← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 49

Sashe 37

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan uncle Suraj ya dawo ya tarar da Nenne a parlour, sabuwar gaisuwa suka yi. Abinci ta tambaye shi yace a'a baya buƙata. Hirar su suka ci gaba can Nenne ta sako zance A'isha.
“Abbi Najma inaga ya kamata a san matsayin yarinyar nan, ta nuna min ita dai bata son komawa can ma, in babu damuwa sai ka barta a nan tare da su Yesmeen”
Murmushi Uncle Suraj yayi yace “Kamar kin san me ke raina kuwa, yarinyar akwai ayoyin tambaya a tattare da ita, zata cigaba da kasancewa da mu har zuwa lokacin da zan gano ɓoyayyen Al'amarin dake cikin rayuwar ta”
Haka suka gama hirar su.

Washegari da safe kamar kullum suka tashi, bayan sunyi sallah itama ta tashi, sai dai ita bata yi sallar ba ta cigaba da zamanta a kyakkyawan ɗakin da aka bata ta kwana. Nenne da kanta ta shigo don tayar da A'isha sai dai da ta ganta kwance idi biyu sai ta tambaye ta
“A'isha kinyi sallah kuwa?”
Ido ta ƙwalalo waje tana duban Nenne. Sake maimaita tambayar Nenne tayi
“Kinyi sallah ne A'isha?”
Duru-duru ta fara hakan yasa Nenne fahimtar ta.
“Oya tashi ki shiga bayi kiyo alwala ki kuma tabbatar kinyi sallah kinji?”
Kai ta gyaɗa sannan ta miƙe tana nufar bayin, fuska da hannun ta ta wanke sannan ta wanke ƙafa, bayan ta fito ta fara kife kife ala doke tana sallah ne.

Yunwar da ta dame ta ne yasa ta fito parlourn ko angama abinci, karo taci da Yesmeen da Adda Najmah cikin shirin su na makaranta. Lokaci ɗaya taji sha'awar komawa _sukul_ kamar yadda take faɗa, a dai-dai lokacin ta tuna da Aunty Jiram ɗin ta. Murmushi kawai take yayin da hankalin ta ya gushe. Fitowar Nenne daga kitchen tana jera abinci a dining yasa Yesmeen da Adda Najma ƙarasawa dining area ɗin.

Sai a lokacin ta dawo hayyacin ta, Nenne na kula da ita sarai sai dai ba tace da ita uffan ba. Sai da ta gama jera breakfast ɗin ta juyo tana kallon A'isha. Fuskar ta ɗauke da murmushi tace “Aisha babu gaisuwa ne” cikin inda_inda tace “Ina wuni”
Da “lafiya” Nenne ta amsa mata sannan tace, ki wuce dining ina zuwa” ba tare da sanin meye dining ɗin ba kawai ta tunkari wurin don iyakar ƙoƙari tayi shi, ji take kamar ƴaƴan hanjin tazasu tsinke saboda babu.

Cikin mintuna da baza su wuce biyar ba sai ga Nenne da Uncle Suraj sun fito cikin shirin sa na kayan police 👮, Aisha na hango shi ta tsura mishi ido kamar zata cinye shi, lokaci guda kuma rana tuna shegun da suka tafi da ita suka mata dukan tsiya.
“Allah yaso naci ubansu kafin na dawo ai” abunda ta furta kenan tana cije leɓen ta. Da kallon mamaki Adda Najma ke binta kawai haka nan Yesmeen, isowar Uncle Suraj ne da Nenne tayi gyaran murya.
Kujera taja mishi tare da faɗin “Good morning Abbi Najma”
Cike da murmushi ya amsa da “Morning”
Nan Najma da Yesmeen suka gaida shi banda A'isha dake bin shi da kallo.

Nenne ce ta katse ta da faɗin “Baki gaishe da Abbin ku ba A'isha”
Cike da basarwa tace “Ina wuni”
Cikin sakin fuska Uncle Suraj ya amsa da “Lafiya ƙalau A'isha”.

Nenne ce tayi serving kowa, daga nan baka ƙara jin bakin kowa ba sai cak cak da spoons ke bayarwa idan sun haɗu da plate. Cinyewa da tayi yasa ta zubawa plate ɗin gaban Nenne ido. Ƙaraf suka haɗa ido sai ta kawar da nata, Nenne kuma ta yi murmushi tare da jawo plate ɗin ta ƙara mata sannan ta tura shi gabanta.

Babu kunya A'isha tasa hannu taci gaba da ci har ta kammala, lokacin su Najma duk sun shige ciki don su yo brush sannan su ɗauko schoolbags nasu.

★★★★★★★

Bayan fitar su Najmah uncle Suraj suka fito shi da Nenne wacce hannun ta ke riƙe da A'isha, part ɗin granny suka nufa a tare. A parlour suka tarar da ita tana kallon Africa TV3. Bayan ta amsa sallamar su suka shiga tare da samun matsuguni. Gaishe ta suka yi ta amsa sannan ta bisu da kallo alamar tana buƙatar ƙarin bayani game da yarinyar da suka zo tare.

Cikin dakewa uncle Suraj yayi mata bayanin komai game da A'isha tun daga haɗuwar su da zaman da tayi tare da su.
Cikin farin ciki granny ta miƙe tare da kamo hannun A'isha, babu musu ta bi ta har zuwa gefenta da ta zaunar da ita tana famar murmushi.
“Kai amma naji daɗi sosai, wannan yarinya kamar ɗiyar Ramatu” (Mom)😂 da yake bata iya faɗin Rohmoh ɗin. Shafa fuskar ta tayi tace
“Yarinya kyakkyawa da ita, to babu komai amma ina neman wata alfarma daga gare ku”
Ba tare da sunce komai ba granny taci gaba.
“Ina so ku bar yarinyar a tare da ni don Allah, nasan zata ɗebe min kewa”
Cikin murmushin yaƙe Nenne tace “Babu komai ta zauna ai duk ɗaya ne,zamu wuce Inna”
Murmushi granny tayi tace “Na gode muku ƙwarai da gaske, Allah yayi muku albarka”
Da “Ameen” suka amsa sannan suka miƙe a tare. A'isha dake gefen Granny tayi luƙus don ji take yi kamar tare da Iya take. Hannu kawai Nenne ta ɗaga mata daga haka suka fice.

Sai da granny ta tabbatar sun tafi ta juyo da A'isha tana duban ta. Murmushin dake kan fuskar granny yaƙi ɓacewa saboda tsantsar farin cikin da take ciki.
“Ƴan mata yaya sunan ki?”
A'isha tace “Suna na A'isha amma ana cemin Ƴar Iya”
Granny ta wangale baki “aaaaa kice takwara ta ce ke ɗin, amma wane suna kika fi so ana ƙiran ki dashi anan?”
Ɗaga kai tayi alamun tana tunani can tace “Aisha nafi so”
“Tooo too shikenan Amma za'a sauya miki suna saboda sauran ƴan gidan basa iya kiran suna na”
Kai ta gyaɗa ba tare da ta fahimci me Granny ɗin tace ba.
“Tashi muje na nuna miki ɓangare na”
Ko ina sai da granny ta nuna mata daga ƙarshe ta nuna mata wani ɗaki
“Wannan ɗakin na baki shi ke kaɗai, amma fa in kina son kwana a ɗaki na ma bazan hana ki ba”.

Farin ciki kamar ya kashe A'isha saboda yanzu ji take har ta zama Ƴar gayu. Granny kuwa sai nan da nan take da A'isha wai tayi ƴa. Cikin ƙanƙanin lokaci A'isha ta sake da granny Kamar dai Iyar ta. Hakan yayi wa granny daɗi sosai.

Da yamma bayan su Yesmeen sun dawo daga islamiyya suka taho ita da Fauzah da kuma Ayrah zuwa part ɗin granny bayan sanar da su fauzan da Yesmeen tayi game da A'isha.

Sun kuwa ci Sa'a A'isha na zaune a ɗaya daga kujerun parlourn. Cikin sakin fuska suka nufe ta gabaɗayansu.
Ayrah tace “Sannun ki, ke kyakkyawa ce” murmushi A'isha tayi tace “Aradu ku kun fini kyau, duk gidan nan Aradu babu maras kyau kamar aljanu”
Dariya suka shaƙe da ita kafin Fauzah ta dakatar dasu da faɗin
“Ni suna na Fauzah, wannan Ayrah, wannan kuma Yesmeen, ki ɗauke mu a matsayin ƴan uwanki”
Dariya A'isha tayi tace “Babu komai, sunayen ku na ƴan birni ne Aradu, ko dan kuma ƴan birnin ne” ta ɗan dakata sannan tace “Ni suna na Ƴar Iya, Amma fa Nenne wacce nake ɗakinta jiya tace daga yau ba haka sunana ba”
Dariya su duka suka yi, Ayrah tace “To meye asalin sunan ki?”
“A'isha sunana fa, don sunan Iya gare ni, amma acan Gallara Ƴar Iya mai hannun ɓarna ake cemin, Aradu kowa ya Sanni a can, hhhh” ta ƙarasa tana sakin dariya.

Kallon mamaki duka suka bita da shi, can Fauzah tace
“Ba zamu ƙira ki da wannan sunan a nan ba, sunan ki kuma sunan granny ne, za mu tambayi Mom ɗina sunan da ya dace da ke”
“Waye kuma Mom?” Aisha ta tambaya
Murmushi Ayrah tayi kafin tace “Ke maman ta ce, Ƴar Indiya ce, baki ga Fauza ma na kama da su ba?”
Ba tare da ta fahimta bata gyaɗa mata kai.
Nan suka yi ta hira abun su har lokacin maghrib, kowa yayi sallah banda Ƴar Iya wacce ta make akan kujera sai hura hanci take wai ita Ƴar Birni.

Granny da kanta ta tsaya kan Ƴar Iya har saida ta buga sallar tata. A nan ɓangaren granny suka yi ta hirar su har bayan Ishã, bayan sunyi dinner suka yi wa Ƴar Iya sallama daga nan kowa ta wuce part ɗin su.
Babu laifi sunyi sabo sosai cikin ƙanƙanin lokaci, Fauzah ta sanar da Mom batun Ƴar Iya tace mata gobe su rako ta wajen ta.

[8/18, 10:03 AM] 𝙳𝚒𝚊𝚖𝚘𝚗𝚍_𝙱𝚑𝚊𝚝𝚘𝚘𝚕💎:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA””” “““63&64

A daren ne Granny ta aikawa surikanta da kuma ƴaƴan ta tana son tattaunawa da su.

Washegari kuwa duka gidan suka ɗunguma part ɗin Granny. Bayan sun gaisa cike da girmamawa take yi musu bayani akan Ƴar Iya, wacce a lokacin aka sauya mata suna da _Ummul-khairy_ domin sunan granny gare ta.

Daga ƙarshe Granny ta rufe taron da faɗin “Wannan yarinya ina so kowa ya nuna mata ƙauna tamkar yadda zai nunawa ɗiyansa, ku ja ta a jikin ku domin akwai wani al'amari a tattare da wannan yarinya, ku so ta don Allah”
Gaba ɗaya suka amsa da “In sha Allah Hajiya zamu kula da ita”
Nan taron ya watse.

Ɓangaren Khairy kuwa bacci take kwasa a lokacin ma, sai bayan wucewar su Granny ta tayar da ita. Daga jiya zuwa yau granny ta fihimci abubuwa da dama game da yarinyar shiyasa bata wani takura mata ba.
“Tashi Khairy kiyi sallah”
Ba musu ta miƙe tsaye tana miƙa kamar wacce zata cinye na gefenta, hakan ya bawa granny dariya sai da ta dara.
“Ja'ira wuce kiyi sallah”
Bayi ta nufa ta wanke fuskarta da hannayenta, daga ƙarshe ta wanke ƙafa ta fito. Sallaya ta shimfiɗa ta gabatar da sallar ta.

★★★★★★★★
Chapter 37 · 0% Book details