← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 49

Sashe 44

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wass-wasa tafiya ake yi amma taƙi ƙarewa, duk tunaninsu ba wani nisa daga nan zuwa can saboda sun saba flight suke be koyaushe. Isarsu Bauchi suka yada zango a wani restaurant, bayan sun ci abinci suka siya tsaraba a wani wuri Mafi kusa daga nan suka nausa bisa titi. Tafiyar awanni uku suka yi suka isa Azare, basu ƙara 1hour ba suka iso Shira, hanyar kam babu daɗi saboda ramukan gashi duk jikinsu yaji.

Ai tunda suka miƙi hanyar Gallara Khairy fa hankali ya tashi, sai uban zuba take musu tana basu labarin tana zuwa wurin nan ita da ƙawarta A'i. Hango gidajen zana da kuma shanu da suka gani suna kiwo yasa suka fahimci an iso, saboda haka suka yi parking motarsu a dai-dai bakin kasuwa.
Mutane sai kallonsu suke yi suna mamaki, yara kuwa sai ihu suke suna faɗin “Yeye yaye wallahi wannan sunanta mota, in kaje birni zaka gansu, ahayye mota a Gallara”.

Su dai murmushi kawai suke yi yayinda Khairy ke musu jagora sai dai duk wajen wanda suka wuce cikin ƴan kasuwar sai tayi musu magana yayinda basa gane ta har sai ta bar wurin. Ai kafin isarsu gidan iya tuni zance ya isa mata cewa Ƴar Iya tazo wallahi ita ce ta zama ƴar birni.

Dai-dai ƙofar gidan Iya taja birki yayinda take tunawa da asalinta, a zahiri kuma kallonsu Sheikh Imam take yi. Granny tace “Ummul-khairy nan ne?”
“Eh granny nan ne”
Granny tace “Wallahi har na tuna lokacin da muke kiwo, mu shiga yaran nan”.
Da sallama a bakinsu suka shiga, Lale maraba, sannunku da zuwa, baƙi daga birni”. Ta ƙarasa tana shimfiɗa musu sabuwar bujukurar tabarma. “Maraba ku zauna” abun mamaki ko kallon Khairy bata yi ba. Da gudu Khairy taje ta rungume Iyar tana faɗin “Haba Iya ta kina gani na shine ko ki ɗan rungume ni?”
Sai a lokacin Iya ta gane cewa shalelenta ce ai tuni ta fara sharar ƙwalla tana faɗin
“Shalelen Iya kece?” lokaci ɗaya kuma ta sake ta tana ja da baya tare da ƙare mata kallo. Kamar wadda aka tsikara ta ƙara rungume Khairyn tana sakin kuka.
“Yau Allah yayi Shalele na ta waiwaye ni, Allah na gode maka ni Shatu”.
Tunawa tayi da tare dasu granny suke ta saki Iyan tace “Iya ga baƙi nan baku ko gaisa ba”
“Ai, wallahi duk na Shafa'a tunda na ganki, kuyi haƙuri, sannunku da zuwa maraba lale”
Granny tace “Yauwa sannu”
“Ina wuni ina gajiya, ya hanya kuma”
“Alhamdulillahi” inji granny “Tare muke da baƙi muma”
“Kuma kuka barsu a waje, ke Shalelen Iya shigo da su mana”

Bayan sun shigo ne aka sake buɗe babin gaisuwa. Nan Khairy ta sanar da Iya waɗannan sune Sabbin iyayenta, ” abun har abun dariya sai da aka ƙara gaisawa sai godiya iya ke zuba musu. Gyaran murya Sheikh Imam yayi yace “To dama dai akwai abunda ya kawo mu, amma kafin nan idan mai gidan yana kusa to da shi sai muyi muku bayani”
“Ah ai Mallam kam baya nan, sai dai ke Shalele kuje ku ƙira shi mana”
Tare da su Ayrah suka fita sai zuba take musu tana nuna musu wurare tare da tuna memories ɗin ta a wurin. Dariya su dai suke yi tare da tabbatar da labarin da ta basu a baya. Duk inda suka wuce kallonsu ake manya da yara kowa sai gaida Ƴar Iya ake ana mata maraba da zuwa. Mutauniyar kuwa sai wani shan ƙamshi take ita ƴar birni.

Bayan sun dawo daga ƙiran Baffi ne kuma suka tarar da Damammiyar fura da nono ƙwarya-ƙwarya wanda suma a nan suka baje suna sha ana ta zance kamar an daɗe da sanin juna. Ita dai Khairy mamaki take yada suke shan furar hankalinsu kwance ba tare da nuna ƙyamarsu ba. Nan ƙima da darajarsu ta ƙaru a idonta.

Bayan Baffi yazo ne aka sake gaisawa, nan yake ta sauƙe musu damin godiya da irin sauyin da jikartasa ta samu. Daga gaishe-gaishe Daddy yace '“Khairy ki ja ƴan uwanki kuje ku yawata gari ko?”
Ai tunkan ya gama tace “To Daddy sai anjima, kai ku tashi muje cikin gari”.

Nan suka nausa cikin Gallara sai kewayawa suke. Dai-dai wajen Bala mai kifi ta tsaya tace “Ku zo mu gaisa da Bala ”
Suna ƙarasawa suka yi sallama, bala sai kallonsu yake yana ƙarawa ganin zuƙa-zuƙan ƴan mata kamar daga aljanna ya washe baki. Gaisawa suka yi yayinda hakima ke zaune akan benci. Cike da yatsina tace “Bala baka gane Ni bane?”
“A'ah Hajiya ku da ba ƴan gari ba kuma taya zan sanku?”
Dariya ta sheƙe da ita su kuma suka zuba mata ido don iya zamansu da Khairy basu taɓa ganin tayi irin wannan dariya ba. Tsagaitawa tayi tace “Bala ka manta Ni kake nufi, idan na kwashe kifin naka zaka gane Ƴar Iya ce kenan” ta ƙarasa tana kai dubanta ga kifin dake tashi da ƙamshi.
Ƙwalalo ido Bala yayi yace “Ai ban ganeki bane Ƴar Iya, ina ni ina mantawa dake?, Yaushe a garin”
Murmushi tayi tace “Bamu daɗe da isowa ba, waɗannan ƴan uwa na ne”
“To sannu da gajiyar hanya, bari a saka muku kifin”
Ayra tace “A'ah ka bar abunka in mun koma zamu fito da kuɗi sai mu siya”
Hararar ta Khairy tayi tace “Kaga Bala zuba mana” jiki na rawa kuwa ya zuba musu ya miƙa musu ledar. Khairy ce ta amsa daganan suka yi masa sallama suka yi gaba.

Ganin gidan Halima yasa tace “kuzo mu shiga gidan ƙawa ta Halima mu gaisa sai mu koma gida ko?”
Halima tayi mamaki ganin ƴan gayu a gidanta don ita bata ma gane Ƴar Iya ba sai da tace mata “Ƴar Iyace” salallami Halima ta fara tana faɗin “Ikon Allah, Ƴar Iya ke kika zama haka”
Murmushi tayi mata tace “Ƙwarai kuwa Halima, nice dai wannan rigimammiyar”
Dariya suka kwashe da ita Halima tace “Gaskiya kin canza sosai don ban gane ku ba, wallahi kamar wata ɗiyar Indiyawa kin ganki kuwa? Sauran kuma su waye halan”
“Waɗannan sune ƴan uwa na na can birni, Ayrah, yesmeen sai kuma Fauzah”
Halima tace “Sannunku da zuwa, bari na dafa muku taliya nasan dai da kina son ƴar murji”
“Ai kuwa har yanzu ina so, ammah zamu koma gida yanzu, ma dawo wataƙila kafin mu tafi”
Halima tace “Haba ƴar iya, to zan aiko muku can gidan Iyar”
Daga nan suka koma gida.

Can gida kuma bayan fitar su ne Daddy yayi wa Baffi bayanin dalilin zuwan su, ammah kafin nan ance waƙa a bakin mai ita tafi daɗi, saboda haka Sheikh Imam yayi masa bayanin komai da komai.
Baffi har da hawayensa yace “Kai amma Allah ya saka muku da alkhairi, wallahi yau naji daɗin da rabona da jinsa tun haihuwar shi uban yarinyar! Mun gode sosai, yanzu dai bari naje na sanar da Arɗo zuwanku sai a buɗe masauƙin ku tunda sai zuwa gobe ko jibi zaku wuce.”

Bayan Baffi ya sanar da Arɗo, tuni aka buɗe musu gidan bakin wanda yake ɗauke da ɗakuna biyar ginin block. Sai da aka gyara tsaf tukun suka wuce Fada, sai wajen takwas na dare mazajen suka wuce. Abinci kuwa daga gidan Arɗo aka kawo musu, kuma sunci suna ta yaba karamci iri. Na mutanen ƙauyen.

Washegari da sassafe aka aiko da abinci daga gidan Arɗo, Shinkafa ce da miya sai kuma gasassun kaji da kuma Damammiyar fura da nono. Bayan sun karya suka yi wanka daga nan akace su Ayrah su tafi can gidan Iya su kaiwa Khairy abinci, daga nan kuma su sanar da Baffi cewa suna jiransu a gidan.

Yaron da suka gani a waje suka tambaya ya raka su gidansu Ƴar Iya yace “Tab, ku kuwa me zai kai ku gidan nan bayan Ƴar Iya ta dawo, to Aradu nidai duk abunda ta muku kada kuce Sa'idu ne ya raka ku”
Dariya suka yi kamar ba gobe, suka ce masa “Eh ya raka su mana babu damuwa ai ba zasu ce shi ya raka su ba.

Nan Sa'idu ya raka su yana ta basu labarin ƴar Iya har da labarin ranar da ta ganshi da kaji zai je ya sayar ta ƙwace ta yanka da ta yanka kuma sai ta bashi wai yaje gida a dafa, ta san duk su ma na gidan kwanɗayin naman suke yi. Yace “Ai kuwa ranar naci duka duk da ba laifi na bane, kawai da dare sai ga ƴar Iya wai a bata rabonta, daga nan aka ce babu nan masifa ta tashi wai ya za'a yi tayi musu sanadin dadi kuma suci su kaɗai?, Sai da Baffan mu ya bata kaza ɗaya ta tafi”
Me su Fauzah zasu yi in banda dariya. Da suka iso ne suka ce masa ai tare suka zo da Ƴar Iya, daga nan suka shiga. Bayan sun gaisa da iya suka miƙa mata abincin don sun san ba lallai Khairy ta tashi ba. Fauzah tace “Iya ina ne ɗakinta, don na san ba lallai ta tashi ba”
“Ina kuwa zan tashi tunda Fauzah bata zo ta tashe ni ba” ta faɗa tana cillawa Fauzah harara. Dariya suka kwashe da ita suna faɗin
“Kinga abinci muka kawo miki ba komai ba, in Baki ci sai mu koma da shi”
Da sauri tace “Yi haƙuri Ƴar uwata mai hanjin lagwani, bani abincin”
Iya ce ta miƙa mata tana murmurshi, sun matuƙar burge ta ba kaɗan ba.

Ayrah ce tace “Au Iya, wai a sanar da Baffi su haɗu dasu Daddy tare da Ƴar Iya”
Harara ta banka mata tace “In zaki ƙira Ni da Khairy na to, kar ki ƙara ce min Ƴar Iya”
Dariya suka yi ita dai iya cewa tayi “Ke Shalele ai ba'a manta da, maza kici ku wuce Kinga baffin ki ya riga da ya shirya tun ɗazu”
Da “To ta amsa tana cin abincin, tas ta cinye daga nan kuma tayiwa Baffi magana cewa ta shirya.

_Naga alama Fans so kuke na rage post, ko dai labarin ya daina burge ku ne😔😣, gaskiya da sakel, in bazaku ke yin comments ba zan ajiye alƙalami na._
_Na gode_
Chapter 44 · 0% Book details