← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 49

Sashe 40

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adda Salma ana can ana zaryar shiga toilet, don tunda ta fara jin wannan sautin cikinta ya juya, ga kuma wani surutu da ake yi mata a cikin kunne, gashi kowa ya gudu ya barta ita kaɗai, kuka take kamar zata mutu amma babu mai rarrashi. Tayi da-na-sanin tsanar yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Gashi yanzu ta jawowa kanta, Mommah sai ta hukunta ta, gashi kuma sai ta shiga uku da bareɗeɗen granny.
Da haka tayi sallah tana roƙon Allah ya kawo abun da sauƙi.

Sai wajajen maghrib gurnanin ya lufa, sannu A hankali kuma ya disashe kamar ba a gidan ba. Can kuma sai suka ji ƙarar ƙofa ƙiiiii, Khairy ce idon ta a kumbure, fuskar nan tayi jawur da ita. Dukkan su kanta suka yi suna rungume ta. Granny ta janye ta gefenta tace “Haba ɗiyar nan, kiyi haƙuri faɗa min wadda ya taɓa ki”
Nenne tace “Ysnzu dai ba wannan ba Hajiya, tayi sallah taci abinci”
Babu musu tayi sallarta kamar yadda ta saba. Granny da kanta tayi feeding ɗin ta, ƴan uwanta kuwa na kewaye da ita don har ga Allah su suna jinta a jikin su.

Ɓangaren Hamma Zaki abun ya ɗaure masa kai cikin ransa yake faɗin “Dama nasan yarinyar nan ba lafiya take ba granny ta kafe har take kwatanta lafiya ta da tata” yamutsa fuska yayi yace “So disgusting”.
Ƙiran pretty ne ya dawo da shi daga duniyar da ya dulmiya, tsaki yayi ya ɗaga.
“Aliyu shine ko kira na bazaka yi ba saboda kana tare da ahalin ka?”
A hankali yace “Kinga Nabila meyasa kike hakane, ke da ko nuna kulawarki gare Ni bakya yi don yanzu ina samun kulawa sai ki ɗaga hankalinki”
Cikin ɗaga murya tace “Dakata Aliyu, iyayenka sun fini ai?, Gaskiya ka dawo ma in zaka dawo don ba zaka shiga hakki naba” tsaki yaja Yana hanging call ɗin. Cikin ranshi yana tunanin meyasa yarinyar ta raina shi, tabbas sai ya saita ta.

Da daddare Daddy ya ƙara gwada numbern Sheikh Imam, and luckily ya same shi, bayan sun gaisa cike da mutuntawa yake sanar da shi game da Khairy, da irin yadda tayi yinin yau.
Sheikh Imam yace “Tabbas akwai abun dubawa a game da yarinyar, sai dai bana Nigeria yanzu haka, kuma zan kai wani satin kafin na dawo,amma da na dawo in Sha Allah zan taimaka da taimakon Ubangiji mu ceto yarinyar nan.”
“Yauwah ya Sheikh, Allah ya dawo da kai lafiya, na gode sosai”
“Babu godiya tsakanin mu, sai na dawo, kafin nan ake yawan karanta Alqur'ani a wurin da take, kuma a guji duk wani abu da zai tada hankalin ta na wannan lokaci”
“In sha Allah za'a kiyaye”
Daga nan suka yi sallama.

Nan yake sanar da Mom akan yadda suka yi da Sheikh Imam, da kuma shawarar da yanke idan Sheikh Imam ɗin ya dawo a haɗa shi da Alee, don Yana da tabbacin akwai sihiri a tattare da shi. Mom taji daɗin hakan kuma ta shawarci Daddy a kan Hamma Zakin ya dawo Adamawa da aikin gabaɗaya don hakan ne kaɗai kwanciyar hankalin su.

_Toh Fans, ya kuke tunanin wasan zai kaya?, mom da Daddy suna yunƙurin lalata shirinta, ko kuna tunanin zata yadda kuwa?, Ya kuke tunanin haɗuwar Hamma Zaki da Pretty?, Kuci gaba da bibiyar alƙalamin diamond bhatool ta hanya yimin comments da share_

[8/21, 11:00 PM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🌸🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA “““67&68”””

Sheikh Imam yasha wahala ƙwarai dagaske kafin ɗaya daga cikin shaiɗanun suka amince da batun shi.
Gyaran murya yayi ya fara magana kamar haka:
“Mu ma ba yin kanmu bane, mun kasance muna aiki da wani bil'adama wanda yake aikin bokanci a can Gallara. Hatsabibin boka ne wanda ba abinda baya iyawa da taimakon shaiɗanu.”

“Wata rana, shekaru goma sha biyar da suka gabata, wata mata mai suna Zaliha taje ga bokan don yayi mata aiki. Tana son a raba auren Wani mutum mai suna Umaru da matarsa Barira, wanda hakan ba abu ne da zai yiwu ba. Bayan sanar da ita da hakan da boka yayi, bata sare ba tace da shi yayi yadda yake ganin zai yi don ita so take ya aure ta. Boka yace ba zai yiwu ba saboda tauraron matar na da matuƙar ƙarfi, kashe ta ba abu mai sauƙi bane. Ammah akwai mafita, dole zata sadaukar da jinin yarinya wacce zasu sarrafa, sannan kuma zata sadaukar da mahaifarta ga baƙin aljani. Duk da haka matar bata sare ba ta amince da hakan. Boka yayi mata alƙawarin zai kashe matar kuma zai haɗa aurenta da Umaru”.

“Bayan wani lokaci taji shiru sai ta dawo wurin bokan, take masa ƙorafin ya taji shiru?, A lokacin ne kuma boka yake sanar da ita ai Barira na da ciki, amma kuma da zarar ta rabu da cikin kashe ta zai zama abu mai sauƙi. Zaliha tayi murna sosai saboda haka bata yi ƙasa a guiwa ba duk bayan sati sai ta ziyarci boka yayi mu'amala da ita. Bayan an haife yarinyar, wacce boka ya musanya hannun ta da hannun ɗan guigui, sai ya bawa Zaliha mutunmutumi wanda da shi zata hallaka Barira. Kamar yadda ya bata haka tayi amfani da shi, ta soka allura a jiki, nan Barira ta fara jinya, ta soka na biyu, jinya tayi tsamari, tana soka na ukun Barira tace ga garinku nan, a ranar kuma boka ya zuba tsantar soyayyar Zaliha cikin ran Umaru, tun a ranar ya fara samun uwarsa cewa shi aure zai yi, sati da mutuwar Barira kuwa ya auro ” Zaliha wacce ta mallake shi, bashi da ikon yin abu sai da izinin ta”.

“A lokacin da Barira ta fara jinya, sanin cewa Umaru mutum ne wanda zai iya wargaza aikin, yasa boka ya tura masa shaiɗanu ciki har da Mantau, gaba ɗaya ya manta da ita, har tayi jinya ta rasu kai har yanzu da nake maka magana Umaru bai san mutuwar Barira ba. Ranar da Barira ta mutu ranar boka ya amshi mahaifar Zaliha kamar yadda suka yi alƙawari. Nan kuma boka ya binciko wannan yarinya ta Barira tana da matuƙar tasiri, kuma ita zata kawo ƙarshen taaddancin Zaliha, saboda haka ya zaɓo mu cikin ma'aikatan sa ya sa mu kasance tare a ita, kada mu barta ta samu sukuni, muke saka ta aikata munanan abubuwa da taimakon hannun ɗanguigui da aka musanya mata. Tun daga ranar muke tare da yarinyar, ba ma barinta tayi wani abu mai kyau tun tana yarinya, mugunta, ta'adi sune abinda tasa gaba, kakanta da kuma kakarta da suka raine ta duk sunyi iyakar iyawarsu don ganin sun kawar da mu sai dai munfi ƙarfin su. Bayan ta kai girman ta ne muka juya ƙwaƙwalwar ta saboda muna tsoron ta sauya daga turbar da muka ɗaura ta. Bata duk wani abu da ya shafi addini, babu abunda ta tsana sama da sallah, karatun Alqur'ani kuma mun riga mun juya ƙwaƙwalwar ta ko sau million za'a yi bazata taɓa haddata ba. Mun fara samun tsaiko ne ta hanyar wasu fararen shaiɗanu da suka shafe ta, da yake mun fi ƙarfin su yasa tasirin su baiyi ƙaimi a tattare da ita ba.”

“Yanzu haka ba mu bane muka zo ba, waɗannan fararen shaiɗanun ne da suka fara tasiri a tattare da ita saboda irin kyautatawar da mutanen da suke rainon ta ke nuna mata, har ta fara sanyi kuma ta daina ɓarna kamar yadda ta saba, hannun ɗanguigui ma yayi sanyi. Ko a lokacin da suka samu hatsari, mun so hallaka ta a lokacin saboda mu huta da wannan aiki mai dogon zango sai dai fararen shaiɗanun sunyi galaba a kan mu, duk da mu muka haɗa hatsarin ko ƙwarzane bata samu a jikin ta ba”

“Yanzu maganar da nake maka muna kan aikin mu, indai muka ce zamu rabu da goɗiyar nan boka zai mummunan hukunta mu, saboda haka babu yadda zamu je”

Sheikh Imam ya share hawayen dake fita da idanuwan sa yace “Lallai kun cika azzalumai, kuma Ubangiji ba zai barku ba, ita Zaliha kuma tun a nan duniya zata ga sakamakon ta. Barin yarinya kuma dolen ku ne”.

Cike da hasala shaiɗanun suka tada wata baƙar guguwa wacce ta zo da girgizar ƙasar gidan, tuni gidan ya fara rawa kamar zai rushe, duk da haka Sheikh Imam bai tsorata ba yaci gaba da karanta Alqur'ani, can guguwar ta lafa suka fara ihu suna faɗin ya dakata, zasu fita amma har sai an since ƙullin da aka yi a lokacin aikin, wnada yanzu haka yana tare da Inna Zaliha a bayan gidan ta. Dole aje a ɗauko wannan ƙullin a since, daga nan zasu bar yarinyar”.

Murmushi Sheikh Imam yayi yace “Shikenan zamu je a since ƙullin amma kafin nan ina so kuyi imani da Allah ku tuba daga irin waɗannan ayyukan da kuke yi, don kuwa Allah baya zulunci kuma baya goyon bayan zalunci”.

Nan Christins na ciki suka musulunta , musulman mah suka yi alkawarin sauya sheƙa daga miyagu zuwa nagari. Sheikh Imam yayi matukar farin ciki. Daga nan jikin Khairy ya sake.

Wani ruwan magani ya watsa mata daga nan ya wuce zuwa ɓangaren baccinsa ya kwanta.

Washegari kuwa sai ga Daddy sassafe tare da Hamma Zaki, har lokacin Khairy na kwance bata tashi ba. Bayan Sheikh Imam sun gaisa da Daddy nan ya sanar da shi komai kamar yadda ya wakana daren jiya. Daddy sai da ya zubar da ƙwalla, Hamma Zaki ma ya tausaya wa yarinyar cikin ranshi yace “Ashe ba banza ba”.

Daddy ya umarci Hamma Zaki ya basu wuri za suyi magana da Sheikh Imam. Bayan fitarsa Daddyn ya sanar da Sheikh Imam game da Hamma Zakin. Murmushi irin na manya wanda yanzu na fahimci ɗabi'ar Sheikh Imam ɗin ne yayi. Ya fuskanci Daddy yace
“Tabbas tun jiya da kuka zo na fuskanci hakan, alamomin wanda sihiri ya kama sun bayyana a tattare da shi. Amma babu komai zan bashi wani magani, da izinin Allah zai samu waraka. Akwai wasu addu'oi ma da zai lazimci karanta su, bi'idhnillah zai samu kariya daga wurin Ubangiji, Allah ya kiyaye gaba”.
Chapter 40 · 0% Book details