← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 49

Sashe 49

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari duka yan matan suka taho part din granny kamar yadda suka saba a yanzu. Tare da granny suka baje dandalin hirarsu. Fauzah kuwa tas abunda ya faru gidan Hamma Zaki sai da ta fadawa granny, nan fa hau fada da masifa sai da ta gaji tayi shiru don kanta, abunda suka so kenan dama. Bayan ta tafi khairy ta kalli Ayrah tace “Mutuniyar basu san fa me muka yi ba!” tafawa suka yi Ayrah tace “Me kika yi dai, ni ai taimaka miki nayi” dariya khairy taui tace “Ai duk da haka kinyi participating a ciki dai” ta karasa tana daga mata gira. Cike da kaguwa Yesmeen tace “Kunga kun samu a duhu fa, ku fada mana me ya faru”
“Ai kam” Fauzah ta fada.
Dariya suka kara yi suna tafawa. Khairy tace “Kai babes kunsan nace sai mun rama duk tsiyar da aka yi mana idan muka je, do u know what?” kai suka jijjiga
“Bayan mun gama gyaran gida munyi girki nasan kamshin ya isa hancin wannan fifgaggiyar Aunty Nabilar, sai da na fakaici idonku na watsa morning fresh a staircase shine fa da ta fito ta wuntsilo” dariya dukkansu suak saka can suak tsagaita.
Fauzah tace “Wallahi kin kyauta kuwa, wannan shegiyar maganinta ke ce, ashe har yanzu yar iya kike” ta fada tana dariya. Khairy ma dariyar tayi tace “Ai abun a jini ne, wollah da ace gida daya muke da ita da taga tsiya”. Idanuwa suka hada su uku sannan suka kwashe da dariya. Kallon mamaki khairy ke binsu da shi tana fadin “Meye kuma ”
Kamar hadin baki suka ce “In tayi tsami zata fito kiji”

Nan suka yi son ransu daga bisani duk suka wuce bangaren su. khairy dai littafanta ta fitar tana biyawa har lokacin lunch.

Ranar monday ne su khairy aka je competition din da ta wahalar da kanta a kai. Alhamdulillahi kuma an samu nasara dob har award school nasu ya samu. An karrama ta ranar a gaban assembly, sosai taji dadin yadda bata bawa malamanta kunya ba, haka a musabaka ma da aka yi na daya tazo a hizb 50, su ma su Ayra daga na biyu sai na uku.

Sun yi farin ciki sosai da wannan nasarar, kowa sai son barka. yanzu gabadaya hankalinsu ya koma ga shirye-shiryen WAEC da NECO suke a daya bangaren kuma shirin saukarsu suke yi.

Cikin nasara kuwa suka kammala WAEC & NECO sai kuma jira result, meanwhile, abubuwa sun faru ciki harda haihuwar Adda Najma da Adda Salma, anyi shagalin suna lafiya kuma Babes fa sun sha kyau a ranakun sunan da suka kasance mabanbanta. A nan ne kuma Fauzah da Ayrah suka yi catch, da farko basu biye su ba sai da su Yesmeen suka saka su gaba tukun suka yarda, Khalil wanda brothern mijin Adda Salma ne kuma ya kammala karatunsa aiki ma yake yi a Dubai, da kyar ya samu amincewar Fauzah, sai kuma Ishaq btothern Mijin Adda Salma ne, shi kuma a nan yola yake aiki a katafaren companyn mahaifinsa.

Su da suke ki sai gashi yanzu sunfi kowa so, Allah Allah suke daddy ya saya musu waya su huta da satar wayar granny suna waya da masoyansu. Su dai Yesmeen da Khairy nasu ido ne.

A cikin hutun nan ne kuma khairy ta je Gallara, a nan ta riski labarin mutuwar Inna Zaliha wacce sai da ta sha jinya a gidansu don tuni Baba ya sallame ta, satinta biyu ta dawo.

Dawowarta ne kuma abun farin ciki ya samu, pretty ta samu juna biyu, ganda ta karu, ga shegen fi'ilin tsiya da ta samo.

A yau Laraba suna zaune suna hirarsu kamar koyaushe Hamma Zaki ya shigo, duk irin yadda zuciyarsu shi da Khairy ke bugawa sai suka meze, gaidashi suka yi ya amsa daga nan Granny ta fito. Sun dadr suna hira kafin yayi mata sallama ta koma bedroom dinta. Har lokacin su khairy na nan suna hirarsu. Can kasan makoshi yace “Kai kuzo” Yesmeen kadai taji yayi magana sai ta rada musu. Addu'a auke Allah yasa ba laifi suka yi masa ba.

A gabansa suka durkusa suna fadin “Gamu” kamsu kuma na kallon kasa. Sai da ya share 3minutes kafin ya janyo ledar dake gefensa. A hankali ya zaro wayoyin kirar Iphone 14 guda hudu, Daya bayan daya ya bawa kowaccensu. Karba suka yi cikin ransu kamar su tashi su taka amma ba hali.

Kamar baya son magana yace “Ba an baku waya ba kuma, bana son rawar kai, banda tara numbers din samari kunji ko?”
A tare suka ce “Munji Hamma, Allah ya saka da alkhairi ya kara bude”
Cikin ransa ya amsa daga nan ya mike yana nufar waje, har ya kai bakin kofa ya dawo yace, “Ke!” ganin ita daya ce a wurin su sun koma wurin zamamsu yasa ta dago kyawawan idanuwanta tana kallonsa yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri da sauri. Mikewa tayi ta nufi wurinsa tace “Gani”
“Idan granny ta tashi kice ta fada miki sakona” daga haka ya tasa keyarsa gaba.

Kafin Zuhr kuwa sun saita wayoyinsu komai zam, duk social media handles kowa sai da ta bude account, don a cewarsu ba zaa yi babu su ba.

Bayan granny ta tashi ne take sanar da ita wai zata koma gidan Hamma Zaki tana taimakawa matarsa da aiki saboda cikin dake gareta. Babu yadda ta iya amma ranta bai so ba saboda zaa raba ta da ababen kaunarta wato babes.

Kamar yadda granny ta fada mata tare dasu Fauzah suka hada kayan Khairyn cikin trolley, da daddare kuwa sai gashi yazo. Da zai koma auka wuce da Khairy.

Tun a parloun ta fara tsinewa kazanta irin ta matar gidan Cikin ranta, in banda karni babu abunda yake tashi. Shima ba iya zaman zai yi ba yasa ya nuna mata daki.

Itama bata ce komai ba ta nufi daki, karkadewa tayi sannan ta wanke toilet daga nan kuma ta janyo wayarta. Ba ita tayi bacci ba sai wajajen 1pm bayan gama latsa wayar da tayi cike da annashuwa da farin ciki.

Washegari ko da tayi sallar asuba bata koma ba don aikin dake gabanta yana da yawa, ta kudiri cewa zata yi aiki kam amma wallahi sai ta saita matar gidan. Parloun kasan ta gyara fess kamar ba shi ba, duk kurar nan babu ita, ta feshe parloun da room freshner daga nan kuma ta wuce kitchen. Ba ita ta gama gyaran kitchen din ba sai wajajen 9am, har lokacin kuna masu gidan babu wanda ya fito. Ko da ta gama gyarawa sai ta daura breakfast daidai yadfa zai ishi dukkansu. Tana gamawa ta jera a dining daga nan ta koma bedroom dinta ta shiga wanka, wata Black atamfa mai flower green da ja, dinkin doguwar riga fitted ta sanya wanda tuni ya amshi jikinta, cikakkiar surarta ta bayyana kamar ka sace ka gudu. Powder da wet lipa kawai ta shafa daga nan ta fito don zuwa ta tayar da majiya dadin.

A hankali take taka steps din har ta iso jerin dakunan da bata san wannene nasa da matar tasa ba, har ta kai hannu zata yi knocking sai ta fasa ta wuce na gaba, knocking tayi daga ciki ta jiyo muryarta tana fadin “Yes come in”
A hankali ta murda handle din ta shiga, wani irin karni ya ziyarci hancinta tuni ta fara yamutsa fuska, dakewa tayi ta karasa gaban bed din tace “Madam, breakfast is ready” sai a lokacin pretty tasan wanda ya shigo don duk tunaninta sweetheart dinta ne.
“Kan uba!” ta furta tana tsirawa Khairy ido, ganin irin kyan da yarinyar ke da yasa taji ta tsaneta. Har khairy ta kai bakin kofa taji muryar pretty na fadin “Uban waye ya kawo ki gidana?”
Murmushin da ya karawa fuskarta kyau har sai da dimples dinta suka lotsa tayi sannan tace “Dan uwana mai gidan shi zaki je ki tambaya, mtss”

Daga haka ta fice, a harzuke pretty ta mike tana nufo Khairyn wacce ta riga ta fice ma daga dakin. Matar da bata iya komai sai gashi ta biyo wata fa gudu.

Khairy kuwa bata damu ba ta cigaba da tafiyarta cikin takunta mai daukar hankali. Pretty kuwa bata hakura ba saboda ganin takun da yarinyar ke yi kamar da gayya yasa ta bi bayanta har ta sauko daga steps din ta shige dakinta tana rufe kofar, wani banzan murmushi tayi tace “Wallahi sai nayi maganinki Auntu Nabila”.

Isowar pretty kuwa ganin parloun a tsaftace kamar na shi ba yasa ta furta “Wow!, ko dai munyi mai aiki ne?” kamshin girkin da ya nugi hancinta yasa ta leka dining area, ganin abinci a jere yasa ta yunkura zata nufi wurin. Ji tayi an dakatar da ita ta hanyar rike hannunta ana juyo da ita.

_COMMENT & SHARE PLEASE_
Chapter 49 · 0% Book details