ce, “Nabeelah, ya ya za ku taso tun daga Sokoto amma ki kasa kira na ki fada min?”
Ta lumshe idon ta a hankali ta ce, “Saboda ba ma so ka san za mu zo. It is a surprize visit”.
Kama hannayenta biyu ya yi ya ce, "I appreciate. How is ADDAH?”
Cikin raunin murya Nabeelah ta ce, “Do you still remember her? Ba ka neman ta ko a waya Maccido!”
Maccido ya girgiza kai idanun sa sun kada, ya ce, “She is always in mind, na zama busy ne kwana biyu. Shekaran jiya muka dawo daga Egypt na kai Lubabatu ganin likita”.
Aunty Nabeelah ta gyada kai, “Ya yi kyau, mu karasa ciki ko? Don a gajiye muke”.
Juyawa ya yi kadan yana kallon falon nasa kamar mai tsoron ko ana kallon su, kafin ya ce, “Ku jira in sanar da matar gidan, bai kamata ta gan ku katsahan ba”.
Ya juya da saurin sa, Nabeelah ta girgiza kai tana bin sa da kallon tsoro da mamaki, a ranta tana kakabin al’amarin nan mai kama da mafarki. To tsoron matar tasa ya ke yi ko me? Ta gaza fahimtar komai, wai Maccido ne wannan? Kanin ta vibrant and energetic? Gabadaya ya zabge kamar an zabtare shi, ya yi sanyi kamar ba shi ba. Muhsin kam ai bai jira an dawo daga yi masa ison ba ya bude booth ya fiddo jakunkunan mu ya cicciba ya yi gaba da su yana fadin,
“Ma’u fito kin ji! In mun shiga ba izni a koro mu”.
Na zunkuda goyona sannan na fito.
Daga matar har mijin sai ganin mu suka yi mun murdo kofa muna shigowa, kowannen mu dauke da sallama a bakin sa. Cirko-cirko muka same su shi da Lubabatun kamar zakaru, da alama ko ma me suke cewa ba cikin dadin rai ba ne.
Wani kallo ta yi mana kamar ta ga kashi, sannan ta juya ta yi masa kallon za mu gamu ne, ta yunkura da kyar da tirtsetsen cikinta ta bar falon zuwa dakin ta. Ko kallon Aunty Nabeelah dake shigowa bata tsaya yi ba.
A rayuwar Attahir Atiku Dogondaji, bai taba jin ya muzanta a gaban Yayar shi da kannen shi irin yau ba. Ni dai ina daga gefe sai faman jijjiga Aasim da ke goye a baya na nake. An ce namiji har kullum namiji ne, shi ya sa Yaya Maccido ya sunkuya ya dauki jakar Aunty da tawa ya ce mu biyo shi, yayin da baby bag din Aasim ke hannuna.
Wani daki ya bude a falon ya ce mu shigo. Daki ne mai tsananin kyau ya sha furnitures na alfarma da shimfidar gado mai laushi. Ya juya cikin jin nauyi ya ce da Aunty Nabeelah.
“Zan je na kai Muhsin hotel na samo muku abin da za ku ci, babu dakin da zai iya sauka a nan”.
Aunty ta ce, “A gaskiya ni bana cin abincin sayarwa sai wanda aka sarrafa a gida”.
Ya jefar da kai gefe, ya ce, “To ba mu yi ba, ko ba kya ganin ta yi nauyi ne, yaushe za ta shiga kitchen ta yi muku wani girki a daren nab?”
Aunty ta kyabe baki, ta ce, “ba matsala, in dai akwai kayan girkin, yanzun nan Ma’u za ta dafa mana”.
Shi sai a lokacin ma ya lura da ni da ke gefe ina fama da baby. Ya dan dube ni na ‘yan sakanni a ran sa ya ce, “Ta yi tsawo, ta kara girma”.
“Ba ki gaji ba za ki iya girki?” Ya fada yana kallon bangaren da nake.
“Babu komai, zan iya”. Na bada amsa cikin girmamawa.
“Okey, mu je in nuna miki komai”.
Na mika wa Aunty Aasim, na bi bayan shi muka fita.
Wani rantsattsen kitchen ya kai ni, komai tafiyayye kuma rantsattse, sai dai tsaftar kitchen din da sauki. Ya nuna min freezer da fridge ya ce, “Komai ki ke nema za ki samu”. Sannan ya bude wani labule da ya raba kitchen din biyu. Kayan abinci ne katan-katan da abincin gwangwani nau’i-nau’i, ya nuna min bangaren spices da maggi, sannan ya dago ya dube ni by mistake muka hada ido.
“Ki dafa har da ni”.
Kai na gyada, ya fita ya bar min madafin.
Samun kaina na yi da bin bayan sa da kallo, wani irin kallo na tausayi da kaunar ‘yan uwantaka. Masculine turaren sa mai sanyi har zuwa lokacin bai bar kicin din ba. Ajiyar zuciya na yi bayan fitar sa, na dau madaidaiciyar tukunya na aza bisa wuta. A raina ina cewa, jallop din cous-cous zan yi da farfesun kifi kawai ya fi sauri.
Na zo shigowa dakin don in tambayi Aunty ko zaben da na yi mana ya yi mata? Na ji tashin muryar ta a bakin kofa cikin bacin rai tana fadin.
“Yanzu a matsayi na na Yayar ka uwa daya uba daya, tarbar da matar ka za ta yi min ke nan? Ta yi min kallon banza ta shige daki, to me na tare mata? Ko zuwana ne ya bata mata rai, ko kuwa ba ka gaya mata ko ni din wace ce dinka ba?
In ba ta so a rabe ta kaima sai ta hana ka rabar kowa naka? Uwar da ta haife ka Maccido tunda ka yi aure ta daina ganin ka? No wonder na ga duk ka fige kamar kazar mayu, to ko dai ita mayya ce ta ke lashe ka ba ta so a ankara sai ta gama cinye ka tas? Ta kaiwa uwarka kasusuwan ka? Attahir let me tell you what you forgot… Addah ba ta da kowa sai mu, ba ta bukatar komai a wannan stage din na rayuwar ta sai mu da kulawar mu. Idan ka biye wa wannan annamimiyar wuta za ta kai ka billahillazee… Na gama fahimtar babu mutunci da imani cikin al’amarin ta.
Bari ka ji in gaya maka, in ma asiri ta ke maka, ko tsoron ta ka ke ji da ka watsar da kowa naka ka kamata, to mu zuba mu da ita shege ka fasa! Ta zo gidan da ba a san asiri ba, amma an iya dungura goshi a yi sujjadah. Tunda ka zabe ta a kan mahaifiyar ka ka je mun yafe mata kai, amma zamu kai kara wajen Allah.
Dadin abun ba kai kadai Adda ta haifa ba… Allah ya kai mu gobe za mu yi asubanci mu koma inda muka fito, in yaso ta yi gunduwa-gunduwa da kai ta sa a tukunya ta dafa ta cinye…”.
Ta fashe da matsanancin kuka, wanda ya sa ni saurin ja da baya na koma kitchen gabana na faduwa. Ban taba jin Nabeelah na magana cikin zafin rai irin yau ba. Jikina har rawa ya ke yi in na tuna babban mutum irin Yaya Maccido take yi wa wannan fadan.
Chapter 7 · 0% Book details