← Book details Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 33

Sashe 3

Yiwa Kai Hisabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

A bayan Nene na kwana, manne da jikin ta. Da asuba ma bayan mun yi sallah sai da ta kara lallashi na tare da jaddada min yi wa Adda biyayya da hidimta mata, ta sa min albarka ta ce, “In kin kasa karatun boko kada ki damu, ba shi ne tikitin shiga aljanna ba, wanda ki ka iya shi ne wanda zai tserar da ke ranar gobe kiyama”.
Wadannan kalaman na Nene a kan karatu na na boko kullum ina tuna su, suna cire min damuwar nakasu na a kai, suna zame min fitilar rayuwa. Baba ya ce da Adda shi ko su Nabeelah sun dawo, ya riga ya mallaka mata ni har zuwa ranar da za ta yi min aure.
Maganganun su duka shi da matar sa Nene masu karya zuciya ne. Amma a wannan lokaci daga ni har Adda ba mu ankara da muhimmancin su ba. Sai a lokacin da aka shimfide mana gawarwakin su a gaban mu. Sun yi hatsari gab da za su shiga garin Talata-Mafara, Malam Hussaini direba hatta kafarsa da hannayensa sun fita daga jikin sa.

Sabon tashin hankali irin wanda zuciya ba za ta iya fassarawa ba. Rana ce da ba zan taba mancewa da ita ba a kundin tarihin rayuwata. Ranar da na tabbata marainiya ba uwa ba uba, har fiye da su Muhsin. Rayuwa ta dandana mana wani irin daci ni da Addah, da babu madacin da ya kai dacin sa. Hankali na ya bar jiki na, nutsuwa ta kau mun, kadan ya rage in rasa hankali na. Kwana na uku ina sambatu wanda babu komai a cikin sa sai "Nene da Baba". Shekaru na goma sha hudu a daidai wannan lokacin, ranar da na amsa sunan ‘MARAINIYA’ gaba da baya a cikin wani dan takaitaccen lokaci mai kama da kiftawar ido.

*** *** ***
Aka ce mutuwa mai tonon asiri, ba mu tabbatar da wannan ba sai lokacin da kannen mijin Adda su biyu Malam Ilya da da Malam Bilya suka zo addu’ar arba’in din dan uwan su. Bayan an shafa addu’a suka kira Adda falon marigayi. Babu kwane-kwane suka ce ta fiddo duk wata takarda da kowanne kobo da ta san marigayin ya bari za su alkinta wa ‘ya’yan sa, har su yi hankalin daukar takalihun dukiyar su. Sannan in ta amince shi malam Bilya zai aure ta don bai kamata a bar gidan ba namiji ba, in yaso sai ya kwaso sauran iyalin sa daga Dogondaji su dawo gidan da zama.
Hajiya Kilishi ta dade kanta a kasa ba ta ce komai ba, har suka gama duk wani tsare-tsaren su, wanda babu komai a ciki sai hadama da babakere a cikin rigar zumunci. Lokacin da suka matsa da son jin amsar ta sai ta ce, ita a yanzu ba ta da magana, tana cikin alhinin rashin mijin ta da tilon dan uwanta, babu wani rabon gado a gaban ta, tunda gadon nan dai babu mai shi daga ita sai ‘ya’yan ta. Maganar aure kuwa ita da kara yinsa har abada! Shekarun ta arba’in da takwas ta kusa isa ‘menopause’ ba ta bukatar wani aure a rayuwarta.
Za ta yi zaman ‘ya’yanta ne kawai da zaman jiran nata wa’adin. Ba ta da sauran muradi a duniya.
Wadannan dattijai ba su hakura ba, bayan wata uku sai da suka sake dawowa suka ce ba ta isa ba, sai ta fiddo komai sun raba wa ‘ya’yan su gado. Saboda gudun rigima da tashin hankali, Adda ta fiddo kananan kadarorin marigayin ta ba su. Suka dauko malaman karya suka yi kasafce-kasafcensu inda suka samfe komai suka mike, suka ce sai yaran sun yi aure sun zauna waje daya za su ba su.
Aure kuma tunda ta ce ba a yi ita ta jiyo, da ma taimakon ta za su yi. Su rike mata marayun ta a gaban su. Abin ya hada da rashin ilmi, ban da haka ‘yar dukiyar da suka gani suka gigice ba ta kai ko kwatan-kwatan abin da mutum irin Alhaji Atiku ya mallaka ba.
Sun yi waya da Nabeelah a ranar ita da mahaifiyar ta suka yi ta kuka kamar ran su zai fita. Nabeelah ta ce, ita tashin hankalin ta shi ne Maccido na kan hanya, wai surprise zai yi wa Adda shi ya sa bai gaya mata zai zo ba.
Duk halin da Adda ke ciki dole ta murmure ta aro juriya ta dora wa kanta. Ta shiga shirin tarbar Maccido.

Watanni uku da sati biyu kenan da rasuwar Alhaji Atiku Dogondaji, wanda ya yi daidai da cikar Babana da Nene watanni uku cif a gidan da ke jiran kowanne dan Adam. Har zuwa wannan lokacin ban koma daidai ba, bana doguwar magana daga eh sai a’ah, abinci sai Adda ta sani a gaba shi din ma sai mai ruwa-ruwa idan na ji hanjin cikina na raurawa. Duk wannan lukutin jikin nawa ya zaizaye na koma kamar a bushe ni in fadi.
Ni dai na san ina wanka, amma bayan shi ko mai bana shafawa, balle a je ga zancen kwalli da hoda. Adda ce ke takaba, amma kusan tare muke yi. Sati biyu ke nan da gama takabar ta.
Sai da ta tabbatar abincin da ta sa mai aikinta Halima ta taimaka mata ta shirya ya kammala a kan tebir sannan ta fada wanka, ta fito ta sanya kaya masu dan haske wadanda rabon ta da sanya su tun mijin ta na raye. Ta fito falo inda ta tadda mu zaune ni da Muhsin, dawowar sa ke nan daga makaranta ko (uniform) bai cire ba ya ce,
“Addah, unguwa za ki ne?”
Fuskarsa ta nuna jin dadin ganin ta cikin kyakkyawar kama yau. Ta zauna tana fadin, “Ma’u miko min carbi na”. Ba tare da ta bai wa Muhsin amsa ba.
Ko gama rufe bakin ta ba ta yi ba suka tsinkayi sautin sallamar sa cikin muryar sa mai kurdawa har cikin kwakwalwar mutum, ta haifar masa da canjin yanayi. Idan diya mace ce ta rikitata, ta haifar mata da kasala wani lokacin har ta rasa control din kanta.
(Maccido-Attahir).
Chapter 3 · 0% Book details