← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 49

Sashe 15

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna isa duk suka dire haka Ƴar Iya ma tayi ganin yadda suka yi. Kallon su tayi tace
“Ina Baffi?”
Banza suka yi mata yayin da biyu daga ciki suka fizgo hannun ta, tana turjewa suna ja har suka isa ciki. Da yake an riga an musu bayanin me zasu yi tuni suka shigar da ita Cell. Fitowa suka yi don su nemo abun da zasu hukunta ta da shi bayan sun sakawa ƙofar kwaɗo da key.

Few minutes suka dawo ɗauke da Koboko (Dorina) irin wacce ake jibgar Dawaki da ita, suka haɗo da bucket cike da ruwan sanyi har wani tururi yake yana fitar da raɓa.

Ƴar Iya da ke cikin Cell hankalin ta baya kan su duk tunanin ta Baffi zasu ƙira mata. Har suka buɗe ƙofar bata sani ba, babu zato babu tsammani police ɗaya ya janye Hijabin check ɗin ta, tuni ta fito daga duniyar tunani ta fuskanci duniyar asali. Tana juyowa kuwa ɗayan ya fizge rigar ta da sauri yayin da ɗayan ya zame wandon.

Tsabar mamaki da ya cika ta rasa me zata yi ma tayi.
“Kutumar Uba, me nayi muku zaku cire min kaya na?, Dama ba gun Baffi zaku Kaini ba ku Ƴan Iska ne?”

Bata aune ba taji ruwan sanyi a jikin ta...tuni ta fara rawar sanyi, yo ita wankan ma yaushe tayi shi ballantana ma da ruwa irin wannan. Har abun tausayi yadda take rawar sanyin ammah su basu ji ba, wani bucket ɗin suka ƙara janyowa suka ƙara tsula mata shi tas.

(Toh fah Ƴar Iya yau kin gamu da gamon ki).

Sai da suka tabbatar sanyin ya ratsa ta suka ciro dorinonin su suka fara sharɓa mata, irin yanayin da take ci ba zata iya ƙwatar kanta ba saboda zazzaɓin da ya rufe ta lokacin ɗaya.

Dukan ta suke yi su biyu da dorinonin su tun tana ihu har Muryar ta ta dishe ta daina fita da kai. Duk da haka maimakon su sarara mata saboda ƙarancin shekaru irin nata sai suka ci gaba da dukan ta har sai da ta daina motsi.

(ALLAH SARKI, ƳAR IYA AN MUTU)

A haka suka fice suka barta. Ta share kusan awa biyu zuwa uku a suke kafin ta farfaɗo, lokacin kuma zazzaɓin da take ji ya sake ta tana buɗe idon ta ya sauƙa a kan baƙin ɗakin da take, nan ta fara tariyo abun da ya faru da ita.

Babu shiri ta fara miƙewa, a hankali ta janyo wandon ta da har ya bushe da kuma rigar ta ta ƙwama, bata ƙara bi takan hijabin ba ta fara ƙoƙarin buɗe ƙofar sai dai ƙyam ƙofa taƙi buɗuwa alamun akwai padlock jiki. Ba tare da ta damu ba ta fara jan ƙofar da iyakar ƙarfin ta.

Kyawawan ja guda uku tayi lock ɗin jikin ƙofar ya ɓalle, wangalewa tayi ta fito. A reception ta fara tarar da wasu polisawa saboda haka tayi kansu ba tare da ɓaga lokaci ba. Wani katako ta gani a gefe ai kuwa ta wawuro shi tayi kan su.

Tsabar mamaki da jin kai irin na polisawa suka ƙame suna jiran ganin ƙarshen iskancin yarinyar. Gani suke yi kamar ƙaramar mahaukaciya ce shiyasa kowa yayi ƙyam.

Ba tare da wani tunani ba Ƴar Iya ta sa hannu cikin aljihun ta da ta cika shi da yashi ta watsa a fuskar su. Nan fa suka farga zasu fara guduwa, ƙara ciko hannun ta tayi ta watsa musu.

Sai da ta tabbatar idanuwan su sun raunana ta janyo na baki-baki tare da buga mishi katakon a ƙafar hagu, ta juyar da shi dama ta ƙara buga mishi nan da nan ya cilla ƙara tare da faɗuwa yana sowa.
“Wayyo ƙafa ta na shiga uku wayyoh Allah wayyoh shikenan ta karya Ni wayyo”

Jin ihun da ɗan uwan su ke yi yasa suka far lalume zasu buɗe office ɗin da ke kusa sai dai ina ta riga ta far musu da shiri.

Haka ta ringa bugun ƙafafuwan su da katako tana yasar da su, polisawan da ke bakin Gate ne suka jiyo ihu nan da nan suka shigo ciki don ganin me yake faruwa.

Kafin shigowar su kuwa ta gano fuskar mugayen da suka buge ta ai kuwa tayi kan na farko. Hannun sa na dama ta samu ta buga mishi katakon da ƙarfi sannan na hagu daga nan ta buge masa ƙafafuwa kamar yadda ta bugawa sauran.

Haka ta jawo ɗayan shima ta fara bugun shi kamar yadda tayi wa ɗayan sannan ta bar shi ƙasa ta dawo gefe tana maida numfashi.

Ganin aika-aikar da yarinyar tayi yasa duk suka fara jin shakkun ta. Kallon su tayi tace.
“In ba zaku kai ni gun Baffi na ba to ku mayar da ni sukul ni wurin Iya ta zan koma Aradu birni duk mungaye ne”
Kuka ta raushe da shi kamar ba ita ce wacce ta nakasa waɗannan tarin ƴan sanda da sun kai takwas ba.

A gaggauce suka fara kwasar ƴan sandan suna jera su cikin mota ba tare da sun bi ta kan Ƴar Iya ba. Kai tsaye asibiti suka wuce a nan aka tabbatar musu da cewa duk sun samu karaya a ƙafafuwan su biyu biyu sai waɗannan biyun da suka karye a hannayen su.

Ƙiran DPO suka yi suka sanar da shi, nan da nan shima ya tsorata da al'amarin yarinyar yace su mayar da ita makarantar su kafin ya zo asibitin zasu yi magana da shugaban makarantar su.

Ba musu da suka koma police station suka nemo Ƴar Iya suka saka ta a mota sai school.................

Ina godiya sosai da addu'oin ku masoya na, masu ƙira da masu tura saƙo duk na gode Allah ya bar ƙauna. Babu daɗin yadda kuka damu da Ni, ina matuƙar son ku da yawa da yawa.

MU HAƊU GOBE DON JIN YADDA ZATA KAYA.
KUN JI ƘUDURIN ƳAR IYA NA KOMAWA GUN IYAR TA DA BAFFI BAYAN TA KWASHI KASHI GURIN POLISAWA.
TOH FAH, GA KUMA DAI AN FARA SAMUN SAUYI TA ƁULLO DA TSIYA.

KU CI GAVA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY 💎 DON NISHAƊANTUWA DA KUMA WA'AZANTUWA.

DIAMOND LADY 💎 CE
TOH ƳAR IYA NACE ALLAH YA TAIMAKA.

COMMENT AND SHARE FISABILILLAH!

[5/2, 9:03 PM] 💎Diamond Bhatool💎:
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA ‘‘‘‘‘25&26’’’’’

[Annabi tsira da aminci su ƙara tabbata gare shi yace: «Akwai wasu kalmomi guda biyu masu soyuwa wurin Ubangiji, masu sauƙi akan harshe, masu nauyi akan mizani, sune _subhanallahi wabihamdihi subhanallahil azeem». Bukhari da Muslim suka ruwaito.

Ya ke Ƴar uwa mai albarka ki lazimci furta waɗannan kalmomi da basu da nauyi da wahala wurin faɗi domin mizanin ki ya nauyaya ranar sakamako]

Ba musu suna komawa police station suka Iya suka saka ta a mota sai school.

Kafin Isar su DPO ya ƙira Principal, ranshi a ɓace bayan Principal yayi picking call ɗin ya fara magana
“Haba Misbahu, fisabilillahi wa rasulihi me ka aikata haka?”
Kwantar da murya Principal yayi yace
“I'm sorry sir, wallahi an samu matsala ne”
“Matsala kake cewa eh, matsala koh?, To bari kaji in faɗi maka Yarinyar nan ba full mutum bace”
“Ban gane ba full mutum bace, kaga kofato ne a ƙafarta” Principal ya faɗa yana rarraba idanuwa.

Jin batun Principal yasa ran DPO ƙara ɓaci yace
“Eh kofato kake magana Misbahu?, Ana maka magana ta aika-aikar da yarinyar tayi kana batun kofato?”
“I'm sorry sir, kayi haƙuri ka faɗa min me tayi don Allah” Principal ya faɗa yana kwantar da murya.
“Toh bari kaji na faɗa maka yanzu polisawa takwas ne a karye, shida ƙafafuwan su biyu kuma hannu da ƙafa” ya faɗa cike da ƙosawa da jin zancen.

Principal da yabi ya ɗimauce, rasa abun faɗa yayi sai kawai yayi shiru.
“Ohk ba zaka ce komai ba Misbahu, lemme hang off the call” ya faɗa cikin hasala.
“Aaah ehma sir mamaki kawai nake yi wallahi, how can that small creature defeat nearly 8police officers?, Da farko ina tunanin dabara ce da ita ammah yanzu na gano tabbas ba mutum ɗin bace.”

Nan Principal ya bawa DPO dabarin Ƴar Iya Tun ranar zuwan ta zuwa wannan lokaci. Cike da fargaban abun da zai ƙara faruwa DPO ya bawa Principal shawara kan ya mayar da ita gida lallai-lallai in ba haka ba duk matsalar da ya shiga shi ya jawo ma kan shi.

Yana katse ƙiran ya ƙira Baffi kan cewa ana neman shi da gaggawa. Duk da cewa yammaci ne hakan bai hana shi amsawa da Toh ba. Nan da nan ya ƙira Shayibu don ya kai shi makarantar.

★★★★★★★★★

*ƳAR IYA POV*

Tun kafin motar ta gama daidaita tsayuwa Ƴar Iya dire tana wani muzurai.
Da gudu ta arta sai hostel ɗin su, tana shiga ta faɗa kan Aunty Ajiram dake zaune alamun karatu ta gama.
Kukan da take yi kuwa har abun tausayi nan fa kowa ya zubowa Angel Ido ganin. Yadda take kuka bilhaƙƙi, wasu na tunanin taci wahala ne wurin polisawa wasu kuma suna tunanin ta cutar da polisawan. Kowa dai jira yake yaji me ya faru haka.

“Aishatu?” Aunty Ajiram ta ƙira ta cikin sanyin murya. Kukan da take yi ta ɗan tsagaita tana sauƙe ajiyar zuciya.
“Aishatu me ya same ki kike kuka haka?”
Shiru tayi in banda ajihae zuciya babu abinda take sauƙewa. Sai da ta koma dai-dai ta fara ƙoƙarin cire rigar ta babu ko ɓata lokaci, tana cirewa zanen dorinar da ta sha wurin polisawa ya bayyana.

Ƙwalalo idanuwan su mutanen da ke room ɗin suka yi. Aunty Ajiram da ta rikice ganin irin shafin bulalar yasa hawaye fara zubo mata. Cikin raunatacciyar murya tace
“Aishatu dukan ki suka yi?”
Sai a lokacin Ƴar Iya ta samu bakin magana.
“Ni wurin Iya na zan koma Aradu, duk Ƴan birni mugaye ne saboda haka na haƙura yanzu da ABCD ɗin in na ƙara girma a can ƙauyen mu sai na dawo.”

“Yi haƙuri A'ishah kiyi zamanki, babu wanda ya isa ya ƙara taɓa ki har ji gama. In Kika koma wurin Iya yi ba zaki zama Ƴar Gayu ba”
Chapter 15 · 0% Book details