Sashe 33
Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
*TUKUICI NE GA TAKORI'S LOUNGE AND TAKORITES*
*SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI*
SOKOTO
Ihsan ce a gaba, Ahsan ya biyo bayanta sanan babansu. Suka yi sallama a dakin Adda. Zaune nake tsakiyar gadon Adda na yi rashe-rashe ina cin gugguru. A tare ni da Adda muka dubi kofa don ganin masu shigowa. Yaya Maccido da na yi masa kallo daya kasa dauke ido na yi a kansa. Gabadaya ya rame ya yi duhu, mutumin da watanni uku da suka gabata kamar ka taba fatarsa jini ya yi tsartuwa.
Hannu na bude wa Ihsan ina kiranta, Adda kuma Ahsan ta ke kokarin dauka. Farin cikin ta ya gaza boyuwa. Ta kara amincewa Allah sami’ud du’a’I ya dawo mata Maccidon ta da ta haifa, ba mai kama da shi a baya ba.
Yaran duk suka lafe jikin Baban su alamar ba su zuwa ba su san mu ba. Da wayo da cakulet da pop-corn na samu Ihsan ta yarda ta zo kusa da ni, na jawo ta jiki na zuciyata kamar takarda. Yau ba ni da abin da zan biya Yaya Maccido. Ahsan kuwa da Adda ta matsa da son daukarsa, kuka ya saka yana kiran Mamansa. Yaya ya ce, “Ahsan my mum? Ba za ka je wajen Mamana ba?”
Adda ta mike ta soma hidima da su, shayi ta fara hada musu mai kauri kafin ta cika gabansu da lafiyayyen abinci wanda na dafa wa Yaya domin ya yi waya ya ce yana hanya, amma bai gaya mini tare da yaran yake ba. Ya ce "Surprise yake so ya yi wa kowa”.
Hawwa Adda ta tura ta gyara sashenmu tun kafin isowar Yaya, don ba ta bari na in yi aikin komai. Girkin ma don na Yaya Maccido ne shi ya sa ta bar ni na yi da kaina.
Yaya Maccido da Adda sai hira suke cikin nishadi. Na kama hannun Ihsan na dauki Ahsan wanda zuwa yanzu ya soma warewa. Na ce, “Addah za mu je a yi wanka, Hawwa ta shigo min da jakar kayan su”.
Addah ta ce, “A dai yi wankan a dawo min da su nan, yau ga kafada ta ga tasu za mu kwana, ki je ki ji da mijinki ya debo hanya ya zo ki ce rainon ‘ya’ya za ki yi, shi kuma wa zai yi nasa rainon?”
Kunya ta kama ni na fice da sauri tare da yaran.
A falo muka yi karo da Muhsin ya ce, “Lallai yau za a yi ruwa da kankara ‘ya’yan Abuja ne a gidan mu?”
Na ce, “To ga su dai ka gansu, ka zo ka sayo musu pampers”.
Na yi musu wanka da ruwa mai dumi, Ihsan na ta yi min hira. Shi Ahsan bai iya magana sosai ba. Hawwa ta kawo min kayansu na sa musu, na gyara wa Ihsan gashinta, nan suka yi shar duk suka yi kyan gani. Muna hira da Ihsan barci ya dauke su a jikina.
A haka Yaya Maccido ya cimmana. Daga bakin kofa ya tsaya yana bina da wani sassanyan kallo. Yafito ni ya yi da hannun sa, ya yi min alamar in zo gare shi. Na yi masa nuni da yaran da ke jiki na. Karasowa ya yi ya dauke su su duka biyun a kafadunsa yana fada kasa-kasa don kada ya tada su,
“This is cheating!”.
Na ce, “Don Allah Yaya ka bar su mu kwana”.
Hararar da ya yi min ta nuna ina bata baki na ne kawai.
Wajen Adda ya kai su ya dawo. Kafin ya gama abin da yake a falo na hada masa ruwan wanka na zuba turaren wankansa a ciki na desire dunhill.
Muna kwance kalmashe cikin jikin juna bayan al’amura sun daidaita a tsakanin mu, na kai hannu cikin sumar Attahir ina cakudawa sannu a hankali. Cikin muryar da ke nuna damuwa na ce,
“Yaya ka rame, at the same time ka yi baki”.
Idanunsa a lumshe ya ce, “Don ma ba a kawo miki gawa ta ba? Amma Lubabatu kashe ni ne kawai ba ta yi ba, in haka ake kishi Allah wadaran kishin mata. This is insane. Ranar da zan miki taki kishiyar ashe ke ma daina so na za ki yi?”
Hannu na ya kai kan tudun wani dinki a kasan kansa.
Cikin damuwa na ce, “Wannan fa?”
Ya ce, “Duk a cikin punishment dina na kara aure ne”.
Cike da tausayi na ce, “Yaya kishin mata kala-kala ne, I can never hurt you like this don ka yi min kishiya, zan yi fushi da kai for the mean time in daina yi maka magana, but I can never ever hurt or insult you…”.
Yaya Maccido ya shigar da ni cikin jikinsa sosai ya rungume ni.
“Balle ma ba zan yi ba Asma’u. Da a ce ke na fara samu ba zan yi mata biyu ba. You are more than enough to every husband. Darajar yaran nan nake dubawa shi ya sa har na daure na ci gaba da zama da Lubabatu cikin mugun yanayin da ko makiyana bana masa fatan auren mace irin ta’.
Tausayin Yaya ya kama ni, na sani tun fil’azal shi ba mai son tashin hankali ba ne. Na soma kissing dinsa lightly duk dai don in mantar da shi bacin ran da yake ciki. Daga nan muka manta komai sai hanyar da za mu faranta ran juna. Kullum ya zo gare ni tamfar ba mu taba kusantar juna ba haka muke komawa. Soyayyar kamar ana mata ban ruwa, tana dada yin yado da rassa.
A hankali zuciyata ta gama macewa a son mijina Attahir, wani irin so da ban san iyakar sa ba. Yaya ya tafi ya bar Ihsan da Ahsan tare da mu, sosai nake kula da yaran, kwana biyu suka ware suka saki jiki da mu, Muhsin na fita da su in ya dawo ya sawo musu ice-cream, ai kuwa nan da nan suka makale masa, su ce min Aunty su ce wa Adda Granny kamar yadda Muhsin ya koyar da su.
Al-Qaseem ya zo ya gaya wa Addah ya samu matar aure, za a je masa tambaya, ‘yar garin Zamfara ce, Addah ta ce in an fidda ranar zuwan ya sanar da ita za ta je insha Allahu.
A gajiye Attahir ya iso gida, falmaran din suit din jikin sa a hannu da jakar macbook din sa ya fito daga mota ya rufe ya taka zuwa cikin gida.
Tun jiya da daddare da ya dawo ba su hadu da uwargidan ba, sanda ya dawo ba ta sani ba sannan da sassafe kafin ta fito ya wuce ofis. Yana shigowa da ita ya fara tozali zaune a tsakiyar three seater.
Kallo daya ya yi mata ya kauda kai yana mamakin wai wannan matar sa ‘yar kwalisa wanke hannu ka taba Lubabatu ce, ta koma kamar wadda aka kwanto daga turu, ta yi baki ta rame kamar ba ita ba. Kayan jikinta ya gane tun wadanda ya ganta da su ne ranar da zai tafi Sokoto. Lokaci na farko da tausayinta ya dan tsirga masa, ya sa kafa ya wuce ta zuwa dakin sa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Yana shiga dakin ya tsaya jikin gado ya soma loosing tie din wuyan shi. Bankado kofar dakin ta yi ta fado kamar an jefo ta. A firgice ya juya suka yi ido hudu. Cikin kakkausar murya ta ce.
“Attahir ina ka kai min ‘ya’ya na?”
Ya juyo tare da dan kura mata ido, sannan ya juya ya ci gaba da abin da yake yi. Hakan ya kara fusata ta, wato ma bai san tana magana ba. Takowa ta yi har gabansa ta kama kwalar rigarsa ta girgiza shi cikin yanayin fita hayyaci.
“Wallahi ko ka ba ni ‘ya’yana ko shari’a ta raba mu”.
Trying hard to control his temper ya ce “Sake ni Lubabatu tun muna shaida juna, bana so tsautsayi ya sa na kara kai hannu a jikin ki, in har ba arziki ne ya kawo ki ba kar ki kuma gigin shigo min daki”.
Lubabatu ta sake shi ganin yadda idanun sa ke mata kallon da ta tabbatar yana nufin abin da yake cewa. Ta sulale a gaban shi ta fasa wani irin gigitaccen kuka, ta ce,
“Tsakani na da kai yau ke nan Tahir, sabida ka auri ‘yar gidan ku? Duk soyayyar da na shayar da kai ka manta? Duk wahalar da na yi maka ta daukar ciki da haihuwa sakamako na ke nan? Me ka gano a jikin wannan yarinyar wanda ba ni da wanda ya fi shi? Shin soyayya ta gare ka tun ba ka da komai ta cancanci wannan butulcin? Me na yi maka a rayuwa banda so da kauna da za ka yi min wannan sakayyar?”
Ta ci gaba da kuka mai nuna komai ya fara kare mata, dabara, izza, masifar da bala’in gabadaya sun kare mata. Saboda wannan Tahir din da ke gabanta ta tabbata sabon Attahir ne ba wanda ta danne shekaru biyar yana mata biyayya da bauta ba.
An ce tsakanin mace da miji sai Allah. Sai ya samu kansa da jin tausayin ta. Ya san Lubabatu na son sa, kuma son ne yake take duk abin da ta ke yi, wanda a haukanta shi zai dawo mata da abin da ta rasa a Tahir din. Yana son Lubabatu domin soyayyar ce ta sa ya aure ta, amma in ya tuna yadda ta shiga tsakanin sa da kowa nasa tunda ya aure ta, sai ta yi bakikkirin a idanun sa.
Hannunta ya kama ya mikar da ita, ya ja ta suka zauna tare a bakin gado. Wani tsami-tsami da bashi-bashi da ke tashi daga jikin ta ya naushi hancin sa. Da kyar ya hadiye miyau, ya ce, “Lubabatu ke ce kuwa? Yaushe rabon ki da wanka? Now, ba ni da magana da ke sai kin je kin yi wanka, ki fesa turare sannan ki zo mu tattauna. Amma ki sa a ranki Asma’u ta riga ta zama wani bangare nawa, dole ki karbi wannan gaskiyar, idan har kina so mu yi magana ta fahimta ni da ke”.
Maganganun sa ba karamin tunzura Lubabatu suka kara yi ba, wai yau ita Attahir ke cewa tana wari, sabida ya auri 'yar cikin sa, har me wannan bagidajiyar zata gaya mata? Kodayake ta san da gaske tana bashin, rabon ta da wanka har ta manta.
Jiki ba kwari ta mike ta bi umarnin sa. Tana fita ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa. Bugu daya na daga ya ce,
“Asma’u ko ki neme ni ki ji ya na iso gida ko?”
Na yi kasa da murya na ce, “Ayya Yayana. Wayar tawa ce Ahsan ya tsoma min a bokitin ruwa, wai zai wanke min. Da kyar Muhsin ya samu aka gyaro ta yanzu. Amma ka san kana raina ko? Kuma addu’ata a kowacce sallar farillahta ita ce Allah ya kare min kai a duk inda ka ke”.
Attahir ya lumshe ido, muryata na kara kashe masa jiki, ya ce, “na gode da wannan addu’a taki Asma’u na, hope my soldier is kicking very well, kuma Ahsan da Ihsan ba sa damunsa? I’m missing you terribly… idan na ce kewa ina nufin ta komai…”.
Murmushi na yi na ce, “Yaya na gode, kai ma ka san in na ce I LOVE YOU is not enough to express the feelings…”.
Maccido sai daga kai ya yi ya ga Lubabatu a kansa tana huci kamar mesa. Kafin ya yi aune ta fizge wayar daga hannunsa ta rotsa ta da kasa. Har ga Allah ya so ya yi sulhu da ita a wannan daren don ta samu sanyi a zuciyar ta ko ya ya ne, amma abin da ta yi din nan ba karamin fusata shi ya yi ba. Ya daga hannu zai kai mata mari, ya yi maza ya taro hannun nasa. Ya rike hannun da zai kai marin da hannun hagunsa ya koma gefen gadon sa ya zauna.
“Fice min daga daki, kafin ki sa a kwashe ki a wheel-borrow yanzun nan, tunda ba tare muka hada kudi muka gina dakin ba”.
Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya tana fadin, “Aikin banza. An dai ji kunya wallahi, kanwar da aka gama yi wa muzurai shekara da shekaru, rana daya ake ce wa I love you don yada girma da bunsuranci. Yarinyar da ko fasali babu, ‘yar cin arziki kawai. Wallahi Attahir ka fadi babu nauyi".
Ganin ya taso zai cimmata ta kara da gudu ta bar dakin, ta shige nata ta banko kofa.
Rayuwar Yaya da Lubabatun sa ke nan. Sai abubuwa sun yi kamar za su gyaru sai ya kuntuka mata abin da zai sa ta kara birkicewa. Duk abin da yake yi akan Asmau ba yana yi don ya tsokane ta bane sai don shi kansa bai san ya ya aka yi yake zama Romeo ba in dai yana tare da Asma’u a waya. Ita kuma gata da labe, kalaman da Lubabatu ba ta iya jure wa jin su, kuma ta kasa daina yi masa labe ga duk wayar da zai yi ko da ba Asma’u ya kira ba.
Mamaki yake, sau tari ya ce "Lubabatu ashe haka ki ke? Ashe iblishiya ce ban sani ba? Shin a kanki aka fara kishiya? To sai dai ki kashe kanki, kuma Asma’u ta shigo gidan. Amma masifar ki, jidalin ki, bala’in ki, haukan ki da rashin hankalin ki ba abin da zai sa, ba abin da zai hana”.