← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 49

Sashe 9

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isowa cikin garin Sakwa suka ce karo da wani mai amalanke zai fita, tsayar da mashin ɗin Baffi yayi ya fara mishi magana cikin harshen fulatanci
“Don Allah ina ne hanyar makarantar kwana?”
Kwatanta wa Shayibu yayi saboda haka suka miƙe sai Gov'nt Girls College Sakwa.
Tun daga bakin gate Ƴar Iya ta fara sakin murmushi, gani yara Sa'annin ta da check na pink yard wasu na tuƙa ruwa wasu kuma sun tsugunna gaban wata mai Blue Check hakan ya bata dariya tace.
“Kutumar Uba....Aradu akwai kallo”

Baffi ne yaja hannun ta zuwa wajen wasu matasa da suke zaune kan wasu kujeru bakin bishiya.
Gaishe su Baffi yayi Ƴar Iya kuwa ko a jikin ta. Bayan Baffi ya faɗa musu cewa Ƴar shi ya kawo makarantar suka nuna mishi hanyar ofishin Principal.

Sun miƙe zasu wuce ne wani Ƙatoton malami mai ƙaton ciki, gashi gunt, baƙi ƙirin yake ga kuma kanshi ɗan ƙarami kamar an san mishi. Ai kuwa da gudu Ƴar Iya ta fizge hannun ta tana nufar inda yake. Sai da tazo dai-dai da shi ta ƙara rage tsayi tana mishi kallon ƙwaƙwaf... Bai ma lura da ita ba sai da yaji ta kwashe da dariya

“Hhh.....hhhhhhh..hhhhhhh wayyoh ciki na, A'i na baro ki da nace kizo kiga mai kama da Bijimin Baffi hhhhhhh....Kutumar Uba Aradu banbanci shi da Bijimin Baffi ƙaho ne sai jela”

Haka ta ƙara kashewa da wata mahaukaciyar dariyar. A lokacin ne malamin yayi noticing nata ya kuma ji abun da ta faɗa, kunya da ɓacin rai suka sauƙa mishi lokaci ɗaya. Gashi yarinyar da yake so Sahiba Bashir sun zo wucewa ita da abokan ta kuma ya tabbatar taji.

Tuni yayi kan Ƴar Iya yana ayyana ko ƴar uban waye yau sai taci uban ta.

(Nace lallai baka san Ƴar Iya ba ne)

Wata irin damƙa yayi mata kafin ta farga ai kuwa tuni tayi wani juyi tare da murɗe hannun da ya janyo ta da shi. Abun ka da ƙato dama muscles sun mishi yawa tuni jikin yayi tsami gashi ta ƙi sakin shi.

Mamaki ne ya kama shi ganin iri ƙarfi da yarinyar ke da shi gashi ya kasa ƙwacewa. Yanke shawarar ihu yayi ko za'a samu masu taimaka mishi.
“Wayyo Allah jama'a ku kawo ɗauki, innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir....”
Bai kai ga ƙarasa ihun ba Ƴar Iya ta buge bakin shi nan da nan jini ya fara zubowa.

Malaman da ke gindin bishiyar nan ne suka ji ihun ai kuwa suka taho don ganin MEH ya faru. Arba da yarinya ƙarama na riƙe da Mr. Small duk iri girman shi yasa suka shiga ɗimuwa.

Faɗa wasu suka fara mata kan ta sake shi ammah shiru....wanda yayi dai-dai da fitowar Baffi da office ɗin Principal nasu don ya ƙira ta ayi mata interview.

Ɗauke da mamaki a fuskar shi ya daka mata tsawa tuni tayi wulli da hannun Mr. Small Wanda yayi dai-dai da faɗuwar shi ƙasa.

Tana sake shi ta nufi wurin Baffi su kuma malaman suka je don bawa ɗan uwan su agaji.

Bayan sun shiga Principal ya fara mata interview ammah sai ya fahimci bata san komai ba....ABC common Bata sani ba tunawa da bayanin Baban ta yasa ya yanke shawarar kai ta aji ɗaya don kuwa ya san halin yarinyar tunda Baban nata yayi masa bayani.

Babu ɓata lokaci Principal ya ƙira wata Senior tare da nuna mata Ƴar Iya yace ta tafi da ita hostel a Bata room da gado. Ba musu ta miƙawa Ƴar Iya hannu a kan su tafi. Ganin Baffi zai tafi yasa ta arta da gudu wurin babur ɗin.
“Baffi ina zaka je?”
“Zan tafi manah, ba kince kina son birni ba?, toh ki zauna gobe ma zan zo kinji”
Kai ta gyaɗa kamar ta fahimta tare da komawa wurin kayan ta.

Ganin babu kayan ta babu alama yasa ta kwarma ihu tare da sakin ashar.
“Kutumar Buhun uban jakin nan, uban waye ya sace min kaya na?”
Rasa mai bata amsa aka yi da ƙyar Principal yace
“An kai miki shi makwancin ki”
Senior ɗin da ta kai kayan ne ta dawo saboda haka ta lallaɓa ta suka wuce room ɗin da aka bata.

_YAR IYA'S FIRST DAY AT SCHOOL_

Ganin makarantar cike da bishiyoyi yasa ta ɗan ji sauƙi a ranta shiyasa ta fito tana kewaya ko ina, kun san Sunday babu karatu mostly students sukan wanke uniform nasu ne suyi wanka.

Ƴar Iya na cikin tafiya zata hau bishiyar mangwaro da ke ɗan nesa da hostel ɗin nasu taji an dakatar da ita.
“Keeee! dan Bura Ubanki zo nan, uban me kike yi a wajen?” Senior ɗin ta faɗa cike da bada umarni da taƙama.
Cike da ɗumbin mamaki Ƴar Iya ta waiwayo ta kalle ta, cikin ranta tana ayyana wace tsagerar ce ta tare ta yau zata san ta zage ta. Juyawa yayi ta ɗale bishiyar abun ta, yadda take tsalle kuwa kai kace biri ne.

Senior da ta ƙulu da rashin kunyar da sabuwar ɗalibar ta ƙunsa mata wuri ta nema ta zauna tana jiran sauƙowar ta tare da tunani iri-iri akan uƙubar da zata bugawa yarinyar.

Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake.......

IN ANYI COMMENTS ZAN ƘARA MUKU UPDATE ZUWA JIMAWA
INA GODIYA GARE KU MASOYAN LITTAFIN ƳAR IYA, MASU COMMENTS ƊIN NAN DA MASU TAYA NI INA MATUƘAR ALFAHARI DA KU, ALLAH YA BAR ƘAUNA. much Love my esteem fans.

DIAMOND LADY 💎 CE!

SHARE FISABILILLAH.

[4/29, 2:48 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA ‘‘‘‘‘15&16’’’’’

Shiru shiru babu Yarinya ba labarin ta nan fa Senior ta tsorata Allah yasa dai ba ifiritan da ke makarantar bane. Ta juya zata tafi kawai taji sauƙar abu a bayan ta daga sama, wata irin ƙara ta sake yayin da ta kife a ƙasa kamar kwaɗo.

Ba komai bane ya faɗo bayan senior sai Ƴar Iya wacce sai da ta saita bayan nata ta diro a kai.

Ganin tayi wa Senior ɗin illa yasa ta cika bujen ta da iska, bata tsaya ko ina ba sai ɗakin da aka bata. Lokacin kuwa har an fara kiraye-kirayen sallar Azahar. Bata kula kowa ba ganin babu wanda ya kula ta, in fact kowa ma hidimar gaban sa yake sai dai abun da ta fahimta shine fita waje suke yi gabaɗayan su.

Wata senior da taji ana kira da Ajaram taso saitin Ƴar Iya tace
“Ke ba zaki je dining bane ko baki ga lokacin cin abinci yayi ba”
Da yake babu kowa a room ɗin yasa ta fahimci da ita take saboda haka ta zubo mata ƙwala-ƙwalan idanuwan ta alamun bata fahimta ba.

Da yake Ajiram na da sauƙin kai kuma bata cin zalin yara yasa ta ƙara maimaita mata. Ƴar Iya tace
“Meye kuma Dayin?, Ba dai wanda ake lalle ba, to ai ni bana yi Aradu ko a ƙauyen mu”
Mamaki ne ya cika Ajiram lokaci guda kuma ta fahimci yarinyar ƴar ƙauye ce saboda haka ta saki murmushi tace.
“Dining gurin da ake bamu abinci ne a nan, ki tashi muje kada ya ƙare baki samu ba”

Huhuhu! Su Ƴar Iya manya, wani zungureren mamaki ne ya maƙale ta, yau itace wani ke lallaɓa tazo taci abinci, ita da bata da aiki sai ƙwacen na wasu taci shine ake nunawa tausayi. Lokaci ɗaya taji tana ƙaunar matar.

Da niyyar ta shine ta ɗauko zabin ta na wurin Arɗo taci kawai sai taji bari ta ɗauko su ci da wannan matar. A hankali ta ɓaro buhun kayan ta ta janyo ledar zabin. Duk abun da take Ajiram na jiran ta don bata tafi ba, tunanin ta ko dai zata ɗauko wani abun ne.

Ledar ta ɗauko tare da buɗe ta, janyo zabuwa ɗaya tayi ta miƙawa Ajiram, mamaki ne ya cika ta lokaci ɗaya ganin gasasshiyar kaza....
“Gashi muci wannan sai muje Dayin ɗin”
Murmushi Ajiram tayi tana tsintar kanta da zama kusan Ƴar Iya, tare suka cinye ta farkon ita dai ta ƙoshi ammah mutuniyar ta saba saboda haka ta janyo ɗayar.

Tasss ta cinye ɗayar, ita kuwa Ajiram mamaki duk ya cika ta. Bayan ta cinye tace wa Ajiram ɗin ta raka ta Dayin suje suci wancan, a lokacin kuwa har ya kusa ƙarewa saboda haka aka ɗan zuba musu kaɗan kaɗan.

Bata wani damu ba tacinye sannan ta fara waigen inda zata ga wannan baiwar Allah ta ɗazu, tana hango ta ta wuce wurin ta guduuuuuu....
Tare suka dawo da yake room ɗaya suke Ajiram na jan Ƴar Iya da hira ita kuwa ta zage sai bata labari take.

Lokacin kwanciya yayi Ajiram ta taya Mutuniyar hawa nata gadon sannan tayi musu addu'a tare da shafawa Ƴar Iya a jikin ta. Nan da nan bacci ya kwashe su.

Washegari da safe da yake ba kullum ake wanka ba a school ɗin ɗalibai suka fara shiryawa cikin uniform ɗin su, Ajiram ita ta taya Ƴar Iya saka nata tana mitar kayan meyeh wannan. Bayan sun shirya aka tafi classroom.

Assembly aka yi daga nan kowa aka ce ya wuce aji. JSS one shine ajin da aka kai Ƴar Iya, tana shiga ta fara baza ido, ganin kowa yana neman waje ya zauna yasa ita ma ta nemi waje ta zauna kamar mutuniyar kirki.

Malamin su na English ya shigo, kowa ya miƙe ya gaida shi banda Ƴar Iya wacce gabaɗaya hankalin ta na kan jakar da Ajiram ta kawo mata wai Principal yace a bata, cikin zuciyar ta tace ke kika san miye Principal ɗin ma ai.
Chapter 9 · 0% Book details