← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 49

Sashe 2

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin irin dariyar yaƙe da Innani keyi yasa ta haɗe rai tamau tace
“Ki ma daina yaƙe ɗin nan don yau ko mutuwa zaki yi sai naci, shegiyar tsohuwa sai shegen rowa ni ban ma san ya aka yi kika zama uwar sarki ba bayan baki cancanta ba”
Ta ƙarasa tana hararar Innani. Innani da ran ta in yayi dubu toh ya ɓaci ta juya zata koma ɗaki caraf ta ji Muryar Ƴar Iya na cewa
“In ma mutuwa zaki yi Aradu sai naci, don ko ɗan ki da ya siya bai isa hana ni ci ba, da kwalmaɗaɗɗiyar ƙafar ki a nan kamar agwagwa”

Innani da ta shige ɗaki ta rasa abun da ke mata daɗi, wannan yarinya duk ta addabi rayuwar su, a da can ita ke da iko da gidan saboda baki da masifa irin nata amma yanzu sam yarinyar nan ƴar da tayi jika da ita sai mulkar ta take.

Ƴar Iya na kai ƙarshen maganar ta ta nufi tukunya, tana buɗewa tayi ido huɗu da sulalen kajin da ke ciki, tuni ta fara haɗiye yawu tana farin ciki.
“Shegiyar tsohuwa ƴar baƙin ciki, yanzu Ni zata yi wa buƙulun cin kajin nan, kwarangwatsa in naga dama guduwa zan yi da shi gaba ɗaya”

Bata tsaya wata wata ba ta bi shawar zuciyar ta ai kuwa ta cire kwalin da ta ɗaure kan ta da shi tuni mummunan gashin ta da ya danƙare wuri guda kamar gonar mahaukaciya ya bayyana ga wani uban bugu da ke tashi daga gashin. Ɗaure kwalin tayi a kunkumin ta yayi da ta sa hannu ta rungume tukunyar a jikin ta.

A haka ta sanya gudu sai waje.........

[4/26, 8:44 PM] 💎Diamond Bhatool💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

__Fictional story with life full of childhood, entertainment, revenge, betrayal and heart touching love __

SHAFI NA ‘‘‘‘‘3&4’’’’’

A haka ta falfala da gudu sai waje, duk irin tiririn da ke tashi daga cikin tukunyar hakan bai sa Ƴar Iya ajiye ta ba sai ma ƙara rungumar ta da tayi.

Basu yi aune ba suka ji su duk a ƙasa, ɗagowar da zasu yi suka yi arba da Ƴar Iya mai hannun ɓarna wacce yanzu har tayi nisa don kuwa shegen gudu gare ta kamar barewa.

Tana bangaje su bata tsaya bi ta kan su ba sai gida, tana shiga ta tarar da iya na tankaɗe garin dawar da zata yi tuwa. Bata yi sallama ba ta dire tukunyar gaban wani faifayin sannan ta hau kan faifayin.

Tana zama Iya da ta kasa haƙuri tace
“Ƴar Iya daga ina kuma kika samo wannan tukunya kuma miye a ciki? Kar dai ɓarnar da kika saba yiwa mutane kika je kika yo”

Gurmuɗa ɗan ƙaramin bakin ta tayi tana buɗe tukunyar sulalen da ta ɗauko daga gidan sarki sannan tace
“Ke iya dana wallahi kin fiye takura da sa ido...Ni har wata ɓarna nake yi ne in ban da sharri irin na mutane”
Ta ƙarasa tana tura baki gaba.

Iya da ta fahimci ɗiyar tata ta hau kuma bata son fishin ta saboda tsab zata musu aika-aika tace
“Yi haƙuri shalelen Iya, ni kaina na san ƴan baƙin ciki ne suke son shigga tsakanina da ke, yo ƴan baƙin ciki manah, Aradu su ne sai su zo su ce kinyi kaza kinyi kaza, rabu da su duk ranar da kika je birni ba zaki yi musu tsaraba ba.”

Lallashin da iya tayi mata yasa ta ɗan sauƙo ammah da tayi niyyar gurza wa Iya rashin mutunci.

Ɗaya bayan ɗaya Ƴar iya ta fara ɗauki dunƙula dunƙulan sassan kajin da aka fara sulalawa basu ma dahu ba. Sai da ta ciro kusan dunƙule goma ta ajiye kan murfin tace
“Iya ga kaza nan kizo ki soya mana sannan ki jira na dawo sai na raba kinji?”

Bata jira amsar Iya ba ta wuce waje a guje....

Kaɗe jikin su dogaran dake a bakin gidan sarki suka yi. Ɗaya daga cikin yace
“Lamara kai na ɗauka fa dokin ranka shi daɗe ne ya ƙwace har ya take mu”
Wanda aka ƙira da Lamara yace
“Toh Aradu ai gwanda ma ace dokin ne ya buge mu da wannan shaiɗaniyar yarinyar....""

Rufe masa baki yayi saboda hango Ƴar Iya na dawowa da yayi sai dai kash bakin alƙalami ya bushe tun daga can ta jiyo me dogaran ya faɗa.

Fara zazzare ido yayi yana tunanin shi kam yau kashin sa ya bushe.....A gadarance ta ƙaraso wajen da suke tsaye ta fara bin su da kallon tuhuma.
“Dallah can meyeh kuka bi kuka tsira min ido ko naci na uwar ku ban biya ba?”
“A...a....h kiyi haƙuri ƴar iya ba zamu ƙara ba” Lamara ya faɗa yana maida kallon shi ƙasa yayin da ɗaya dogarin kuma jikin sa in in banda rawa babu abun da yake yi. Kamar wadda ta tuna wani abu kawai ta miƙe zata shiga gidan tana faɗin
“Kun ci sa'ah yau ina farin ciki na ci kifi ga kuma nama na jirani Aradu yau da na karya ƙafafuwan ku musamman wannan me gemu irin na tauren nan.

Ƴar Iya na shiga gidan bata wuce ko ina ba sai ƙofar matan sarki, don ko hauka take ba zata shiga ƙofar tsohuwar can ba sai ta kawo mata tukunyar ta.
“Gafara dai gafara dai matan sarki” Ƴar Iya ta faɗa yayin da ta sauya tafiya sai wani lanƙwashewa take kamar hawainiya, farfara idon da take yi ne ya ƙara bawa Saratu Matar sarki ta tsakiya dariya.
Babu tsammani kawai suka ji Muryar Saratu na sheƙa dariya.

“Kan babar uban can, ke ni kike wa dariya?”
Saratu da ta kasance Ƴar duniya gaba ɗaya ta takurawa uwargidan sarki Salamatu da iyalen ta ga kuma shegiyar rashin kunyar da take fama da ita.
Salamatu tun ba yau ba ta san Ƴar Iya shiyasa tayi miƙit da bakin ta, ita kuma Saratu dama daga Kahin (ƙauyen da ke kusa da su) aka auro ta. Kuma Ƴar Iya bata fiye biyo ƙofar sarki ba iyakarta ƙoƙarin waccar tsohuwar.

Saratu kuwa dariya ta ke sheƙawa kamar wanda aka sheƙawa laughing gas. Can ta tsagaita ta kalli Ƴar Iya irin kallon da uban wa kika zo tace.
“Lallai kuwa yau naga iya shege, Salamatu kina ji wai ni yarinyar nan take kwatamawa rashin kunya, Aradu yau Sai ubanki ma yaci uban sa, dogarai zan sa su ɗauko tsumangun zane Dawaki su ci ubanki" Ta faɗa tana kama fuska wai ita babba, miƙewa tayi da niyyar fita don ƙiran dogari ai kuwa a lokacin Ƴar Iya da ta hasala ta ja ƙafar Saratu ji kake tiiiiiiiiim! Kamar faɗuwar buhun kaya. Bata yi wata wata ba ta samu saitin bakin Salamatu ta buga mata naushi tuni jini ya fara zuba kamar famfo....hango wani kashin shanu da ke can gefe tayi ai kuwa kafin ƙifta ido ta ciko hannun ta da shi ta dawo. Bakin Saratu da ke jini gashi sai ƙwala ihu take tana son tashi ma ta kasa. Buɗe bakin tayi ta fara cusa mata kashin shanun nan tana faɗin “Shegiya haɗiye ko naci ubanki, haɗiye maza, yauwah maza dai haɗiye” sai da ta cinye kashin nan tas har abun tausayi tukun ta ƙyale ta tana sakin dariyar mugunta, su Saratu kuwa anji jiki baki ya mutu, hawaye ne kawai ke zubowa.

(Nace maganin maras kunya kenan, dama an ce kin ishe su ai, yanzu kin haɗu da gamon ki).

Miƙewa tayi ba tare da ta damu ba ta bar gefen Saratu, Salamatu kuwa kame kanta tayi tana maida kan ta ƙasa.
“Ke kuma sai kace wata munafika dallah ɗago kanki, wato mata dai sun iya tsula tsiya da munafurci, dubi kan ta kamar asusun boka, ja wannan lafcecen jikin naki ki bani wuri ko na dawo kan ki”
Ai da gudu Salamatu tayi ɗakin ta. Maida kallon ta ga Saratu tayi tana yamutsa fuska tace
“Ke kuma gobe in na zo ki ƙara min rashin kunya ki gani, bari na ƙira dogari ɗaya ya sanar da sarki matar sa ta karye” ta faɗa tana kashewa da dariya sannan ta fita.

A bakin ƙafa ta sanar da dogarin cewa Saratu matar sarki na neman sa daga nan ta cika bujen ta da iska.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan su A'i Aminiyar ta wacce take take mata bayar kamar bafadiya. A'i ma ba baya ba a rashin ji shiyasa duk ƙauyen babu wacce Ƴar Iya ta zaɓa matsayin abokiyar ta irin A'i, tare suke tsula tsiyar su, su tsokali wannan su zagi wannan in sun ganshi su duka wannan aikin su kenan cikin gari ini suke suna yawo kamar ƙudaje daga nan sai can.

Tun daga baƙin soron gidan su A'i Ƴar Iya ke ƙwala ƙiran ta.
“A'i A'ilo kan kaza Amadu ya siyo mata kaza taci” wannan shine kirarin da Ƴar kewa Aminiyar ta tuni zaki ga ta fito da yake ita ma duk ta ishi gidan su har Allah Allah suke ta fita. Yau da bata fita ba tsiyar da ta tsula musu ba'a magana.

A'i na fitowa daga gida ta dubi ƙawar ta tace
“Kutt Ƴar Iya dama kina cikin Gallara yau ko kallon ki banyi ba, ko dai kin samu kaso ne shiyasa”
“Dallah ni ba magana nace ki min ba ki zo muje gida yau na samo babban rabo”
Nan ta bata labarin kifin Bala da ta kwaso da kuma Naman Iya Uwa Maman sarki. Suka yi ta dariya suna shaƙiyyancin su.

Har sun kama hanyar gidan su Ƴar Iya A'i tace ”ah Ƴar Iya wallahi mu bi ta dandali ta wurin Bayero mai balangu nasan zamu dara. Tafa hannu suka yi suna dariya Ƴar Iya tace
“Ke A'i yau kam dai sai cikin mu ya cire don ciwo mu dai wuce.

Tafiya suke suna taɗe-taɗen su har suka iso dandali, duk da cewa dare bai yi ba lokacin ne ma ake kiran sallar Ishã ammah yara da manya, ƴan mata da samari sun cika maƙil ga kuma ɓangaren Bayero da yake sayar da balangu sai kai kawo ake a wurin.
Chapter 2 · 0% Book details