← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 49

Sashe 39

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da son kawar da zancen Ayrah tace “Allah sarki Hamma Zaki, wallahi Ni yanzu fa tausayi yake bani” ta ƙarasa kamar zata yi kuka.
Fauzah tace “Wallahi kullum sai nayi mafarkin ɗan uwa na, kin san Mom fa kullum sai tayi kuka”
Yesmeen tace “Ai dole tayi, ni kan wannan matar tasa mai siffar aljanun dama daga ganin ta ai shaiɗaniya ce”
“Ke dai kibari Yesmeen, wallahi da Hamma Zaki zai barmu gidan shi zamu koma muci uban shegiya ko kuma a haɗa shi aure kawai da Adda Salma tunda tana son shi”
“Toh ƴan Manzon manyance, ku tashi ku bani wuri munafikan yara, ƙanana da ku kun iya gulma” Muryar granny ce ta katse su.
“Kai don Allah granny, ke matsalar mu dake kenan wollah, don kawai mun jajanta abun dake damun mu” Ayrah ta faɗa tana tura baki.
Baki Granny ta kama da hannunta ɗaya, ɗayan kuma ta riƙe kunkumi tana bin Ayrah da kallo
“Toh rasa kunya ɓeran tanka, kin Isa ƙwarai, to ko ubanki Bello bai isa na faɗa ya faɗa ba, shashasha kawai, shi Mazan ne damuwar ku?”
Fauzah tace “Yi haƙuri ƴar tsohuwar mu me ran ƙarfe, nasan kema dai kina kewar Wannan jikan naki da mace ta ƙwace shi ta hana shi zuwa kallon ki”
Ai jin batun Fauzah sai granny ta ɓare baki tana kuka
“Ƴar nan fauziyya ai dole, wannan shaiɗaniyar matar tasa kullum sai na tofa mata yasin ƙafa goma don ta cuce mu, shegiya mai fuskar aljanu” ta faɗa tana fyace majina da gefen zanin ta.
Khairy da bata fahimtar komai gashi granny da kuma ƴan uwan ta sai ƙwalla suke zubarwa yasa ta ƙarasa tana rungume granny “Ki shiru haka nan granny, Ni nan nayi miki alƙawarin dawo miki da Maza (kamar yadda taji granny ta faɗa) garemu, ƴan uwa na kuyi haƙuri kunji?”

*Hamma zaki da Khairy*
_Ya kuke tunanin za'a kaya, kuyi comment an jima nayi update, Ina son mu kammala littafin nan kwanan nan ne_

COMMENT & SHARE PLEASE

[8/18, 5:46 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA””” “““65&66

Granny tace “Shikenan ɗiyar kirki, na yarda dake sosai, Allah yayi muku albarka”
“Ameen dukan su suka amsa mata” daga nan suka ɗunguma sai part ɗin Mommah. Lokacin Madam Ajimola tazo, dole Khairy ta tsaya yin karatu wanda suke yi a parlourn Granny.

Tafe yake cikin takunshi mai nuna tsantsar haiba da kamala irin tashi. Can ƙasan maƙoshi sallamar tasa ta fita, Madam Ajimola dake ƙoƙarin koyawa Khairy karatu ta ɗago, kasa haɗa ido dashi tayi hakan yasa ta sunkuyar da kai.
“Good Morning sir”
Kai kawai ya ɗaga alamar iya amsar da zai iya bata kenan. Ganin yarinya zaune amma bata yi ko gigin gaisar da shi ba yasa ranshi ɓaci. Cikin ranshi yace
“Koma wacece, I'll teach her a lesson” daga haka ya wuce Bedroom ɗin granny.

Lokacin da ya shiga granny na sallar walaha saboda haka ya fito da niyyar komawa anjima. Sauran parts ɗin gidan yabi ya gaida su kamar yadda ya saba kafin ya koma bedroom ɗin shi yana mamakin wannan ƴar yarinya mai zarra da har zai shiga ta gagara gaida shi sai dai malamar ta.
“silly girl” ya faɗa yana juyawa zuwa ɗaya ɓangaren. Madam Ajimola na gama yi mata Lesson ta wuce abunta. Granny da ta idar da salla ta fito tana faɗin “Maza ina ka shiga ne”
Da kallon mamaki Khairy ke binta, ko ina taga mazan?. “Ke Khairy ina maza?”
“granny wani maza kuma?”
“Ke bana son shiririta, yanzu ya shigo ina sallah ko ya fita ne?”
“Eh ya fita amma ina ga zai dawo”

Bata rufe baki ba taji irin ƙamshin da ya bugi hancinta ɗazu, babu shakka wannan shine mazan granny Kuma Hamma Zakin ƴan uwanta.
A hankali ta ɗago da idonta don kallon mamallakin wannan ƙamshi. Ganin granny ajikinshi tana share ƙwalla yasa ta nufi Bedroom ɗinta.

“Maza sai yau ake ganin idon ka?, Yau wata nawa da auren ka sai yau ka tuna da mu?”
“kiyi haƙuri granny, nasan Ni me laifi ne a wajen ku, Wallahi ban san me yasha kaina ba ne”.
Ya faɗa yana yamutsa fuska alamar maganar da yayi tayi tsayi.
“Ai dama na san wannan matar taka mai kama da tsatson bokaye ita ta raba mu, shikenan na haƙura, ina ita matar taka?”
“Gida can abuja”
“Hohoho dole ma ta dawo nan Adamawa da zama, don bazata raba mu da kai ba ita kuma tana tare da nata iyayen ba”
Cike da ƙosawa da zancen granny yace “wacece wannan yarinyar?”
Washe Baki granny tayi jin an ambaci Khairyn ta.
“Ayyo, ƴar wajena wai?, Ummul Khairy ce sabuwar ƙanwar ka”
Cikin ransa yace “Wannan fitsararriyar?, Ai sai na koya mata hankali”.

“Amma dai tana da taɓin ƙwaƙwalwa?”
“haba maza ya za'ayi kana cin mutuncin yarinya, to bata da taɓin hankali ko kaɗan, ragas take Kamar kai”
Cikin ransa yace “In kuwa ragas take tabbas zan koya mata hankali”.
Cike da jin haushin yadda granny ta nuna son fitsararriyar yarinyar da ko kallo bata isheshi ba yasa yayi mata sallama ya koma ransa babu daɗi yana tunanin ta yadda zai yi maganin ta.

Da yamma sunje part ɗin su Ayrah Adda Salma ta tsokalo Khairy. Suna zaune a parlour suna hirar su wacce rabi da quater akan Hamma Zaki ne, ita dai bata cewa uffan saboda har yanzu bata taɓa ganin fuskarsa ido da ido ba, iyaka dai bata taɓa ganin mutum mai girman jiki kuma mai ɗaukar hankali ba irinsa.
“Kai dallah ku rufawa mutane baki, idiots. Kun wani saka wannan gidahumar baƙauyiyar kuna mata zancen Hamma Zaki, oya ku tashi ku bar parlourn nan”
Adda Salma ta faɗa tana cilla musu harara, cike da kallon da ke nuna ƙyama.

Tunda Khairy take baa taɓa ci mata fuska irin na yau ba, kuma yau ne karo na farko a rayuwarta da wani ya taɓa nuna ƙyamarta. Har ta juya zata fita ta juyo ta kalli Adda Salma tace “Kada ki ƙara ƙira na da bagidajiya, ƙauye kuma tushen kowane” daga haka ta saka kai zata fita, babu tsammani taji hannun Adda Salma ya damƙi wuyanta. Duk abinda suke Mommah na kallon su, ita kanta ta gaji da mugun hali irin na Salma, shiyasa ko da yarinyar tayi mata rashin kunya bata ce komai ba.

A hasale Khairy ta juya tana taskawa Adda Salma Mari, Marin da tunda Mommah tahaife ta bata taɓa jin irin sa ba coz sai da tayi loosing sight ɗin ta na wani lokacin.
Da yatsa take nuna ta tace “Wannan shine karo na farko da kika saka na karyar alƙawarin da na ɗaukar wa Iya ta, kin sa haƙuri na ya ƙare, to Wallahi ki fita sabga ta”
Daga haka ta arta a wani irin speed kamar wata iska, bata tsaya ko ina ba sai Bedroom ɗin ta, tana isa ta kulle ta faɗa kan bed sai wani irin numfashi take fitarwa.

Gabaɗayan su basu bi ta kan Adda Salma dake zaune a ƙasa ba dirshan, sai ma bin bayan Khairy da suka yi. Hankalin su yayi mummunan tashi, gurnanin da ke tashi daga rufaffen ɗakin ya matuƙar razana su. Granny kuwa kuka take tana faɗin “Kuje ku ƙira maza yazo, nashiga uku ni Aishatu, ke Najma karɓi waya ta ki ƙira min Daddyn ku”
Da ƙyar ta laluɓo number Daddy, cikin tashin hankali ya shigo gidan, ko parking bai daidaita ba ya fito ya nufi part ɗin granny. Tun daga bakin part ɗin yake jin gurnanin kamar an sake mayunwacin zaki.

Ƙarasawa yayi, bai gama shiga tashin hankali ba sai da ya ga Hajiyarsu na kuka.
“Maza ɗan nan a fito mun da yarinya, in ba haka ba zan bar gidan nan nima”
Cikin ɗimuwa ya tambayi Fauzah dake kuka shabe-shabe coz tunda take bata taɓa jin irin wannan kukan ba. Bayani tayi masa, cikin ɓacin rai yace “Shikenan yanzu ya za'a yi ta fito?”
Granny tace “Ka ƙira min maza nasan shi kaɗai ne zai fito da ita, wallahi yarinyar nan ta illata sai na saɓa muku”
Daddy wayarsa ya ɗauko ya ƙira Hamma Zaki, thank God Yana ma gidan ashe.

Kasancewarsa maras son hayaniya yasa gurnanin nata ya fara sauƙar mishi da ciwon kai, a haka ya daure ya ƙaraso zuwa ƙiran Daddy.
Nan yayi masa bayani kamar yadda Fauzah tayi masa. Takaici ne ya kama Hamma Zaki amma ya dake yace “Daddy to a ƙira Sheikh Imam mana”
Murmushi Daddyn yayi don shi har ga Allah kansa ya kulle.
Number ya Sheikh ya danna amma bata shiga, hakan yasa ya ƙarasa bakin ƙofar yana ƙiran sunan ta
“Khairy, Khairy”
Babu alamun za'a amsa kuma gurnanin bai daina fita ba. Cikin ransa ya ɗauki aniyar hada ta da Sheikh Imam ko ma meyeh in sha Allah ba zai gagare shi ba.

Har lokacin azahar ya kusa wucewa shiru, hakan yasa Nenne lallaɓa su suje suyi sallah. Bayan tafiyar su kowa zuciyar sa babu daɗi Nenne ta ƙaraso jikin ƙofar ta kafa kanta ta fara magana “Yarinya ta kiyi haƙuri ki buɗe kinji, Kinga ni da grannyn ku ga ƴan uwanki duk muna cikin damuwa, ki taimaka ki buɗe”
Cikin wata razananniyar murya da amon ta ya zaga ko ina na gidan tace “Meyesa Nenne, ki tafi kema, ba ita bace, ku tafi in mun gaji zata buɗe”
Jikin Nenne karkarwa kawai yake, cikin ƙarfin hali tace “Toh kada ku cutar da ita don Allah”
Tsawa aka daka mata wanda sai da kowacce kusurwa ta gidan ta jijjiga.
“keeee, ki tashi ki tafi muka ce, wannan ba damuwar ki bane, tun tana ciki muke tare da ita, da munyi niyyar cutar da ita da munyi”
Ai tun kafin maganar ta kai karshe Nenne ta fice da gudu, duk gidan a ɗimauce suke, musamman yadda Muryar ke tashi ga kuma tsawar da ta jijjiga ginin gidan.
Allah Sarki granny kuka take, ta kasa cin abincin ma, gwanda yaran an saka su dole sun ci.
Chapter 39 · 0% Book details