← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 49

Sashe 47

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka rayuwa taci gaba da kasancewa, Khairy ma ta shiga islamiyya kuma karatun nan abun mamaki shiga yake yi har sai da tazo ta wuce su Fauzah, a bangaren boko ma ba a barta a baya ba, don in kaje kana fadan sunanta kowa ya santa ba dan komai ba sai don ƙwazonta da kuma shiga rai da take da shi uwa uba iya mu'amala da mutane, abun mamaki kuma idan mutum ya nuna mata wargi sai ta cire rigar mutumci tayi masa tas tamkar dai *ƳAR IYA*

*TWO YEARS LATER (Bayan shekara biyu*

Wasu kyawawan Ƴan mata ne da suka gaji da haɗuwa da kyau su huɗu tsaye a bakin gate ɗin Islamiyya, kowaccen su sanye take da hijabi babba brown colour sai kuma wando coffee brown yayinda ba'a iya ganin colour na rigar don yadda hijabin ya sauƙo
Duk cikinsu babu baƙa, farare ne tas wanda in kayi musu kallo ɗaya bazaka so dainawa ba sai ka kai wani duban garesu.

Ta biyunsu a ɓangaren dama ne tace “Ya Ilahi, wollah yau ɗin nan I'm exhausted sisters, gashi drivern ma yaƙi zuwa da wuri, don Allah ku samar mun wurin zama in ba haka ba anjima zan faɗi muku”
Ta farkon tace “Sorry Khairy Ai dole ki gaji, rabonki da runtsawa tun jiya, and all this is bcuz of so called competition ɗin da zaku ce, ga kuma musabaƙar da kika makalawa kanki” ta ukunsu ce tace “Ni wallahi Fauzah na rasa Khairy wace irin mata ce, in tasa abu gaba ko abinci bata ci, Allah dai ya shirya ki”
Tare suka ce “Amin” ta ƙarshen ne bata ce uffan ba dai-dai da zuwa driver Yana parking gabansu tace “Oyah! Letz go babes”

Ai kuwa nan suka shige motar sai gida, suna parking dukkansu suka wuce part ɗin granny, bayan sunyi wanka kowaccen su ta ɗauko Alqur'ani tare da shimfiɗa sallaya. Baka iya jin muryoyinsu har lokacin sallar maghrib suna karatun. Alwala suka ɗauro tare da tayar da sallah.

Har zuwa lokacin babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana, bayan sun idar da sallah Khairy ta kwaso mordern biology textbook, new school chemistry textbook, new general mathematics da kuma okeke's Physics. Nan ta baje tana karanta su tare da warware matsalolin da dama, ni Bhatool ido kawai na bita da shi don abun ya bani mamaki musamman yadda take ragargaza equations, tana solving mathematics ba tare da amfani da calculator ba.
(Allahu akbar).

Sauran ƴan matan a ɗaya ɓangaren suna karanta Alqur'ani ne cikin ransu ba tare da mai karatu yana iya jiyo muryoyinsu ba.
Ƙiran sallar Ishã ya tayar da su suka gabatar, bayan sunyi sallah kuma suka ɓarke da hira tare da komawa parlourn. Granny dai sai mita take wai sun shige jikin jikarta yanzu bata samun kusanci da ita.
Ƙyalƙaylewa da dariya yesmeem tayi tace “Kai granny ba dai kishi ba, na so an haife ni lokacin da kike matashiya da naga salon love ɗin ki” duka grannyn ta kai mata ita kuma tana zamewa, sauran dariya kawai suke yi. Granny tace “Wannan yarinya ba dai iskanci ba, kuyi dai ku gama makarantar nan duk aure za'a yi muku, yara sai shege faɗin lob kamar akansu aka fara” ta ƙarasa tana sakin tsaki.

Dining gabaɗayansu suka nufa, bayan sunyi dinner kowa tayiwa granny sallama tare da wucewa ɓangarensu.

Washegari weekend ne, da safe suka shirya don yau Mom ta tasa su gaba sai sunje gidan Hamma Zaki coz Basu taɓa zuwa ba tsawon lokacin nan, a cewarsu kar suje Aunty Nabila tayi dambunsu.

Cikin Expensive abayas da suka gaji da haɗuwa ƴan matan suka shirya, sunyi kyau kam kamar ka sace ka gudu, ba zaka san da irin kyan da suka yi ba sai kun kai dubanku ga tauraruwarsu wacce kamanninta suka juye tamkar wata ɗiyar larabawa, i doubt not Fulani ba ba baya ba a kyau. Handbag ɗin hannunta ta gyarawa zama tare da gyara veil ɗin da tayi rolling. Cikin muryarta mai daɗin sauraro tace “hey Babes...mu wuce ko,”
Murmushi suka yi kamar haɗin baki suka ce “wow! Khairy kin gaji da haɗuwa fa”
Hararar wasa ta jefa musu tace “Babes ai kuma kun gama haɗewa, Ni inaga ma zan daina yawo da ku don zaku sa kasuwata ta yi sanyi” ta ƙarasa tana kanne ido ɗaya tana dariya”
Yesmeem ce ta kawo mata dukan wasa tana faɗin “Wallahy Khairy ke kike kashe mana kasuwa, kin tuna wannan Khalifa mai ɗinkin?”
Duka ta kaiwa Yesmeen ɗin, Fauzah tace “Muje Babes, Kuna ɓata mana lokaci, Allah dai yasa mu dawo lafiya”
Kyaɓe baki dukkansu suka yi suna faɗin “Ameen”.

_Toh jama'a me kuke tunanin zai faru a gidan Pretty?, Ku dai ku ci gaba da bibiyar alƙalamin Diamond Bhatool, loads of love_

[28/08, 9:07 PM] 💎Diamond_Bhatool💎:

🍀🌸🍀🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA “““79&80 ”””

Mota suka shige daga nan driver yaja motar, bakin wani tafkeken gate yayi horn, babu bata lokaci aka bude musa, “Masha Allah” dukansu suka furta, sai da driver ya daidaita parking suka fito.

Entrance door din suka nufa suna zazzare idanuwa kamar wasu barayi. Doorbell suka danna amma tsawon wani lokaci babu alamar zaa bude har sai da suka kosa da tsayuwa.

Khairy tayi tsaki tace “Nifah babes na gaji wollah, tunda nazo da wayar granny kawai mu kira Hamma Zakin ko bata nan. Amma kafin nan muyi ta danna doorbell in ta gaji da ji hala ta bude ”
Duk sunyi na'am da shawarar Khairyn suka fara danna doorbell din ba kakkautawa. Tsawon mintuna bakwai amma babu wani yunkurin budewar, in banda tsaki babu abunda suke saki.

A hankali taja gefe tare da shiga contacts na wayar, _Maza_ ta fara dubawa don tunaninta ga hakan ya tsaya, abun mamaki numbernsa wanda special ne ya bayyana. (Bari dai na bawa readers numbern Hamma Zaki in da mai sonsa to.....0707777....).

Dialling tayi tare da karawa a kunnenta, a lokacin kuma sauran suma suka iso gareta. Ajiyar zuciya khairu ta sauke jin numbern ya shiga, sai dai yana fara ringing akayi rejecting, bata kai ga kara kira ba kuma kiransa ya shigo wayar. Picking tayi tare da saka wayar a handsfree. Cikin mutyarta mai dadin sauraro tayo sallama, shima amsawa yayi sai dai ya shiga wani yanayi jin wata daddadar mutya wacce take dauke da wani sinadari da bai aan na menene ba. A gefe daya kuma yana tunanin lafiya? Numbern granny kuma wata ta daga don shi har ya manta akwai wata khairy a gidan.

Tsawon lokacin da suka shafe babu mai magana a ciki alamun dukkansu sun shiga wani yanayi ne, don ita khairy a nata bangaren zuciyarta ne ke wani irin bugu, Fauzah ce ta tabo ya nan ta dawo hankakinta, cike da inda-inda tace “Ehm eh dama su Fauzah ne, mom tace muzo kuma muna ta jira a bude mana kamar babu kowa a gidan”
“Shikenan ku tsaya yanzu zaa bude kunji” daga haka yayi rejecting kiran. Numbern Pretty ya lalubo tana picking ta furta “Hello sweetheart...” katseta yayi yana fadin “Ki wuce ki bude kofa tun dazu kina nufin baki ji karar doorbell ba?” bai jira amsarta ba ya katse kiran yana sakin tsaki.

Lokaci daya kuma ya tuna da wannan daddadar murya, “Fauzah” ya furta, “Noo that should not be Fauzah, then who?” ganin zai bata wa kansa lokaci yasa ya mike tsaye.

A bangaren su khairy ko 3minutes basu kara ba suka ji karar bude kofa, waiwoyawa dukkansu suka yi suna duban kofar. Pretty ce tsaye cikin wasu tsinannnun kaya, ganin wadannan cousins din Hamma Zakin yasa ta saki tsaki tsaki tana jifansu da wani matsiyacin kallo, tayu yunkurin konawa idonta ya sauka kan Wata kyakkyawar yarinyar da bata santa cikin familyn ba, dumm zuciyarta ta buga amma ta kafse tare da shigewa abunta tana juyi kamat wata macijiya. Dariya khairy ta kwashe da ita tana fadin “Babes don Allah baku ga muciya bane, hhhhh kinga yanda take wani juyi don Allah”
Dukkansu dariyar suka yi kamar zasu yi kuka, daga hakan khairy tace musu “Mu shige ciki mana babes” ta karasa tana kanne musu ido daya.

Dukkansu suka dunguma zuwa parlourn, cak suka tsaya saboda kurar da parloun yayi, ta can gefe kuma ga datti alamun dai matar gidan ba girki take yi ba order take. Cikin ransu duk Allah wadai suke da hali irin na in-law din tasu wacce babu wani kyakkyawan hali daga gareta da ya isa garesu, tabbas jarrabawar Hamma Zakin ne amma ina mutum mai nagarta itinsa da mace irin Aunty nabila?. Ganin babu inda zasu yi gashi kuma Mom tace yini zasu yi wallahi da ba zasu zauna a wannan kazamin parloun ba.

Khairy ce tayi tsaki tace “Babes mu nemo kayan aiki mu tsaftace parloun don wollah ni bana iya zama a cikin kazantar nan”
Yamutsa fuska Ayrah tayi tana fadin “Ai dolenmu, amma wai dagaske Hamma Zaki kuwa yana iya rayuwa a hakan?”
Fauzah tace “Nima abun ya tsaya a raina, mutumin da tsabagen tsafta wani lokacin har mamaki muke yi”
Yesmeen ta cafke da fadin “Kin manta kullum cikin kiranmu da kazamai yake yi bayan babu wani abun kazanta da muka yi”
Fayzah tace “Ai wollah dole mom taji, haba no wonder Hamma ke ramewa, ku tuna lokacin da Hamma Salim yayi aure yanda kullum kara kyau suke duk da akwai yaro ma, amma ki ga Hamma Zaki, miskilamcinsa ma kullum karywa yake” ta karasa hawaye na silalowa daga idanuwanta.

Khairy ce ta goge mata hawayen cike da kulawa tace “I'm sorry sister, Allah yana tare da my haka Hamma Zaki ma, addu'a kawai zamu ke yi masa ok?” kaibta gyada khairy tace “Now babes to work, mu gyara parloun nan irin wanda baa taba yimasa ba”
“Yea” suka hada baki tare da fara tattare parloun.
Chapter 47 · 0% Book details