← Book details Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 49

Sashe 33

Yar Iya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin yanayin ta ya sauya yasa ya fara Binta a hankali.
“Kiyi haƙuri bazan iya sakin ki daga aure ba,. Ki bari muyi rayuwar mu har ki haifa min yara”
“Bura ubaaaa” ta faɗa da ƙarfi
“Aradu yanzu zaka sake ni ko na kashe ka anan!”
Sanin hali yasa Arɗo cewa
“Shikenan Zan sake ki ba sai kin kashe Ni ba, na sake ki saki ɗaya”
Dariya tayi sannan tace
“Yauwah ka kyauta, na bar maka kayan ɗakin, Ni barin garin ma zanyi Aradu. Amma kafin nan ka samo min irin kazar jiya ina ci zan bar garin”

Babu yadda ya iya ya fice ɗon neman kazar. Ita kuma tafito cikin gidan. Ƙamshin wainar da ake soyawa a ƙofar Innani ta jiyo, tuni ta wuce can tana wani taku ita ala dole amarya.
“Sannun ku dai”
“Sannu da fitowa amarya, an tashi lafiya”
Salamatu ta faɗa tana kallon Ƴar Iya.
“Lafiya ƙalau, waina ce ake soyawa?”
“Eh wallahi,”
“To a zubo min na taɓa mana”
A wata kanga salamatu ta zuba mata daga haka ta wuce ƙofar ta.

Tas ta cinye wainar ta zauna jiran arɗo, sai can gashi ya shigo.
“Yauwa arɗo, na gode Ni zan wuce sai watarana kuma SADUWAR alkairi”
Ta faɗa tana amsar ledar. Wani iri yaji yace
“Ina zaki je ne haka?”
Kai tsaye ta bashi amsar “Birni zan koma gurin Aunty jiram ɗina”
“To ga wannan sai wata rana”
Hannu tasa ta amshi kuɗin tana faɗin
“Nagode arɗo, sai watarana.

*Masu tambayar littafin Ƴar Iya daga farko kuyi following channel ɗina zaku samu.*

[6/23, 10:49 AM] Diamond Bhatool💎🩷✍️:

🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸 🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀
*ƳAR IYA* *(Mai hannun ɓarna)*
🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀🌸🍀

_NA_

*Fadimatu Adamu Hassan*
*Diamond Lady 💎*

SHAFI NA “““55&56”””

Tana amsa ta fice daga fada. Bata tsaya ko ina ba sai gidan Iyar ta. A lokacin kuma ƴan taron biki basu gama tafiya ba, cikin su ne wata taga amarya....nan mamaki ya cika ta amma bata ce komai ba saboda ta san in tayi magana zata kwaɗu ne.

Ƙira ta fara ƙwalawa Iya yayin da Iya ke makewayi
“Iya! Ina kike ne Iya ta?”
Ba shiri Iya ta fito tana gyara zaman zanin ta tana faɗin
“A'ah shalele na a gida?, Har kin fara yawo Shalele?, To muje ciki”

Iyan ce ta fara shiga ɗakin, sai da Ƴar Iya ta tabbatar da cewa Iya ta shige ta dubi matan dake zaune a kan taburmar kaba suna hira, yamutsa fuska tayi tace
“Ba a gama bikin bane?”
Ɗaya daga cikin su ta ce
“An gama”
Harara Ƴar Iya ta cilla musu tana faɗin
“To uban me kuke yi baku tafi ba?”
Jikin su ne ya fara rawa suka kasa magana. Ƙasa da murya Ƴar Iya tayi tace
“Ku haɗa kayan ku ku ɓace a gidan nan”
Daga haka ta shige bukkar Iya.
Su kuwa Tuni suka fara haɗa shirgin su don su wuce.

Tun kafin ta zauna Iya ke Binta da kallon tuhuma, murmushi ta aika mata tare da zama a baki gadon bunun dake ɗakin.
“Shalele lafiya na ganki a nan?” ta tambaye ta cikin Muryar dake nuna tsantsar damuwa.
“Iya ai birni zan tafi nikam, tuni Arɗo ya sake ni”
Cikin ƙwalalo ido waje Iya tace
“Ya sakeki kuma? Jiya fa kika tare?”
Cikin sigar kwantar da hankali tace
“Eh Iya ni na saka shi, birni nake son tafiya, nima ina so na zama Ƴar gayu, na zama abun alfahari gare ku.”
Duban ta Iya tayi kafin tace
“Duk da haka ban ji daɗin kashe auren ki da kika yi ba”

Hawaye ne suka zilalo daga idanuwan yayin da suke sauƙa akan kyakkyawan kumatun ta. Duban Iyar tayi cikin ido tace
“Iya na gaji, tunda nake kullum jefa ku cikin damuwa nake saboda wannan”
Ta faɗa tana nuna hannun ta
“Hannu na shine dalilin komai, Iya zan koma birni nima na gina rayuwa ta kamar yadda Aunty Jiram ke faɗa min”
Cikin karyewar zuciya Iya ta dubi shalelen tata sannan ta saki murmushi
“Duk da haka muna buƙatar ki Shalele, ƙaddarar ki ce haka, mu bamu gaji da ke ba kuma bazamu gaji da ke ba koda kuwa kece zakiyi silar ajalin mu”

Murmushi itama tayi tace
“Iya ta kenan, banajin zan cigaba da zama da ku, Ni ɗin annoba ce ƙwarai, amma duk dare kwanan nan sai an ƙira Ni zuwa birni....dole naje birni iya a can ne zan zama mutum kamar kowa...gaskiya ne Ni ba cikakkiyar mutum baceeeeeeeee”
Ta ƙarasa cikin murya mai fidda wani razanannen amo.

Jikin Iya har rawa yake ta rasa ya zata yi, bayan wasu daƙiƙu kuma ta koma kamar ba ita tayi ihun ba. Duban Iya tayi tace
“Ki amince da tafiya ta saboda hankali na duk ya tafi can, zan dawo gare ki a matsayin cikakkiyar mutum Iya ta, ina ƙaunar ki. Sannan idan Baffi ya dawo ki sanar da shi, duk wanda ya tambayi ina nake kuce na tafi birni....zanyi kewar ku Iya”

Iya ta goge hawayen ta tace
“Shikenan Shalele na amince ki je birni, kije birni Shalele na! Ina so ki zama abar alfahari a gare ni, zan so kiyi rayuwa mai kyau”
Murmushi tayi tare da rungume Iyar kamar zata mayar da ita ciki, sun ɗau tsawon mintuna kafin ta saki iyar tana miƙewa tsaye.

Daga haka ta nufi bukkar ta....duk kuɗaɗen ta da ta tara na maganin mata ta ƙwaƙulo su tare da fara jera su. Sai da ta jera sannan ta Ƙirga taga dubu 20 cif, haɗa su tayi da kuɗin da Arɗo ya bata ₦2000 sannan ta ƙulle su cikin wani tsumma, daga haka ta miƙe tare da komawa ɗakin Iya.

Jakar Ghana Must go da aka saka kayan auren ta ciki ta janyo tare da saka kuɗin ciki, iya kuma duban ta kawai take cikin karyayyiyar zuciya da kuma tausayi.

“Tabbas ta cancanci rayuwa mai kyau, tun daga kan iyayen ta take fuskantar hukunci, hukunci maras daɗi, an mayar da yarinya rabi mutum, ya Ubangiji!” a zahiri kuma tace “Ka kula da Shalele na”

Bayan ta tabbatar ta haɗa komai nata ta ajiye gaban ta, hawaye na tsiyayowa daga idanuwan ta ta ƙarasa tana rungumar Iya
“Zsn wuce Iya, Baba na ma ki sanar da shi in ya buƙaci hakan, zanyi kewar kuuuuu”
Daga haka ta saki jikin iya tana ɗaukar Bagco nata ta ɗaura a ka.

A haka ta fice daga gida ta nufi hanyar bayan gari, duk da cewa bata san ina zata je ba haka take tafiya ba tare da waiwayowa ba.

(Safe trip Ƴar Iya.... Allah sada mu da alkairin shi)

*ALEE POV*

Bai wani jima ba ya dawo gidan, ko alokacin su Ishy basu bar gidan ba. Cikin takun shi na zaratan maza ya fito daga motar tare da nufar apartment ɗin su, fuskar nan tamau kamar dai Hamma Zaki yaron Mom 😒.

Ciki-ciki yayi sallamar yana sanya ƙafar shi ciki, ganin basa parlourn yasa ya haye sama zuwa bedroom nashi. Wanka yayi sannan ya kwanta kan lallausan gadon nashi. Bacci yayi niyyar yi amma kuma ya kasa, ya rufe idon amma ina, ganin baccin ba mai yiyuwa bane yasa ya janyo wayar shi ya fara latsawa don tunanin da yake addabar shi baya so ya samu matsuguni.

WhatsApp ya shiga Yana replying messages Wanda yawanci wishes ne ake masa, ɗaya ɓayan ɗaya yayi replying duka wishes ɗin sayin “Thanks”, “Thank You”, “I appreciated” “Thanks alot” amsoshin kenan.
Sai kuma messages ɗin Hamma Yusuf da su Dr. faruq wanda duk zolaya ce. Ba tare da yayi musu reply ba ya fice ya koma status, duk da cewa shi ba ma'abocin ganin status bane haka nan ya tsinci kanshi da sha'awar haka.

_Sarah_ ne farko, gaban shi ne ya faɗi ganin numbern ta a wayar, haka kawai ya tsinci hannunsa da shiga. Pictures nata ne da gani a bikin Hamma Zakin tayi. Sanye take cikin blue and pink sari wacce ta fidda ainihin kyau irin nata, doguwar sumar ta da ta jiƙa da gyara ga kuma wani mahaukacin hairstyle da akayi sai abun ya ƙara ƙayatarwa, pink 🎀 ribbon aka ɗan maƙala ta baya....nace Masha Allah.

Sai da yayi zooming gashin yana ƙara dubawa tare da lumshe idanuwan shi. Tunawa da kan Pretty da yayi wanda ya kasance kamar hamatar ɗan iska sai uban attachment da ta maka yasa yaja tsaki “Mtsss”. Bai tsaya ba yaci gaba da kallon Sara, fuskar Mom ɗin shi ne ta faɗo a ranshi nan ya ƙara tabbatar da cewa Sarah kyakkyawa ce.

Da ƙyar ya bar picture ɗin yayin da wani yayi appearing, wannan kuma ita da Captain Sulaiman ne, haka kawai yaji ranshi ya ɓaci daga nan ya fice yana viewing sauran statuses ɗin.

Sauƙa yayi daga WhatsApp ɗin ya koma Instagram nan ma dai karo yaci da pictures da kuma videos na dinner ɗin su, tsaki yaja tare da ajiye wayar gabaɗaya yana runtse idon shi tunawa da Pretty da yayi, ya kamata ya duba ta. Wata zuciyar tace
“Waɗannan bullshits ƙawayen nata na nan”
“To kai ina ruwan ka?” wata zuciyar ta faɗa mishi.
Miƙewa yayi yana nufar bedroom nata dake downstairs. Kamar kar ya Ƙarasa kawai yayi ƙarfin hali tare da danna kanshi zuwa hanyar, sai da yayi knocking jikin ƙofar sannan ya shiga. Su Ishy kuwa najin knocking suka wuce Toilet abunsu.

Da gudu tazo tayi hugging nashi tana sakin kukan shagwaɓa.
“Sweetheart ina ka shiga haka tun asuba ban ƙara ganin ka ba....”
“Sorry Nabees” abunda ya iya furtawa kenan sakamakon yanayin da ya tsinci ruhin shi da gangar jikin shi. Kissing nashi tayi sannan tace
“Ok shikenan kaga ko abinci fa ban ci ba”
“Baki ga abinci a dining bane?”
“uhm uhm Ni ban gani ba, ai baka ce min akwai ba”
“Sorie”
Hannun ta ta ɗaura a kafaɗar shi sannan tace “To muje ka raka Ni naci”
Kasa musa mata yayi sai ya bi bayan ta. Nan ma dai kukan shagwaɓa ta saka wai ita sai dai yayi feeding nata.

Haka ya zauna yana bata har ta ƙoshi daga haka tace yazo su gaisa da friends ɗin ta. Kamar ba shi ba ya haɗe fuska yace baya zuwa daga nan ya wuce sama ya barta a wuri tana kallon shi galala.
Chapter 33 · 0% Book details