← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 33

Sashe 15

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

******
JEDDAH, SAUDI-ARABIA
Yau ni Ma’un Nene ce a filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz dake birnin Jeddah. Duk da jinya ce ta kawo ni, na yi farin cikin kasancewa ta a kasa mai tsarki. Daga filin jirgi motar asibitin Doctoor Sulyman Faqeeh ce ta kwashe mu zuwa asibiti, inda likitoci suka rufu a kan Addah suka ba mu daki V.I.P kamar yadda Yaya Maccido ya zaba.
Kyawun dakin ya isa, kamar kana gidan ka. Ba abinda babu. Har da ciki da falo, talabijin, A.C, firji, da duk abin da dan Adam zai bukata. Tunda aka shigo da mu dakin ban kara ganin Yaya Maccido ba, yana can wajen management din asibitin. Haka tunda muka taho wata kalma ba ta hada ni da shi ba. Sai in na samu faraga in harare shi son raina in dauke kai. Aka ce aikin banza wai harara a duhu, don Maccido bai san ina yi ba, don kuwa ban ishe shi kallo ba. Duk da cewa ga kujera ta ga tasa, har kafadun mu na gugar na juna. Earpiece ya sa a kunnen sa yana sauraron kira’ar Abdurrahman Sudaith, daga baya ban san me yake yi ba sakamakon bacci da ya dauke ni bayan mun ci abinci.
Har muka sauka a Jeddah ina barci. Na gane an zo ne ta hanyar hannun Yaya da na ji ya zagaye ni yana unfastening belt dina. Saura kadan numfashi na ya dauke sakamakon dumin numfashin sa da ya sauka a wuya na. Na galla masa harara, a raina na ce ko ina ruwansa da ni? Oho! Meye business din sa da saka belt dina da cirewa? Bai san na yi ba, don kuwa bai ma kalle ni ba.
Na nisa daga zuzzurfan tunanin da na fada, daidai lokacin da aka turo kofar dakin namu aka shigo. Yaya ne, hannun sa rike da ledojin da na fahimci abinci ne ya sayo. A take akuyar ciki na ta motsa, don kuwa rabo na da abinci tun na cikin jirgi.
Zama ya yi a kujera ya ja karamin tebir gaban sa ya daura ya bude ya soma cin kentucky fried chicken din da ya shigo da ita, yana yi yana korawa da lemon Pepsi mai sanyi.
Na saci kallon sa tare da hadiyar yawu, mukut! Ko ya tuna da ni ya miko min dayar ledar, amma mutumin nan ban ishe shi kallo ba. Ya cinye kazar sa tas! Ya fiddo waya ya kira inda daga sunan Sweetie na fahimci shi da matar sa ne. Sauran hirarrakin kasa sauraro na yi, don ban saba jin irin su a rayuwa ta ba, sai na mike na sa silifas da zummar barin dakin. A raina ina ta mamakin Yaya, ashe da ma yana magana haka?
Na ce a raina, bari in fita in dan zaga ko zan samu abin da zan saya in ci. Na tuna ko sisi ba ni da shi. Idona ya cicciko da kwalla, na fita jikin barandar dakin na tsaya ina kallon shige da ficen motoci, a lokaci guda ina share siraran hawaye daga idona. Ni ban san kaddarar da ta jefa ni hada tafiya irin wannan da Yaya Maccido ba. Mutumin da uwar sa ma ba ta dame shi ba, wace ce ni da hakki na zai dada shi da kasa?
Wani balarabe ne ya zo inda nake ya tsaya ganin ina kuka yake tambayata cikin larabci ko akwai taimakon da nake nema? Daga ni har shi ba mu ga sanda Yaya ya fito ba, sai jin hannun sa na yi cikin nawa yana yi wa Balaraben godiya, ya ja ni muka koma daki.
A kujera ya dangwarar da ni, ya tsaya a kaina. Kallo yake kare min daga sama har kasa, kafin cikin kaushin murya ya magantu da cewa.
“What’s wrong with you?”
Chapter 15 · 0% Book details